WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
Mai_Dambu
3/1/22, 18:56 – Nuriyyat: 37
Steven
“Kin kashe ni Mama kin gama da Rayuwata, Rebecca itace rayuwata, amma dan rashin Imani kuka sayar da ita kamar yar akuya, ina laifin ki ce baki son na tafi da ita ba wai ki sayar da ita ba, Ashe kiyayyar da kike mata har ya kai haka, Nagode Mama”
Ya fada tare da komawa ya kwanta, yana zubda kwalla baki daya ya tsani kan shi, bai san me yasa maman shi ta yanke wannan mugun danyen aikin ba, koda Kawun shi da Obinna suka zo bai ce musu kome ba, dake Maman ta fita.
“Obi idan kaje gida ka dauko min passport dina da kayana, ka kawo min kaji”
“Ok” daga haka bai kuma magana ba, yana zauna sai kallon Kawun shi da matar sa yake, har suka bar dakin.
A daren Obi ya kawo mishi kayan shi, ya tafi idan ake biyan kudin asibiti ya biya Bill din shi, sannan Obinna ya raka shi airport, sai kusan karfe goma na dare jirgin Lagos ya tashi da shi, tafiyar kenan da yayi tare da alkawarin niman Rabi’ah idan ya koma U.s yasan shiga italiya ba zai bashi wahala ba.
**
Rebecca
Tafiyar da muka fara ba zance tana da dadi ba, amma tafi kome wahala, domin tunda muka kutsa sahara motar take falla gudu, duk da muna bayan motar ne a zaune,.kuma a takure ga isar sahara me É—auke sa yashi, haka muka kwana muka wani. Ga zafin rana, wasu a cikin mu har sun fara rashin lafiya.
Kwanan mu biyar motar mu ta samu matsala, Allah sarki. Anan ne aka bamu ruwa a wasu irin gorina, tare da gaya mana cewa.
“Wannan ruwan zai kai ku kwana uku zuwa hudu idan mun gama gyaran zamu iso ku akan lokaci”
  Sahara ga zafi ga bala’in guguwa,.idan ta kwaso yashi haka zai nutsa da mutane. Inji Aunty Blessing.
“Aunty Kuma haka zamu keta shi?”
“Eh haka zamu wuce a cikin shi”
“Eh Rebecca, wannan tafiyar sai dai muce Allah ya fidda mu” haka ta riko hannuna muka fara tafiya, dake da yamma ne, haka kuma saka kai domin babu damar kwanciya a hanya, haka muka yi ta tafiya har dare ya raba. Kafin goshin Asuba mun yi tafiyar kilomita dari da hamsin.
  Mun gashi sosai,.har gari ya waye babu bakin magana, kallon Aunty Blessing nayi nace mata.
“Aunty Ina jin Æ™ishirwa” kallon abokan tafiyar mu tayi, sannan ta ce min.
“Kiyi hakuri idan na baki yanzun mutane zasu saka mana ido.” Gyada mata kai nayi muka cigaba da tafiya sai da muka yi tafiyar wuni guda, zunzurutun Æ™ishirwa wasu haka suka yi ta suma, sai da aka basu ruwa, sannan aka raba mana busashen burodi, muka ci muka kuma kurb’an ruwan, hutawa muka yi kafin aka cigaba da tafiiya, kafaffuwar mu sun kumbura. Kai tafiyar babu dad’i domin baki daya bamu da karfi, haka muka kwashi kwanaki uku muna tafiya.
A cikin mu mutane biyu sun mutu, haka muka bar gawarwakin su, a nan angulu zasu sha lagwada, a cikin tafiyar dama mun hadu da wasu kwarangwal din mutane, Aunty take gaya min cewa ai Æ™ishirwa ya kashe su, wannan abin ya d’aga mana hankali kallonta nayi sannan nace mata.
“Aunty amma kin tab’a wannan tafiyar ba shine na farko ba?”
“Eh na tab’a, sai dai kasar mu ne da babu samu yasa ba zabi zuwa Æ™asashen turai domin niman abincin”
   “Haba shi yasa na fahimci haka,” kusan tunda muka fara tafiya babu mata a tafiyar sai ni da Aunty, amma da muka yi tafiyar kwana biyar cif Anan muka kuma haduwa da wata motar me É—auke da yan mata shi ma ta b’aci, dan mugunta sai gashi ni da Aunty Muna dariya, dan haka kallon su muka yi tare da cewa.
“Maza kuzo mu taka ai yanzu mun zama uwa daya uba daya,” tafawa muka yi da Aunty.
“Kusan kwana nawa ya rage mu shiga Libya?”
“Kwana biyar zuwa shida” aunty Ta gaya musu, a take suka dauki kayan su, suka goya muka kara daukar hanya.
“Aunty me yasa motar yake samun Matsala?”
“Zafin sahara da kuma tukin da suke mishi dole injin ya tabu” ta gaya min, gyada kai nayi tare da kallon yan matan da suke gefen mu.
“Aunty”
“Rebecca ki huta don Allah”
Shiru nayi ban kuma mata magana ba. Har muka kwana a hanya, sannan muka cigaba da tafiiya, nan ma mun yi masifar galabaita,
A kwana na biyar ne wanda gamu da iyakar Libya da nijar, muka zube a wurin Allah ya taimaka da asuba ne, mun shanye ruwan mu, babu kome a goran mu, dole muka suma a wurin sai da gari ya waye ne akwai Yar karamar camp aka dauke mu, zuwa cikin shi, aka mana maganin gaggawa tunda ba zama zama yi ba, haka aka gama mana bayan mun farka muka ci abincin, sannan da dare muka tsallaka kasar Libya.
  A daren aka so mu wasu su wuce Algeriya amma hukumar kasar ta hana a shigar mata kasa, dan dole muka wuce gabar tekun kasar, wanda shine tafiya mafi hatsari da tashin hankali, dan haka muna fara tafiya, sai da muka kwashe awa goma sha uku saboda fadace fadacen da ake a kasar,. kafin muka isa bakin gaɓɓar wanda yake karkashin jagorancin yan tawayen kasar,.muna zuwa wurin suka shiga bude wuta dan haka muka kwanta, jakunan mu suka ɗauka tare da zazzage shi, hodar iblis ce a cikin shi, sai wasu drugs sai harsashi babu iyaka, babu wanda yasan akwai abinda suka samu a cikin kayan mu, dan haka haka suka nuna mana wasu cantainer,.muka shiga cikin shi,.suka rufe mu rub.
  “Aunty Me yasa aka rufe mu?” Na tambaye ta a mutukar tsora ce.
“Akwai dalili, hukumar tsaro zasu iya zuwa, dan haka dole kowa ya kwanta” haka muka kwanta, aikuwa kamar yadda suka fada sai ga Hukumar tsaron sun zo, da farko an yi bata kashi tsakanin su, daga baya kuma aka bude mu, abin mamaki wasu mutane na daban aka kashe.
“Captain ka duba yan matan nan zamu rage zafi da su” a tsorace na koma jikin Aunty na tsaya, haka aka zabi yan mata goma a cikin su, ban da Aunty. Kara rungume ni tayi daga ni har ita muna kuka. Sakamakon yadda yan matan nan ke ihun, wani irin abu naji yana yawo a kaina, sake k’amk’ame Aunty nayi, suna gama lalata dasu, suka fito tare da kiran mutanen da zasu dauke mu a jirgin ruwa,dama akwai jiragen a wurin kawai ba zasu bamu bane sai sojojin sun zo sun kwashi rabon shi.
“Ke” daya daga cikin yan tawayen ya nuna Aunty, a razane ta kalle shi.
“Kin fi kowa ne da zaki wuce babu wanda ya bukaci haka.daga gare ki?”
    Ban san me ta ciro ba, amma nuna mishi wani abu a gefen wuyarta, dauke kai yayi tare da cewa.
“Sai tafi ai” haka muka shiga cikin jirgin ruwan da ya dace ya dauki mutane biyar shida sai gashi an mishi labta mishi sama da mutane goma sha biyar. Haka kuma a yadda Aunty take gaya min akwai irin katun-katun kifaye masu cinye mutum, tun da na shiga ruwan na kira kaina, a kirjin Aunty, jirage goma sha biyu suna tashi a bakin tekun, muka fara tafiya, sannan bai zama dole mu tsallaka da rai ko lafiyar mu ba.
**
Bilal Jikamshi.
An gama gyaran kamfani tare da kintsa kome, sannan aka tura sanarwar dawowan ma’aikatan kamfanin. A ranar da aka fara dawowa aka yi board meeting baki daya duk wasu masu ruwa da tsaki na JF Group suna cikin meeting din.
  “Bamu san me yasa ka tara mu ba a nan kasan kowa yana da abin yi ko?” Inji Alhaji Abubakar,
“Eh toh idan kayi hakuri zaka gani” kallon su yayi sannan ya ce musu.
“A ranar daya ga watan da ta wuce an samu cigaba da ban yi mamaki ba, domin a É“angaren kasuwancin mu a hannun jarin an samu 1.0% wanda idan da zamu duba yanayin kasuwan hannun jari ya fadi, sai gashi ta É“angaren kasuwancin hannun jarin da muka fitar ya samu cigaba na ban mamaki. Sai dai kuma kamfanin tana bukatar ma’aikata tare da kara musu albashi.”