NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Kashe wayar yayi tare da wurgi da ita domin yana cikin b’acin rai ne bayan son magana ko kadan, ita kuma zata kara kunna mishi wata b’acin rai da yake ji, dafe gashi yayi yana faÉ—in.

“Na gaji da kome wallahi kamar na gudu na bar kasar nake ji” ya fada a sanyayye.
**
Monday
Wanda yayi kwana huÉ—u da dawowarta, saka unifoam tayi ta fito daga cikin dakin su, ta zauna tana kallon Ammyn da Wasilah. Sai Jamila da itama zata wurin Jarabawar Jamb dinta. a yau.
“Ramcy ya dai?”
“Hmm! Babu Ammyn yau na tashi da kewar Beeyah ne, wallahi ina matukar kewar ta.” Ya fada tana share kwalla.
“Allah yana sane, yana ji yana gani ba zan yi kuka dayawa ba, amma nasan ko bana raye zata dawo da Yardan Allah”

Shiru Jamilah tayi domin tasan sanadin rashin lafiyarta ne ya janyo batar Autar su..
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/1/22, 18:56 – Nuriyyat: 35
“Ku shirya ku tafi babu lokacin,, domin zaku iya kara.” Ammyn ta fada musu, tana me barin falon, haka suka shirya amma Rahmo bata samu karyawa ba sai tea ta diba a mug ta tafi da shi. Su Jadwah da Jawahir suka fito suma,kallon juna suka yi sunawa Wasilah tsiya.

Bata wani kula su ba, har suka ajiye Jamilah, sannan aka wuce da su makarantarta, sai da aka fara ajiye Jadwah da Jawahir, sannan aka tafi dasu na su makarantar. Tana shiga makarantar dalibai dayawa suka fara ihu da murna, har aka shiga ajin su. Shigowar Teacher Abdullahi ran shi a b’ace ya tawo gabanta, ya tsaya tare da daka mata tsawa.
“Waye Barista Faisal Abdul Hadi Shema?” A matuÆ™ar razane ta mike, tana kame kame.
“Kiyi wuce shugaban makaranta tana kiran ki” da sauri ta fita tare da nurse office din shugaban makarantar, tana zaune wasu mutane biyu suma suna kallon ta, ta shiga kanta a sunkuye..
“Gani Ma”

“Rahmah Ishaq DaÆ™ayyawa ko?” Ta kuma tambyar ta,
“Yes Ma”
“Ina tayaki murna da kuma jin dadin nasarar da kika dauko mana, da wannan abinda kika samo mana makarantar Jikamshi Model school sun bukaci ki koma can da karatu”

Da sauri ta kalli Shugaban makarantar tana me matukar tsoro,
“Am…”
“Gasu nan zasu tafi dake” daga haka ta kalli mutane biyun, ta ce musu.
“Gata nan Allah ya bada sa’a”
“Me yasa ba a gayawa Iyaye na ba? Ko kawai fadowa nayi daga sama? Gaskiya a zan tafi ba, sai ba gayawa iyayena abinda suka yanke a kaina daidai ne” daga haka ta juya abin ta,  barin office din tayi sannan ta koma aji, sai a lokacin kwalla ya xubo mata tana son tuna a ina ta tab’a jin sunan makarantar Jikamshi nan, ganin zata da  takura kanta yasa ta share ta cigaba da sauraron malamin da yake ajin su.

Baki daya bata fahimci abinda ake koyarwa a cikin ajin haka dai, har aka tashi bata san me ya faru..

**
Nadrah Ali Ruma.

“Irfan don Allah mu tsayar da wannan relationship É—in wallahi bana son haka don mu tsayar da shi haka”

    Takowa yayi gaban ta, yana kallon fuskarta cikin b’acin rai ya ce mata.
“Gaya min meye na gaza miki? Ina sonki sosai.”
“Amma ni Mommy ta min miji, ya zan yi da kai? Don Allah stop it”

    Fisgota yayi jikin shi, tana kokarin yakin shi, ya had’a bakin su yana mata wani French crazy kiss, kamar zai cinye bakinta, hannun shi yana yawo a jikin ta, cikin tsananin b’acin rai ta kwace jikin shi tare da kifa mishi mari. Cak ya dauke wuta yana kallon fuskarta unbliever shafa cheer din shi yayi tare da sake mata wani banzan killer smile.
“You slap me?” Ya tambaye ta, sai lokacin wani irin tsoro ya kama ta.

Nuna mata hanya yayi tare da cewa.
“Jeki” ya fada yana wani irin huci, tare da juya mata ba, yana cizon lip din shi na kasa, wani irin dunkule hannun shi yayi yana ji kamar ya juya yayi ta kwallo da ita, amma ya rarrashi kan shi. Amma sai ya bata mamaki inshallah.

   Jikinta a sanyayye ta fita tana share kwalla, domin kuwa bata kawo zai kyale ta ba, dan haka dukkan su kowa yayi zuciya da dan uwan shi.

A bangaren Irfan kuwa zuciyar shi ce tayi zafi kamar zata buga, domin yana jin kamar ya cire ya huta, dan haka yaji a ran shi zai rabu da ita, kodan abinda tayi mishi dole ya rabu da ita, ba zai iya dukar mace ba, amma dole sai tayi kukan abinda tayi mishi.

**
Korea

Alhamdulillahi jikin Ummi yayi sauki, kallon Bilal tayi da suke magana da ita ta video call.
“Eh akwai abinda nake ganin yake damun su, sannan idan aka ce za ayi fito na fito da su, ba mamaki haka zai iya affected din marketing na shareholders din JF Group. Abinda za ayi kawai ka gama kome a nutse idan na dawo sai musan abin yi amma tabbas da wannan yanayin ya isa ya ruguza JF Group.” Ta fada tana kallon shi.
“Duk yadda kika ce, ki gaida min Umma zanzo karshen shekara inshallah sai na kammala kome.”

   “Toh babu damuwa”

**

Lokacin da aka tashi suka dawo gida, kamar mara lafiya haka Rahmah take tafiya, har zuwa falo.
“Lafiya?” Kallon Ammyn tai tare da sake jakarta ta fada jikin ta tana jan shashekar kuka.
“Lafiya? Meye ya faru dake?”
“Ammyn ban san Meye ya faru ba, wai wai sun sauya min makaranta” ta kuma rushewa da kuka,
“Toh wani abu ga faru ne a lokacin tafiyar ku” rike hannun Ammyn tayi tana zare ido, cikin azababben tsoro.
“Wallahi ban san kome ba, kawai bude idanu nayi naga ya sace Ni”

Rike hannunta Ammyn tayi tana kallon cikin su, cikin tsannanin b’acin rai ta kifa mata mari.
“Wani ya sace ki? Amma kika kasa buÉ—e bakin ki,.ki gaya min? Ikon Allah Meye nayi na cancanci azabtawa daga gare ku? Na zata Kinyi hankali ashe mahaukaciya nake tare da ita? Yayi duk abinda kika kwaso wallahi ki nime wata.”

“Ammyn!” Jamilah ta kira sunanta.
“Akan me? Waye ya isa ya tserewa kaddaran shi? Na zata iya yanzun an wuce haka, don Allah kar ki mana baki domin zai cigaba da bibiyar rayuwar mu har mu koma ga Allah” ta taso tare da d’aga kafadar Rahmah, suka wuce dakin su. Tana kuka,

“Waye ne shi?” Jamilah ta tambaye ta,
“Wallahi ban san cikakken sunan shi ba, kawai dai ya saka ni a gaba ne.”
Shiru tayi kanta a sunkuye, tana shashekar kuka,
*Meye ya faru?” Nan ta kwashe Abinda ya faru a airport ta bata labarin.

“Toh sai ki iya bakin ki, domin idan taji haka ba zata yarda ki cigaba da karatu ba.” Inji Jamilah,  fita tayi daga dakin ta nufi wurin Ammyn, zama tayi tana kallon kasa.
“Kiyi hakuri, Rahmah bata san kome ba. Don Allah kiyi hakuri ba zata kuma ba, kin ji Ammyn mu, don Allah mu ci albarkacin Autar ki”

Murmushi tayi tana me kamo hannunta.
“Mutuncin ku nake karewa, idan ban yi fushi ba me zan yi, a ce har an sace ta bata gaya min ba, ji nake kamar ku fasa karatun nan kullum tsoro ne yake cika Zuciyata, gani nake kamar wani zai iya cutar da ku, shi yasa nake ganin keba zaki tafi wani waje karatu ba, kiyi anan zan fi samun nutsuwa Hankalina zai kwanta”

“Ammyn mu duk inda kika zab’a mana zamu yi karatu ki mana addu’a Allah ya kare mu, insha Allah babu abinda zai faru damu”
“Allah yasa ya kuma kare ku daga mugun ji da mugun gani”

   Har dare Rahmah tana dakin su, bata fito ba, sai can ta fito shima dan tana jin yunwa ne, ta fito ta dafa Indomie ta koma dakin.

Washi gari.

Kin kwanciyarta tayi tana barci domin bata ji a ran ta, ta tafi makaranta ba, sai da Ammyn ta shigo dakin ta samu tana barci ga motar makarantar yana kofar gidan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button