WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
Sai da Teacher Abdullahi ya buga mata kofa ta bude tana kallon shi.
“Kinsan zamu tafi karfe bakwai”
“TOH” ta fada sannan ta koma cikin ban dakin tayi wanka sannan ta shirya cikin wasu unifoam din, ta fita tsaf da ita, kamar an ce ta juya inda eveltor yake ta hango shi zai shiga da sauri ta dauke kanta, tsabar tsoro bata lura ba ma, fitowa Teacher Abdullahi yayi dan gaba dashi, Teacher Fashola ya fito.
 Gaishe su tayi sannan suka nufi wurin karyawa,duk abinda take karfin hali ce, domin baki daya ta kasa nutsuwa,haka taci abincin kamar wacce bata so, sannan suka nufi inda Motar kungiyar da ta dauki nauyin gasar, suka tafi.
  Kwantar da kanta tayi tana jin wani irin faduwar gaba, a hankali ta d’ago kanta, tana me kallon shi a cikin wata bakar Nissan rogue, sunkuyar da kai tayi tare da jin baki daya jikinta yana rawa.
    Bata kuma sarewa fatalwan shi ne yake Binta ba, sai da aka fara abinda ya kawo su, kawai tana gab da lashe gasar ya bayyana, cikin wani irin tsoro ta damke skirt dinta, tana jan wani irin kuka, tana basu amsa. Tana bada amsar karshe ta tashi da gudu ta fita, zuwa restroom a gaban madubi ta tsaya tana me sake kukanta. Zuwa yayi ya bayan ta, kamar me goge ban dakin ya saka mata abu a hancinta, take ta zube a jikin shi, janyo wani abu yayi ya sakata. Sannan ya tura abin ya fita da ita.
Baki daya ya renawa mutane hankali ya tafi fa ita, har can wani karamin hotel. Ajiye ta yayi sannan ya juyo mata ruwan sanyi a kanta, wani irin jan numfashi tayi tana kallon shi a mugun firgice ta farka.
Kare fuskar ta da hannn ta.
“Keee!” Ya daka mata tsawa,
A matukar firgice ta hadiye kukanta.
“Don Allah kayi hakuri kaji wallahi ban ga kome ba”
“Ki min shiru na ce” ya kuma daka mata tsawa, sunkuyar da kai tayi cikin kuka da mugun tausayin ka.
“Kayi hakuri don Allah kaji ba zan kuma maka haka ba”
“Dawa dawa kika gayawa?”
Cikin shashekar kuka ta ce.
“Wallahi ban gayawa kowa ba, daga Ni sai Allah.”
Matsowa yai tayi baya tana girgiza mishi kai.
“Kayi hakuri kaji wallahi idan wani abu ta faru da ni again wallahi billahi azim mutuwa Ammyn zata yi don Allah ka barni muji da zafin halin da muke ciki.”
Tausayi ya bashi ya ce mata.
“Ok kiyi shiru babu abinda zai Miki” shiru tayi jikin ta babu inda baya rawa, kallon yadda ga firgita yayi sannan ya ce mata.
“Tashi muje” a hankali ta mike daga zaune jiri na diban ta koma ta zauna,
“Wallahi i can walk” kallon ta yayi tare da zabga mata harara ya ce mata.
“Toh me zan Miki?”
Ya tambaye ta a masifance, sake daurewa tayi ta mike, ta fara tafiya a hankali luuu ta tafi zata zube ya tare ta, ta sauka a hannun shi. Wani irin luuuuu tayi da idanunta. Ya tab’a kumatun ta, kallon lokacin da ya diba yayi,da sauri ya dauke ta tare da kai ta makarantar bayan ya kuma mai da kayan da ya dauko ta dashi.
  Yana ganin malaman ta suna kokarin buga kofar, ya tura abin da yazo dashi domin shigar cleaner yayi. Bashi hanya yayi yana shiga ya kwantar fa ita, kafin ya fara kamar yana aiki can ya fito da sauri yana haki.
“Wata ta fadi a cikin ban daki” da sauri suka shiga ban dakin har da shi, suka fito da ita a hankali, tare da fita daga hall din da ita, Teacher Fashola yayi report din abinda ya faru, sannan suka tafi da ita asibiti bayan sun kira motar asibiti. Ajiyar zuciya yayi baki daya zuciyar shi tayi nauyi.
Haka ya bisu har asibitin ya nufi inda suke, yana jin ana musu bayanin babu kome damuwa ce da kuma ta shaki kamar wani abu ne ya sakata suma, juyawa yayi abin shi, tare da nufar waje. Baki daya ji yake gwara ya tafi ya barta tayi abinda ya kawo ta, idan ba haka ba yadda take da matukar tsoro ba zata yi kome ba.
 Da wannan tunanin ya baro Japan.
**
Abuja
“What?” Maman Steven ta fada tana mikewa.
“Kinga abinda nake gaya Miki ba? Na haifarwa Fulani girl yaro wai da ita zai tafi amerika, ni da na haife shi bai yi tunanin tafiya dani ba”
“Steven ka kyauta tashi ka je xan yi magana da mamanka wannan abinda ka yi ba karamin alkhairi bane jeka zamu yi magana kaji karka damu zata Barka ku tafi da Rebecca”
“Thank you ma” ya fada bayan ya bar dakin, yana godiya, sai ya fita Madam Fater ta zabga mata harara cikin fada ta ce mata.
“Baki da hankali yau na tabbatar da haka, waye ya gaya Miki ai fasa abinda yayi niyya ne? Ba haka ake hukunta mutum ba, kawo kunnen ki na gaya miki yadda zaki yi” tana kai mata kunnen ta, ta gaya mata wani zaro idanu tayi tana sake wata irin murmushi me cike da manufofin ta zasu cika.
“Da ihun da kike yi, why not ki tura shi can Anambra ya gaida Uncle din shi Emeka, sannan ya musu koda kwana biyu ne sai yayi a can amma kina tadda jijjiyar wuya kamar baki zauna a bariki ba,.gaskiya ya kamata ki kara wayewa domin abinda kike ba irin na cikakkun masu hankali ne.”
“Kina zagina ne fa kawata, domin dai wannan zagi ne, babu kome a cikin shi saai zagi.
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
Mai_Dambu
3/1/22, 18:56 – Nuriyyat: 34
“Akan me zan zage ki? Yabon ki nake idan bai miki ba nayi tafiyata,.hanyar arziki nake nima miki amma dakikiyar Æ™waÆ™walwar ki bata baki haka ba.” Mikewa tayi zata fita ta riko hannun ta, tana me kallon ta cikin damuwa ta ce mata.
“Kiyi hakuri ba zan kuma ba, duk abinda kika yanke daya ne”
  “Toh Babu damuwa idan ya tafi sai ki kira ni nazo mu tafi” inji Madam Fater.
“Toh Aminayar arziki, Nagode fa” haka suka fita suna hira Madam Fater na kara xigata da yadda zata tafi da kome har suka fito daga waje. Sun same mu da Steven yana aiki da laptop din shi, ni kuma ina gefe jingine da pillow, hannuna rike da apple.
“Sannun Steven Ashe kun dawo ya me jikin kuma?” Fuska a daure ya ce mata.
“Fine” ya cigaba da abinda yake bai kuma bin ta kan su ba, har suka fita kallon Maman shi tayi sannan ta ce mata.
“Hmm! This Fulani girl, sai kin yi da gaske ki raba shi da ita.”
“Kai kamar baki yarda dani bane, kawai saka idanu nan da kwana uku zan kira ki” ta fada sannan suka karasa bakin hanya, sai da ta hau mashin sannan ta dawo daga rakiyar ta.
   Kallon shi nayi tare da jan rigar shi, juyawa yayi ya kalle yana me d’age min gira daya.
“Na koshi.” Na mika mishi apple din, amsa yayi tare da ajiyewa a gefen shi, a hankali na kwanta tare da juya mishi baya. Ban jima ba barci ya dauke ni, murmushi yayi lokacin da ya kirani yaji ban amsa ba.
“Rebecca!!” Ya kuma kirana, yaji shiru, É—aukar apple din yayi ya kai daidai inda bakina yake ya gutsira a hankali yana ci yana jin wani abu na fisgar shi har ya gama ci daidai shigowar Maman shi.
Bata ce mishi kome ba ta shige part din ta, har yamma wajen karfe shida ta fito ta daura abincin dare, doya da miya, wanda ya sha dry fish. Ba karamin kyau yayi ba domin. Baki daya sai da gidan ya dauki kamshin ana girki,
Har zuwa lokacin ban farka ba, shima kuma bai tashe ni ba, sai dai mafarkin da nake ne ya sani na fara kuka, wai gani a wani daki me mugun duhu. Ko tafin hannu na bayana gani.
“Rabi’ah!!!” Aka kira suna na, juyawa nayi wata mata ne, da fitila a hannun ta. Ban ga fuskar ta ba, gefen ta wasu ne suma ban ga fuskar su ba, ja da baya nayi.
“Zo muje gida”
“A’a” na fada da karfi, sannan na juya da gudu. Sai dai duk gudun da nake kamar a wuri guda nake, juyawa nayi naga suna nan a wurin har yanzun.