WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
 “An me zamu kara musu albashi su? Haba ba zai yiwu ba, sannan maganar diban sabin ma’aikata Nadrah zata fara aiki anan;” inji Hajiya Turai,
   “Suhaima Kabir Wazir da Zuhairah Kabir Tambuwal zasu fara aiki anan kamfanin” inji Hajiya Shuwa, tagumi yayi yana kallon su, dan bai san me zai ce musu ba, a hankali ya mike tare da cewa.
“Kusan ina da abin yi, ba zaman ku nake ba,asalima kanfanoni na shekara me zuwa zasu fara aiki, so idan yayi muku kyau ku gyara kome min ku idan bai muku ba matsalar ku ce” ya juya yana kallon Hajiya Atikah, hannun shi daya cikin Aljuhun wandon shi ya ce mata.
“Ummin mu, ki duba abinda ya dace idan zaki debi sabin ma’aikata babu son kai babu son zuciya sannan kar a Kore tsof…”
“Kai Bilal Meyer nufin ka?” Inji Alhaji Abdulkadir, ya fadi bayan ya buga tabirin.
Juyawa yayi yana kallon shi, kafin ta ce mishi.
“Babu kome” daga haka ya juya ya fita a dakin taron, yana fita suna haduwa da Irfan Kabir Wazir da Nadrah, alamar ma fada suke. Dauke kai yayi tare da mai da hankalin shi kan wayar shi.
“Oppa!” Ta kira sunan shi a hankali, cak ya tsaya da sauri ta kwace hannunta a wurin Irfan ta tawo wurin shi tana faÉ—in.
“Ina kwana?”
“Lafiya lau” ya juya yana kallon Irfan sa fuskar shi tayi jajjur,
“Your boyfriend!” Tab’e baki tayi tare da cewa.
*Dan mutunci ne ba boyfriend ba, muje mana” ta nuna mishi hanya.
“Kayi hakuri ban maka ta’aziya mutuwar Ha Na da Yoo ba, ya hakuri” murmushi yayi sannan ya ce mata.
“Alhamdulillahi! Ya karatun?”
“Na gama sai dai zan koma master Insha Allah, daga nan idan na dawo kuma na fara aiki”
“Next kuma sai zama Mrs Irfan Kabir Wazir” tura baki tayi tare da cewa.
“A’a ba dai shi ba” ta fada a hankali,
“Ai kice kema kin soma Yaudaran samari?” Ya fada bayan ya latsa key motar shi. Budewa escort din shi suka yi tare da kallon shi.
“Sir”
“A’a yau ni daya zan fita” tsagal Nadrah tayi tana fadin.
“Tare da dai” ta wuce daya side din shi ta shiga shima ya shiga.
A hankali ya fitar da motar yana ja a sanyayye, yana kallon hanya, har suka fita a area din kamfanin.
Makarantar su ya wuce tana kallon shi har suka isa makarantar ganin yaki bata fuskar ayi magana yasa tayi shiru.
Yana shiga ya hango motar mutumin shi, yana parking lot shima ajiye nashi yayi yana murmushi, fita yayi itama ta fito,kallon juna suka yi.
    A tare suka wuce office din Humaidah. Yana shiga ya samu iyayen Yaran da Faisal ya kora sun zo sai masifa suke. Yana shiga yaja kujera ya zauna.
“Mara mutunci sai yanzu kayi niyyar zuwa?” Inji Faisal, murmushi yayi mishi.
  Shigowar Rahmah cikin shigar kamala musamman da taki amsar skirt sai riga da wando, rigar kuwa har gwiwarta, sai dan karamin fashion hijab iya kafadarta. Kanta a sunkuye ta ce.
“Good morning Sir, good morning Ma” sannan ta koma gefe ta tsaya kanta a mugun sunkuye.
  Anan aka fara tattaunawa akan abinda ya tara su,kallon Rahmah Mr Jikamshi yayi tare da cewa.
“Yan mata meye ya faru?”
Shiru tayi ta kasa magana, sai da ya kuma tambyar ta, sanan ta fara gaya mishi abinda ya ran suka mata,. kanta a sunkuye.
“Bayan wancan mutumin ya musu fada su bar class din, shine jiya bayan an tashi daga makaranta.” Tayi shiru.
“Hmm, ina jinki”
Cikin shashekar kuka,.ta ce musu.
“Don Allah kar ku bari Ammyna taji labarin.”
“Bilal ba dan Nazo akan lokaci ba,.Yaran nan sun saka Rahmah a gaba sai ta cire kayanta sun dauke ta a wayar su, Kasan yadda naji ne? Kamar a tare Layinah a sakata ta cire kayanta tsirara. Ina mahukunta makarantar?”
Dunkule hannun shi yayi yana….
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
Mai_Dambu
3/1/22, 18:56 – Nuriyyat: 38
“Amma ai naga tunda basu dauka ba ya kamata a musu uzurin da fada gaba ba zasu kuma ba” wani irin jan iska yayi tare da cewa.
“Idan aka kama Nadiah Muhammad Alfah aka mata haka zaki ji yadda nake ji, Bilal dube ta yarinyar me ta musu? Sannan dan suna makarantar mu zasu lalata mana suna!”
“Me yasa baka karya hannun Yaron ba? Da kayi haka ba mamaki Uban ya fahimci halin da yarinyar ta shiga a Kore su, sannan a bata record din su yadda gobe zasu guji tab’a kowa. And ke kuma koma ajin ku.” Ya fada bayan ya mike yana gyara zaman Jacket din suits din shi.
 Flash back.
Kwana biyu da koran Yaran daga aji da Faisal yayi, sai suka hadu tare da shawarar dole su Rahmah abinda Faisal yayi musu koda kuwa basu mishi ba, akan ta zasu rama yadda zai ji zafin abinda suka mata. Shine bayan an tashi, daya daga cikin yan ajin su yayiwa wata Yar class din magana ta tawo mishi da Rahmah, shi kuma Faisal ya zama kamar inuwar Rahmah duk inda ta shiga yana biye da ita da kafa ko a mota yana bibiyar al’amarin ta, yana ganin lokacin da suka shiga inda ake basket ball kuma hall ce, dan haka bai yarda da haka ba, shine ya biyo ta.
Ita kuma a dan tsorace ta bi bayan yarinyar da ta ce mata zata amso abu ne, suna shiga aka rufe kofar yan mazan nan suka shiga dukarta tare sa cewa.
“Maza cire kayan ki” kuka take tana cewa.
“Don Allah kuyi hakuri karki min haka”
“Kika ce? Toh so nake nayi fucking brain É—inki out” wani irin tsoro ne ya kuma ka mata bata san lokacin da ta shiga kuka wiwi ba, daidai sun kunna wayar su kenan, tare da kokarin cire mata kayan ta ya shigo da wani sanda, tana ganin shi ta kuma fashewa da kuka. Takowa yayi tare da d’aga ta, ya dauki hularta ya saka mata.
     Tasowa suka yi tare da gyara tsayuwar zasu yi dambe da su, shi kuwa ya rike sandar da kyau yadda ya shiga dukar su da shi, yana kwallon da su, sai da yayi musu dukan kawo wuka sannan ya riko hannun Rahmah suka fita bayan ya dauki jakarta, suka nufi waje, yana isa ya samu Bus din makarantar ya tafi dan dole ya saka ta a motar shi, suka tafi gida. Ganin yadda ta tsorata yasa shi kai ta yawo, yana son lallai ta sake ranta kafin ya kaita gida. Haka yayi ta yawo da ita tun tana dari dari har ta sake suka yi having fun and sharing moment.
Kallon ta yayi tare da cewa.
“Da skirt da wando wanne kika fi so?” Juyawa tayi ta kalle shi a sace, tana wasa da kasan skirt din sai da ta dauki lokaci kamar ba zata bashi amsa ba, sai kuma ta ce mishi.
“Wando” mamaki yadda ta iya Jan aji kamar ba ita ba, ga wani kunyar da take da shi. Yana son ganin mace me masifar kunya. Kallon agogon hannun ta tayi a tsorace.
“Don Allah kayi sauri Ammyna zata min fada” karawa gtr din shi bala’in gudu yayi kamar zai tashi sama, tafiyar minti goma sha ya kawo su unguwar su. Kofar gidan ya tsaya Ammyna tana tsaye, fuskar ta kawai zaka kalla ka tabbatar tana cikin zulumi ta ina Rahmah zata dawo.
  Ganin motar da ta tsaya a gaban gidan, sai da tayi fatar Allah yasa ba ita bace. A cikin motar kuwa jikin Rahmah ne ya dauki rawa.
“Innalillahi wayyo Allah na, bude min na fita” idanun Ammyn akan motar, bude motar yayi, ta fito kamar an korota, wani irin zufa take kamar wacce ake gasata.
Kallon ta Ammyn tayi bata ce kome ba, ta shige cikin gidan. Haka ya bi bayan ta shima, domin ganin yadda Ammyn ta tsaya sai da ta dawo ya saka mishi girmama tarbiyyar Rahmah. Zama tai a sofa tana kallon wasilah da take ta faman karatun Alkur’ani, dauke kai tayi tare da kallon kofar falon a hankali daidai shigowar Rahmah, mai da Idanunta tayi kan Wasilah bata kuma ce uffan ba.
“Assalamu alaikum!” Rahmah tayi sallama,
“Yaya Ramcy ina kika tsaya ne?”
“Hmm….hmm”
“Assalamu alaikum” yayi sallama daga bakin kofar.
Kallon Rahmah tayi cike da mamaki, kafin ta amsa mishi.
“Wa’alaikumunsalam” ta fada tana jin takaicin Rahmah.
“Shigo mana” har lokacin Rahmah tana tsaye da jakarta, wani kallon da ta watsa mata yasa ta wucewa dakin su,shigowa falon yayi yana cire takalmin shi.
“Barka da gida” murmushi tayi sannan ta nuna mishi wuri ya zauna.
“Yawwa” zama yayi tare da sunkuyar da kan shi. A hankali ya ce mata.
“Kiyi hakuri.”
Cikin Dattako ta kalli yadda yake jin kunyar ta.
“Babu kome” tashi tayi tare da nufar kitchen.
“Ina wuni?” Wasilah ta gaishe shi,
“Lafiya lau, ya karatu?”
“Alhamdulillahi”
“Masha Allah, kin had’a Alkur’ani ne?” Murmushi tayi sannan tace mishi.
“Da saura Ya Rahmah ce ta kusan haÉ—awa a tartil ni saura izu Ashirin da biyar.” Mamaki ta bashi, haba shi yasa nutsuwar ta yayi yawa Alqur’ani yana yawo a jinin ta baki daya nutsuwarta da kamalarta irinta wanda ya sha madaran Alqur’ani ne.
“A ina kuka karatun?”
“Dan gaba da mune a masallacin jibwis” Murmushi yayi tare da gyada mata kai domin yasan karshe ne inda suke karatun.