NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

  Tsawon kwana huɗu suka dauka Ammyn tana gaishe-gaishe, kafin ta isa gidan wan Mahaifiyar ta, babba malami ne. Kanta a sunkuye da yake tambayar Yaranta.

Dakyar ta iya mishi bayani, kafin ta rushe da kuka tana faÉ—in.
“Sun batar min da Yar Æ™aramar yarinyar da bata wuce aika waje ba, Kawu na rasa Rabi’ah, sannan tura yaran suke karuwanci. Kawu malam zuciyata kamar zata buga.”

    Murmushi yayi sannan ya ce mata.
“Baki yarda da kaddara bane shi yasa kike jin haka a ranki, da ciwo sai amma kuma idan ka barwa Allah sai ta maka abinda ba zata ba,” kallon agogon hannun shi yayi sannan ya ce mata.
“Ki je bayan la’asar ki dawo.”
“Nagode sosai kawu malam” ta tafi, kallon almajiran shi yayi su goma, ya ce musu.
“Ku karo min goma, sannan ku dauki wancan Alkur’anin ku raba, idan an gama a yanka toron agwgana”

“Toh malam” suka fada, a take babban su ya dauki Alqur’anin ya raba musu, suka samu izu bibiyu. Zama yayi ya fara rubutu a wani allo, tare da mai da hankalin shi wurin  masu karatun nan, yana gamawa ya ajiye a gefe. Ya shiga cikin dakin kayan malantar shi.
(Notes malam ba irin kwadayayyun malaman nan bane, mutum ne me tsarkake zuciya karki karanta a wani wurin ance malamai yan maula ne ki dauka kowani malamin tsangaya haka suke, a’a ba haka suke ba mutum ne masu matukar kyakyawar zuciya, ba zuhudu da kaunar abin duniya yasa suke raye ba, sannan duk wani malami da zaka gani yana da’awa tushen shi tsangaya ne, dan haka a daina yiwa malamai daurin goro domin su din mutanen kirki ne)

   Dauko wani tsohon fatar zaki yayi, sannan ya shiga cikin gidan ya samu matar shi uwar gidan. Kafin ya bukaci zama matar nan ta dauko taburma ta shimfida mishi. Zama yayi tare da kallon ta, sannan ya ce mata.
“Bani danko”
Wani irin abu ne kamar roba kamar,amma an fi samun shi a ta yankin arewa maso tsakiyar Nijeriya, a jikin bishiyar roba, shi dankon, kamar yadda bishiyar baure yake zubda ruwan shi, haka shima yake zuba a jikin bishiyar, wani Almajirin.shi da ya tafi har lakwaja anan ya samo shi shine ya bawa malam, dake ya tab’a jin malam ya nemi dankon amma bai samu me kyau ba, wani mutum ya kawo mishi karan Yarinyar shi bata da nutsuwa shine ya mishi wannan aikin.

  Zama yayi ya kira Sageer ya kawo mishi kayan aikin shi.
“Talatu kin ga wannan al’amarin ko bayan raina, idan an  zo maganar yarinyar nan ki warware musu kome, Uwar nata kuka an tura yarta wata duniya, Insha Allah zata dawo lafiya lafiya, da yarda Allah”
“Insha Allah malam kai zaka ware abar ka, ba wani ba” inji Amaryan shi Iyah.
“Kayya bana tunanin haka, da dai TOHe Allah ya bamu Yawan rai.” Ya fada tare da tofa addu’oi, yana gamawa ya kira Sageer ya mika mishi.
“Naga kana aikin dukanci maza dinke min karka bar wata kofa ko alama, sannan ka dauka ka kai can, wurin randar ruwan nan ka zama shaida ko bayan raina kai zaka warware domin su Talatu da Mamma wai ni zan warware.

         Kayi ta mishi bayan ruwa, insha Allah babu abinda zai faru, idan na gama ka koma wurin karatun ka.”
Mika mishi ruwan farau-farau Iya tai tana kallon shi kafin ta ce mishi.
“Na tausayawa Harirah, wallahi batar Yaro Masifa ce, baki daya bata da nutsuwa”

“Idan Allah ya zana Æ™addaran ka, ko kana cikin jin dadin ka ne sai ya faru da kai, kai dai Allah ya jarabce mu da abinda zamu iya, ya kuma bamu ikon cinye jarabawar mu”
“Amin Ya Allah malam” suka fada, yana magana sha ya mike tare da nufar dakin shi ya zauna tare da É—aukar madubin shi ya saka, sannan ta shiga duba littattafan addinin da suke dakin shi. Har aka kira azhar ya fita Masallaci. bayan ya dawo suna fara karatu sai kusan uku da wani abu aka tashi.  Yana alolan la’asar Ammyn tazo ita da su wasilah.

     Kallon su yayi sannan ya ce mata.
“Ku shiga daga cikin gidan, kai abokina zo muje masallaci.”
“Toh yallabai” inji alkasim, su Ammyn suka shiga cikin gidan, suma sallah suka yi. Tare da gabatar da sallah.

   Bayan wasu mintina suka dawo, zama malam yayi, tare da ɗaukar allo ya fara rubutu suna hira, har ya gama.
“Kai abokin karawa na, dauko min butar can.” Cikin jin kunya Alkasim ya mike tare da dauko mishi butar. ya cewa Alkasim.
“Zuba min ruwan” haka yayi ta zuba miagi har ya gama sannan ta ce mishi.
“Mahaifanka zuciyar su a bude take, domin babu sharrin shi wancan miskilin abokan adawa sun hana shi komawa bakin aikin shi, bayan kowa yasan yadda aikin su yake da matukar muhimmanci da tasiri a kasar mu, dan haka wannan rubutun ka kaiwa Alhaji Muhammad Lawal Dambatta, ya tabbatar ya bawa Dan shi Aaman ya sha, inshallah zai koma bakin aikin shi nan da wasu shekaru zai zama babban mutum me matsayi a aikin su. Kai ma ka kula da kanka domin wannan Ja’iran me idanu a tsaye zata baka wahala, ko na baka wani abu ko ban baka ba, sai ta wahalar da ruhin ka. Kasan me yasa? Sabida wani irin yanayi da suka tsinci kansu. Duk wannan kunyar da take ji zata watsar da shi.”

Idanun shi ya maida kan Ammyn, sannan ya ce mata.
“Kiyi hakuri da kaddaran da , zaki gani, da wanda zaki cigaba da gani, amma idan har ina raye INSHA Allah ba zan barki kiyi kuka ba, Kiyi hakuri da yadda Æ™addara tazo Miki, Insha Allah Yaran ki zasu zame Miki inuwa me sanyi amma sai Kinyi hakuri da yanayin da kika samu kanki.”

Nasiha yayi mata sosai, sannan ta bata rubutu a sabon kwanon sha, bayan ya zuba zuma a cikin shi, sannan ya juya ga Wasilah.
“Kiyi hakuri Kema, zaki ga abu a tare da shi. Sai dai dukkan ku sai kun yi hakuri ban ga kome a cikin alakar ku ba sai alkhairi da yan damuwa kaÉ—an.’

      Shiru yayi sannan ya cewa Ammyn.
“Ban ga Jamilah da Rahmah ba, amma nasan ita Rahmah me hakuri ce, kuma hakurinta zai mata rana, ki kula Yaran ki, Allah ya baki su domin Ni daina kuka. Rabi’atu tana tsakanin rayuwa da mutuwa ne, ko a gaban ki take ba zata kaucewa kaddaran ta ba. Rabi’atu zata dawo gare ki, sai dai tafiyar Ƙaddara ce mara dadi, ga rashin ishashen guziri, kiyi hakuri koyi darasin rayuwa kuma ki yarda Allah yana tare dake ne shi yasa har haka ya fado cikin kaddaran ki. INSHA ALLAH ba zaki yi kukan da kika yi na baya ba, kin rigada kin gama kukar ki, sai addu’a da sauran abinda Ubangiji zai nufa dake.”

          Haka yayi ta musu nasiha, har yamma sannan ya mika mata ruwan rubutu goran faro,  sannan suka Mishi alkairi kamar ba zai amsa ba, sai da matan shi suka saka baki. Washi gari suka bar Jama’are, da niman dacewar Ubangiji, da yamma suka isa masaukin su, sannan suka kwana da sassafe suka nufi Lagos, cike da kewar Yarinyar ta Ammyn tabar Jigawa, da alkawarin duk bayan wata shida zata na zuwa tana jin labarin Rabi’ah.

  Yar Duwala.
Tun lokacin da Adizah ta kira ta, tare da gaya mata ai ga halin da aka kawo Sahurah ta canja unguwa, tare da kiran matar da ta amshi Rabi’ah ta gaya mata  inda take.

Zaune suke a farfajiyar gidan, Dr Musa yana kallon ta kafin ya ce mata.
“Amma baki da kirki yarinyar da bata da lafiya zaki turata aikatau? Yanzun don Allah Meyer amfanin haka? Gaskiya ba a mata adalci ba.”
“Musa kasan ina sane da abubuwan da kake min na share ka? Toh babu ruwan ka da Rabi’ah.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button