WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
   Kanta a sunkuye tana jin abinda Mommah take fada, har lokacin kukan da take na kewar wasu ne ba na gidan bane,, ta rasa gane su waye ta manta, su waye take kewar su har haka. Sai da Mrs Uchanna Jeshua ta ce mata.
“Shiga cikin ko” a hankali ya shiga cikin motar, tana d’agawa Mss Folina hannu, har suka fara kokarin tafiya, juyar da kai tayi tana jin hawaye na zuba mata.
  TOH mai karatu yanzun zan bar Jaruma ta cigaba da labarin ta, yadda nake kowani labarin sai dai ayi hakuri da typing error da rashin editing 🤣😼🥺😆
*
REBECCA
Tafiya ne nisan da ban san inda zamu tafi ba, ban san kowa ba, ina son na tuno abinda ya faru na manta, Ina ne zamu? Ina ne zasu kai ni? Ban sani ba,  kwanciya nayi tare da lumshe idanuna, ina son tuno wani abun da yake giftawa ta idanu na, da zaran nayi kokarin haka kawai sai naji kaina ya fara sara min dan haka na lumshe idanuna, na fara barcin dole me ɗauke da wasu irin mafarki.
  Karfe bakwai na dare muka shiga cikin wani gari bayan mun ci Uban go slow me tarin yawa, kafin na shiga raba idanu na,.ina kallon garin kamar wani duniya ko ina hasken lantarki ga gine gine masu tsawo da kyau, haka muka yi ta wuce gine gine masu kyau irin benen nan me dauri da dauri.
Karfe takwas min shiga wani gida ba za a ce mishi katafare ba, amma gidan ya hadu babu laifi, wasu matasa maza biyu ne a gidan sai wata mace.
“Barkan ku da gida?” Inji matar da suka tawo dani, ina bin bayanta kamar jela, ina makale da kayana dake cikin bakar ledar viva.
“Ruth kamar Yar Fulani mika dauko mana?” Inji matar tana hararana. Cikin girmamawa matar ta ce mata.
“Aunty Bafa Fulani bane, kawai yanayin ta ne haka, kuma kisan Staven yana hanya, shi ya bukaci haka dan Allah kar ki ce mata miki ba” ta fada kamar a dame.
Cikin hargagi ta mike tare da nufar Rabi’ah ko nace Rebecca, ta zungure goshinta. Tana hararana ta kamar zata buga ta.tana. Wucewa sauran matasa mazan suka ce mata.
“Aunty Sai hakuri amma kin san halin Maman Staven halin ta sai ita babu me iya mata, sai Allah yadda kika san idan na tafi Services kar na dawo, domin na gaji da zaman gidan nan, Staven kawai take d’agawa kafa amma mu kamar ba ita ta haife mu ba, shi yasa idan na tafi bata. kuma gani.na.
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
Mai_Dambu
3/1/22, 18:55 – Nuriyyat: Albishir ku.. kuce min goro...ko kusan S.squar Fashion &More Sun kuma kawo muku ingantattun kayan su masu kyau da rahuwasa... Turaren wuta na zamani. Milk candy Hijabs da gowns tare da kayan Yaran ku masu kyau da inganci zaku iya tuntubar wannan number👇ðŸ¾ðŸ’ƒðŸ¼Http://wa.me/+234 703 003 7697
29
Mr Uchanna Jeshua.
Asalin shi É—an garin Anambra ne, mahaifin shi, amma ma zauna garin abuja a unguwar Gwarumpa,. Sakamakon aikin da yake na gwamnati da kuma kasuwanci, Mr Uchanna Yana da Kani Obinna Uchanna Jeshua, sai dai sunan shi bai fito ba kamar na Dan uwansa sai aka fi sanin shi sa Jeshua,
Mary ita ce matar Uchanna, sun yi aure har da Yara uku maza, Steven Ikenna da Ennamani. Dukkan su, suna da abinyi kasancewar Mr Uchanna ya mutu shekara daya da ya wuce, Steven Yana aiki a jami’ar Carolina dake Æ™asar Amurika, bai yi aure ba, dana duk shekara yana zuwa Hutu.
    kanin Mr Uchanna bai tab’a haihu ba, tunda ya auro matar shi me suna Ruth, kusan shekaran su goma sha biyar kenan, mutuniyar Steven ce, shi ya bata shawaran ta dauko Yarinya daga gidan marayu wanda zai zame mata kamar nata,. wannan abin ba karamin dadi yayi mata ba, sannan ya gayawa Uncle din shi yadda suka yi, shima yayi na’am da haka, toh inda gizo yake saka Madam Mary wacce sunan ta na Yaren Igbo Enedo. Yar bala’i ce, wasu na alakanta mutuwar mijinta da Masifar ta ce ta janyo haka, domin an ga kiranta lokacin.da zai yi hatsari, domin har lokacin bata fasa Masifa da Bala’i ba.
  A duniya babu abinda Madam Mary take so kamar Steven tana kaunar shi kamar rai da gangan jiki, shi yasa addu’ointa baki daya Allah ya kare mata danta daga sharrin mutanen banza.
Sauran yaran kuwa ba wai bata son su bane, domin babu uwar da zata haifi da tace mata son shi basu kai Steven matsayi bane, kawai tana son su daidai wa daida.
   Sannan tun daga ganin Rabi’ah wacce yanzun ta koma Rebecca take jin kamar ta kashe ta, zunzurutun kiyyyar da take ji a kanta.
Sannan duk da wannan yanayin na ta, babu laifi tana zaune lafiya da makotanta, musamman gefen dama inda take da makota mijin dan Yola ne matar Yar Gombe. Wato Dr Hayat Abdulwahab da Matar shi Hajiya Rumanah Hayat Abdulwahab.
**
Dutse
Wata Kyakkyawar Mace ce zaune, tana kallon su Kafin ta mike.
“Ku dauki kayan Yarinyar ku kaiwa danginta kusan yadda zai shiga hannun su, tare da basu labarin Yarinyar ta mutu.ko kusan inda zaku same ta ne?”ta tambaye su, girgiza kai suka yi tare da amsa mata.
“A’a”
“Dr Musa fa”
“Ranki shi dade mun rufe babin shi”
“Da kyau, dan haka maza a aika musu da sakon gidan da take aiki sun yi gobara sun mutu baki daya.”
“Toh” suka fada tare da barin falon, sannan ta juya ga Yar Duwala ta ce mata.
“Zamu bar garin nan an gama aikin shi, matukar aka cigaba toh hukumar kare hakkin dan Adam zasu fahimci muna nan dan haka kwana biyu ki tattara ki bar garin nan kafin su dira Miki.
“Toh Hajiya Adizah!” Wannan yanayin da Adizah ta gaya mata bata da zabin da ya wuce ta koma Kano tunda tana da gida a can, kuma babu laifi can ma tana samun na uzurin ta babu damuwa zata gwada tattara kome ta koma can da zama dan zai fi mata sauki yadda zata rayuwar ta cikin farin ciki da walwala.
**
Lagos
A gajiye suka shigo cikin gidan, yarda jakar makarantar Wasilah tayi tana faÉ—in.
“Ammyn Barka da gida! Ayi a gaji da wani abu ina jin yunwa” tsaki Rahmah ta ja, tare da nufar kitchen. Rungume Ammyn tayi tana murmushin jin dadi.
“Ammyn Barka da gida, ya aiki?”
“Alhamdulillahi, Rahmatullah ya karatu ina Sarkin ci.” Wucewa cikin kitchen din tayi tare da É—aukar kofi tayi tana me zuba cornflakes sannan ta zuba ruwa kaÉ—an kafin ta zuba mishi madara.
 Da sugar tana murmushi, kadan kadan kafin ta juya zuwa waje, ta zauna tana sha, tana wasa da kofin.
“Rahmah me aka samu ne haka?” Ammyn ta tambaye ta, domin tasan duk cikin Yaranta babu me rayuwa cikin farin ciki kome kashin sa, bata hanata walwala.
Murmushi tayi a karo na biyu ta ce mata.
“Babu Ammyn mu”
“Anya zan yarda kuwa? Domin murmushin tana kama da wanda yake cikin farin ciki”
  Tashi yayi bayan ta gama shanye cornflakes din ta,. Tana faɗin.
“Allah babu kome” ta fada tare da nufar kitchen.
Wasilah da take cikin abincin ta, a nutse ta ce.
“Ammyn ina Yaya Jamilah?”
“Tana dakin ku” sai da ta gama ci sannan ta nufi dakin tana kallon Jamilah da take kwance tana karanta book.
“Yaya Jamilah ko zaki min wannan aikin?” Ta tambaye ta, tashi tayi tare da amsa tana dubawa, kafin tace mata.
“Ki samu Rahmah itace take da kokari akan Science ni Art class ce”
“Toh ai na mata rashin mutunci ne tace ba zata min ba, don Allah ki bata hakuri”
“Shi kenan zan bata hakuri” sannan ta wuce abinta, tana cewa.
“Yawwa Nagode” ta nufi ban daki.