WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
Mai_Dambu
3/1/22, 18:55 – Nuriyyat: Albishir ku.. kuce min goro...ko kusan S.squar Fashion &More Sun kuma kawo muku ingantattun kayan su masu kyau da rahuwasa... Turaren wuta na zamani. Milk candy Hijabs da gowns tare da kayan Yaran ku masu kyau da inganci zaku iya tuntubar wannan number👇ðŸ¾ðŸ’ƒðŸ¼Http://wa.me/+234 703 003 7697
25
“Kiyi hakuri har yanzu muna kan bincike ne, Insha Allah za a same.” Shiru yayi bai kuma cewa kome ba, karshe ma mikewa yayi Namir yabi bayan shi.
Koda suka fito daga cikin gidan, raka Namir yayi wurin motar shi, yana kallon shi har ya bar wurin bai iya cewa kome ba, domin bai san me zai yi ba.
“Allah ka kare Rabi’ah a duk inda take.”
 …
A cikin kwanaki uku baki daya ka shirya kome, shi kanshi Jikamshi ya yaba musu da yadda kome ya tafi dai-dai babu wani tashin hankali ko damuwa, asalima ma’aikatan kamfanin JF Groups da kan su,suka bayyana Hajiya Atikah Abbas Jikamshi Mrs Abdul Hadi Shema, itace suke son ta zama Boss Lady din su. akan haka ba karamin d’aga musu hankali yayi ba, nan suka shiga tattaro hankalin yan jaridu da cewa ai Mr Jikamshi yayi haka ne domin Hajiya Atikah kanwar Ahmad ne,.mahaifin su dan haka tun kafin zaben an rigada an sayi masu zaÉ“en.
   Dan haka su basu amince da zaɓen ba, domin ba sahihiyar zabe bace haramtacciyar zabe ce, kuma idan ba akwai manufa akan zaben ba akan me zai tsaya kai da fata a zabi kanwar Mahaifin shi.
Sai gashi from anywhere tambayar da ake mishi kenan,
“Wai da gaske ka daura kanwar Mahaifin ka ce a matsayin Boss Lady?” Tun yana kallon abin kamar abin wasa, sai gashi ana d’ago wasu abubuwan da basu shafi zaben ba wanda har ya kai an tabo maganar da ake mishi lakabin da cewa yana kashe matan shi ne domin yayi arziki da su.
  Wannan abin da ya taso daga JF Group ya masifar tab’a hannun jarin su a manyan kasuwannin duniya, wanda har ta kai sunan kamfanin su da shi kanshi ya fara kasa, kamfanin shi na Jimkashi Mineral Resources Company, ya fara samun matsala, wannan abin yayi mugun d’aga mishi hankali. Dan dole ya shi gayyatar da wani gidan Jaridar People Magazines.
     Da farko da yaje aka yi hiran da shi bai dauka da dumi ba, sai da aka fara mishi tambayoyin da suka so harzuka shi, kuma an yi haka ne domin masu hannun jari a kamfanin su, su ji haushi sai ya gashi ya sake murmushi me taushi,.sannan ya cewa yar jaridar.
“Eh toh, idan har aka duba fuskar kasuwancin duniya, JF Groups sun yi Cross world, domin daga cikin abubuwan da ake fitarwa a karkashin Jagorancin JF Groups, muna fitar da Kayan abinci zuwa kasashen Afrika, sannan muna fitar da audiga, muna fitar da karo da asalin sannan a part dina Jimkashi Mineral Resources, ina fitar da karafuna zuwa kasashen china.
  Ina fitar da karo a nawa na kaina, sannan ina da kamfani nawa guda biyu a kasar waje, daya yana garin Busan. Alhamdulillahi iya kuÉ—aÉ—en da nake samu daga wadannan kamfanin, sun ishe ni ba sai na nayi blood money ba, sannan mata na uku da suka mutum na barwa Allah amma ko waye ya kiyaye haduwar mu da shi”
 “Mr Jikamshi! Ana yawan cewa matasan masu kuÉ—i basu cika damuwa da mata ba, sun fi alakanta kan su da ajiye karuwai, ko maza suna luwadi da su, sai gashi ko a wancan kwanakin da suka wuce an samu labarin P.A din ka Khalil Ibrahim Khalil, an samu wani matashi da ya ce yana tare da Khalil Ibrahim Khalil kuma yana kai shi wurin manyan shi.”
Murmushi yayi sannan ya ce mata.
“Toh maganar gaskiya ban san wannan maganar ba, asalima ba wai ba zan yi aure bane,misali ke sunan ki Amrah Jamil, i love you!”
Wani zaro idanu tayi waje, tare da cewa.
“What???” Yar dariya yayi sannan ya ce mata.
“Kin girgiza ko? Toh ai duk macen da zance mata haka toh abinda kika yi shi zata yi, sannan bayan nan ita da danginta sun shiga damuwa, damuwan ba wai akan I love you bane, rayuwarki ce abar farauta duk yarinyar da zan fada soyayyar ta, ko zata fada soyayya na abu daya ne ta shigo rayuwata ne domin na bata kariya, shi yasa a halin da nake ciki soyayya ba tawa bace, domin ina tsoro da makiyin boye dan ban san dalilin da yake kashe min rayuwa ba.”
  Shiru tayi idanun ta cike da kwalla, ta ce.
“Mr Jikamshi! Ina jajjanta maka, amma baka ce kome akan zargin p.a É—inka.”
Dariya yayi sannan ya ce mata.
“Eh toh Khalil dai mutumin kirki ne, kuma ban tab’a kama shi sa mugun abu ba, sannan idan har mace ba zata tsira ba, ya kike ganin namijin da ya mai da kan shi É—an daudu. Dan haka bana sha’awan soyayyar jinsi guda ko ta jinsi da bani da ra’ayi Amma da zaran na fara soyayya zan bawa Yarinyar kariya da dukkan fitar numfashina, Yarinyar da zan so hatta barci sai tayi zan kwanta ina fada miki yadda nake ji, Na rasa Muneebah da Bioden, na rasa Ha Na da Yarona kina tsammanin wacce zata zo shigo rayuwata zan barta ne haka, lokaci yana zuwa lokacin da zan cika alkawarina.”
   “Ina me baka hakuri akan abinda ya faru, dan haka dukka dukkan anan zamu tsayar da hiran mu na bakon mu na bako, da ni da na gabatar Amrah Jamil”Â
   Daga nan ya fito daga cikin dakin labaran ya nufi inda Khalil Ibrahim Khalil yake tsaye.
“Kayi hakuri Yallabai, ban gaya maka bane domin na ga hankalin ka ya kararkata kan rikicin da ake a JF Groups shi yasa ban gaya maka ba.”
“Is ok” ya fada tare da shiga motar shi ya zauna yana me sauke ajiyar zuciya,. Jan neck tie din shi yayi yana me lumshe idanun shi.
  Ya kai minti biyar a wannan yanayin har suka isa gidan shi, yana fita ya nufa cikin gidan shi.
Yana shiga ya zube a kujeran falon, yana sauke ajiyar zuciya, wayar shi ce tayi kara,ya dauki kiran tare da sakawa a kunnen shi.
“Hello! Yanzun naga hiran ka, wow ka burge ni, i like yadda kake da nuna shaukin ka akan matar da zaka so.” Sai da ta ja wani irin numfashi me matukar daukar hankali, ganin zata ishe shi da iyayi ya kashe wayar.
Sannan ya mike tare da tattara na shi ya nashi zai koma inda ya fito gobe inshallah sai kuma nan da wata shida ya dawo baki É—aya.
**
Dutse.
Duk da ba wani aiki take ba, kula da Junaid take, sai ko ta zauna tayi ta kallo wanda shi kadai yake dauke mata kewar Altine wacce tayi mata lakabi da Mama. Shigowa Muhiyuddin yayi ya kalli yadda take kallon cartoon.
“Huuuu!” Ya ce mata, razane ta juya tana kallon shi, zama yayi yana kallon ta, ga Junaid da yake barci a gefen, hannun shi ya kai kafadarta. Ta saka hannunta tare da cire hannun shi tana kallon tv.
    Sake baki yayi yana kallonta, ya kuma kai hannun shi zai tab’a ta, ta tashi a wurin ta bar shi a falon.
  A hankali zaman gidan ya zame mata, jiki bata magana da kowa sai Junaid, kuma bata shiga harkan kowa sai Yaron,. Sosai ta saba da yaron kullum sai ta sha maganinta, wanda ya haifar mata da samun lafiyarta sai dai ba zaka tav’a ganin tana murmushi ko dariya ba, asalima ban da Junaid bata magana da kowa, duk abinda zaka sakata zata yi maka, da fari sun zata cewa kurma ce, bata magana sai da Muhiyuddin ya gaya musu tana magana, yasa suka Amince.