WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
  A yanzu tana niman wata biyu kenan da zuwa gidan, duk maitar Muhiyuddin haka yake kyale ta, sai ta fara bashi haushi, inda ya fara korafin bata jin magana tana mugun wasa da Junaid.. duk da haka Hajiya Halimah bata wani damu da korafin shi ba.
**
Daƙayyawa
“Allah ya isa tsakanina da ke Asabe kin san karya kika min da kika ce min yar kanin ki tana can birni tana aikatau kudi me kyau, Allah sai ya saka min mugun shawaran da kika bani akan bada yar mutane da kika sa nayi!” Inji Gwaggo Lami tana kuka .
Haka ya faru ne sakamakon kawo Sahurah bata da lafiya, wasu irin kuraje sun feso a gabanta, ga shi bata rike kashi, kamar zatayi hauka domin baki daya tafita hankalin ta.
“Dalla ki min shiru nasan sharrin magauta ne, amma ace daga can birni za a kawo ta babu lafiya ai wannan abin da tashin hankali. Ki kwantar da hankalinki inshallah zata dawo” ta fada tana me jan ta daki tana bata hakuri, tare da ciro kudi me shegen yawa ta bawa Gwaggo Lami
 Â
  Baki daya sai fadar ya kare aka koma kamar da, inda tayi ta jajjantawa Sahurah domin kuwa bata zaci haka ba, Ita dai tunda ta samu kudin ta, sai abu na gaba, inda ta tambayi Sahurah gidan da Yar duwala take. Cikin matukar ciwo ta ce mata.
“Hmm! Kun kad’e har buzun ku, babu wani aikin da muke sai karuwanci, dan haka koma kun je inda take wallahi ba zaku same ta ba, domin tana da gidaje dayawa, wanda ko kun je ba zaku same ta ba, kuyi addu’a Allah yasa yarinyar tana dutse ku nemo ta, amma kuka sake ta bar dutse ta bar iyakar Jigawa hahhhhh ban san a wacce irin kama za a dawo da ita ba, domin hmm” daga nan bata kuma cewa kome ba, dan haka hankalin Gwaggo Lami a tashe ta bar gidan.
  Kamar mahaukaciya ta shiga gidan, ta fara hada kayanta. Ko jiran gobe yayi bata yi ba, ta bazama sai tasha, anan suka hadu da mijinta ya tambaye ta.
“Lafiya ina zaki?” Cikin tashin hankali ta ce mishi.
“Yarinyar nan Rabi’atu yar gurin Isayaka, na dauke ta na kaita aikatau, ashe karuwanci aka kai su ba aikatau ba.”
   Kamar ya rufe ta da duka, ta kore ta, tana kuka tana kome haka ta koma gida, da dare da kanshi ya kai maganar wurin me unguwa, aka tara mutane, ana tattaunawa..anan an samu magidanta kusan bakwai da suka shiga tashin hankali.
Dan haka suka tura aka taso Asabe a gaba, har kofar me Unguwa da Sahurah.
“Ke Sahurah me ya faru da ke?”
“Hm! Tunda yar Duwala ta kai mu dutse mun yi wata uku, a hannunta kafin aka kai ni gidan aikina, dama aikin wanke wanke ne, haka nayi na tsawon wata biyar kafin matar da mijin suka koma Æ™asar waje.
Sai aka kai ni kano wurin wata Hajiya me suna Adizah, anan na zauna ina har nayu kyau ana koya mana yadda zamu yi aiki a kano. Bayan mun gama koyan aikin, ne aka tura ni Abuja gidan wani mutum, tunda na je, bana aikin kome sai dai ya kwanta dani ta baya, har zuwa yau da aka dawo dani, da kudin aikina da ban san yawan shi ba, ga wanda nake sace mishi. Dama kuma ko gidan da nayi aiki da su ina musu sata, toh mutumin yasan ina mishi sata sai da ya ga bana iya rike kashi da fitsari , wallahi nayi nadamar rayuwata dama zan mutu na huta da azabar da nake ji.
  Wallahi duk yaran da aka fitar damu matukar basu dawo ba, TOH wasu sun mutu ne, domin naji Alhajin yana fada cewa nice kawai tsafin shi bai ci ba sabida ni din shegiya ce shi kuma yafi aiki da Yaran da aka haife su da aure, shi yasa yayi ta kwanciya dani ta baya, yana tula min kudi masu yawa domin na manta kome”
Ta karshe tana kuka, aikuwa jama’a a wurin sun yi alawadaran halin Asabe da Lami.
“Yanzun dan rashin Imani Lami dan uwanki yayiwa Yarinyar nan Jamilah fyade har kina da kunyar da zaki daukar Rabi’atu, tabbas zaku kashe mutum idan kuka samu, amma.wallahi ban isa da gidana ba, domin cutar tayi yawa kuma ki a kafa gobe ki nimo musu yar su”
   Cikin kuka da tashin hankali ta ke bashi hakuri amma ina, fushi ma yayi ta bar kofar gidan me Unguwa ya nufi gida, abin da ciwo.
“Sahurah a ina zamu same ta mu dawo da sauran Yaran.”
“Hhh! Toh ban sani ba, amma ita kan bata inda na santa wahala zaku sha kawai ni kam ku min addu’a na mutu, domin duburana kamar ana caccaka min allura wayyo Allah na….
Innalillahi wa inna alaihil raji’un allahumma ajirni fii musibati wa’akhlifni khairan minha
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
Mai_Dambu
3/1/22, 18:55 – Nuriyyat: Albishir ku.. kuce min goro...ko kusan S.squar Fashion &More Sun kuma kawo muku ingantattun kayan su masu kyau da rahuwasa... Turaren wuta na zamani. Milk candy Hijabs da gowns tare da kayan Yaran ku masu kyau da inganci zaku iya tuntubar wannan number👇ðŸ¾ðŸ’ƒðŸ¼Http://wa.me/+234 703 003 7697
26
Washi gari
Lamih ta bar garin Daƙayyawa, sai Dutse. Tun safe take niman gidan Yar Duwala bata samu ba har dare, karshe inda zata kwanta ma gaggaranta yayi tayi karshe a tasha ta kwana,tayi danasanin abinda suka aikata.
  Gari da ya waye, dole haka tattaro ta dawo gida, inda ta samu bakin labarin Sahurah ta rasu sakamakon ciwon jikinta, kamar zautattaciya haka tayi ta ihu tana kukan Allah ya kare Rabi’ah.
   **
3 Months
A cikin wadannan bayin Allah ba zaka iya cewa waye yafi wani son ganin Yar duwala ba, domin Ammyn kasa zama tayi sai gata daga Lagos tare da Wasailah da Alkasim da suka rakota.
 Duk wanda yaganta yasan tana cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, tayi kiba shar da ita, tunda suka je gidan Gwaggo Lami, ta gaya mata gaskiyar abinda ya faru. Ammyn ta zuba mata ido tare da cewa.
“Yanzu dama kiyayyar da ke tsakanin mu har takai ki tura min Yarinya karama irin Rabih karuwanci? Wai na tambaye ku meye na tsare muku? Sannan kin duba duk faÉ—in dutse baki ganta ba? Allah ya isa min, Allah sai ta bi min hakkina da ita Yarinyar. INSHA ALLAH zata dawo.”
“Kiyi hakuri don Allah kiyi hakuri mun zalunce ki, kuma mun saka ki kuka da ke da Yaranki don Allah ki yafe mana, duk da bamu cancanci haka daga gare ki ba” mata kewa Ammyn tayi tare da barin gidan. Domin bata da abinda zata ce mata, ta rigada ta bar su da Allah shi zai bi mata hakkin ta, a labarin da ta bata bata jin Rabi’ah ta bar yankin Jigawa. Dan haka zata nime ta kafin ta bar Jigawa na har abada.
Haka kuwa ya kasance, domin Washi gari suka bude dutse, suka sha yawo kamar me, sun zaga kanannun Unguwanni, the next day ma haka sai da suka jera kwana huÉ—u suna niman Rabi’ah gida gida, kafin Wasailah ta ce mata.
“Ammyn kiyi hakuri inda rai da rabo zata dawo gare mu, amma Yanzun wahalar da kan mu muke,.yau kwana huÉ—u sai dai muyi wanka mu fito daga masaukin mu, kuma Kinsan kudi ake biya mu hakura ki barwa Allah yana nan yana gani amma wannan yawon da muke ba zai bamu kome ba sai kunci don Allah ki duba abinda na ce” ganin yadda take kuka tare da rokon su koma yasa Ammyn bata mata musu ba, ta kalli Alkasim tana me share kwalla ta ce mishi.
“Don Allah kayi hakuri ina ta wahalar daku”
  “A’a Ammyn babu walaharwa, Allah ya bayyanata,” ya fada a hankali yana me hararan wasilah. Abin tausayi haka suka wuce Jama’are.