NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

      Yana da burin zai haƙƙa rijiya a  cikin gidan, sai gashi Allah yayi ikon shi. Yanayin da yake kara shiga jikin Harirah kenan, idan ta tuna tayi ta kuka.

      Sai da suka yi Isha sannan suka kwanta, bata nutsu ba sai da ta ga sunyi barci baki daya. Sannan hankalinta ya kwanta itama ta saka hakarkarin ta a kasa,tana nazarin meye tayi yan uwan mijinta suka tsane ta haka? Me ta tsare musu haka da suke ganin bakin ta,  ajiyar zuciya ta sauke tare da kunna torch din hannunta,taga yadda Yaran ta suka dunkule su uku gwanin ban tausayi, ga Rabi’atu a jikin ta,.ta makale ta kamar zata gudu ta barta. Murmushi tayi tana shafa kan yarinyar wanda yake dauke da lumsassun gashin gaban goshinta, sun yi wani irin luff luff, sai wani irin sheki yake. Gwanin burgewa domin idan da zaka nutsu ka kalleta zaka dauka irin hafcase ce, mutanen Portugal su ba farare ba, su ba bakakke ba. Yanayin fatar ta yana yin kwayar idanun ta, domin idan da zaka nutsu zaka dauka diyar Beyonce ce, zunzurutun yanayin fatar ta da yake kamanceccniya da na wancan shaharariyar mawakiyar kasar Amurika.

     Haka suka kwanta fuskarta a dame, har barci ya dauke ta, mutumin bai kuma shigo musu ba,.har asuba ta tashi yaran suka yi alola da sallah, sannan suka zauna har rana ya fara fitowa, kafin tasa suka kuma kwanciya. Abincin su na jiya shi suka kuma dumama  shi suka ci.

    Yanayin rayuwa ya cigaba da tafiyar da su, haka dadi babu dad’i har, Ammar yazo ya kai su makaranta, aka gama musu kome, Jamilah dama a Ss2 zata shiga aka bata ajin, dake makarantar gwamnati ne, sai dai dake na kudi suka fara a yan yellema zata taimaka musu anan.

      An gama kome ranar Monday, talata suka shirya baki daya, suka tafi abin gwanin burgewa, hankalin Ammin su ya kwanta a karshe dai Yaranta sun koma makaranta, sai dai tsugunne bata kare ba, domin kuwa dole zasu yi karatu zasu ci abincin ai ba zasu rayu haka ba,  ba zai yiwu su zauna haka babu abincin da zasu ci ba, dan haka ta fara kokarin niman sana’a kafin tayi arab’in. Dan haka ta shiga nazarin abinda zata yi domin kare mutuncin Yaranta.

     A hankali lokacin yayi ta tafiya, har suka doshi kwana arba’in, gefe guda taga sauyi daga Yaranta, domin rashin komawa makarantar shi ya tab’a rayuwar su,.har suka koma wani irin a cikin gidan su.

*
Ranar talata aka yi addu’ar arba’in Alhaji Ishaq,.tare da fitar da wasu abinda yan uwan shi zasu iya fitarwa domin,  kananun magana da ake a gari yasa su jin kunyar abinda suka aikata, dan haka inda yake noman rani, aka fitar da abubuwan da Baba Haliru ya rike, dan dole aka fitar da kayan gonar aka sayar, shi kuma Badamasi ya bada dabobbin da yake kiwon su,.ya bada aka raba gadon.

      Babu yadda suka iya da Harirah, amma tabbas da suna da hali da sai sun ga bayanta, amma a ran su. Ba karamin kullatarta suka yi ba, har gwara Badamasi bai tsananta ba, shi dai yayi alÆ™awarin ba zai kuma shiga cikin al’amarin Yaran Ishaq ba, dan haka kar su kuskura su ce sun san shi.

    Gefe guda kuwa Gwaggo Lami da Nairah kamar su saka Harirah a wuta, babu yadda suka iya da ita ne kawai, amma tanadin da suka mata Allah kadai ya sani. Washi gari da safe Baba Haliru ya shigo cikin gidan yana dariya ya ce mata.
“Harirah ba kin bi gari akan mun rike kayan Ishaq ba, toh wallahi muna nan dake kudin sai ya kare kin yi kuka da idanun ki, sakarya.” Daga haka ya fita daga cikin gidan, bata damu ba kawai dai ta rike kudin a matsayin abin da zata rufawa iyalin ta asiri..bata kuma jin zata nima a wurin wani domin babu abinda zasu bata, wanda Allah bai bata ba, dan haka ta adana kudin.

     Alhamdulillahi samun wannan kudin da kayan abincin ya sanya ta samun dan wadata, dan haka suka fara kosai da koko, a har cikin gidan ake zuwa saya, kuma cikin ikon Allah albarka ya fada cikin kayan sayarwan su.

         Dake sun raba kome Rabi’atu ce ma bata kome sai daka yaji, kafin kace me gidan ya cika makil da Yara, tare da manyan maza da mata, da suke jira a basu, abin sai godiyar Ubangiji kawai domin babu nakasashe sai kasashe, babu maraya sai rago, domin bata jin ko mace me miji zata nuna mata kula da iyali. Tayi matukar kokarin mai da hankalin ta sosai akan iyalin ta, a matsayin ta na uwar Yara mata hudu dole ta saka ido akan niman abinda zai rufa masu asiri,.har abada ba zata tab’a daurawa Yaranta tallah ba, ita zata yi kome idan har zasu iya siyarwa kafin su tafi makarantar boko.

  Alhamdulillahi Allah ya taimaka babu wani kome da ya dakatar da wannan kudirin domin Yaran sun kasance masu zuciya da son cigaban mahaifiyar su,

Yau Juma’a ya kama a gurguje suka gama kome, sannan suka mata sallama suka fitaa. Rahmah da Jamilah,.suna tafe a gaba yayinda Rabi’atul da Wasilah suke baya, sai hira suke akan karatun su, Jamilah da Rahmah.

   Har suka iso filin makarantar, anan suka samu ana Assambly, tsayawa suka yi a can gefe sabida ana take kasa. Ana gamawa suka shiga cikin dalibai dukkan su.

       Bayan an gama malamin da yake Islamic ya fito yayi musu addu’a, sannan shugaban makarantar shima yayi kafin ya gabatar da sabon malami amma dan bautar kasa, inda shima ya fito yayi bayani da turanci, shi bahaushe ne, domin iyayen shi yan arewa ne, yayi bayani sosai inda yace zai na darasin Biology a aji shida na biyar,  kafin aka sallame su.

 
Tunda suka shiga aji Yan Ss2 basu da hira sai na Malam Aaman D Muhammad. Jamilah tana jin su bai burgeta ba,.ita bata ga abin damuwa ba a wurin shi ba..
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/1/22, 18:51 – Nuriyyat: WATA ALKARYAR….
THE BEGINNING OF DESTINY
NA
Mai_Dambu

EWF

Kowani bakin wuta<4>

Sam bai burgeta kuma bawai dan yana bako ba a’a ita asali haka take ba kome yake burgeta ba, dan haka abokiyar zamanta ce ta tab’a ta.

“Jamilah Ishaq malamin nan bai burge ki ba?” Murmushi tayi tana kallon yarinyar me suna Saratu ta ce mata.
“Bai burge ni ba!”

Ta fada cikin nutsuwa tare da maida hankalin ta, akan malamin English ya shigo.

    Bayan ya gama darasi ya basu assignment, sannan ya fita kasancewar karatun ne a ranta, duk tafi sauran yan ajin mai da hankali akan karatu, haka yasa koda suka fita break bata fita ba, har Rahmah da Wasilah suka shigo ajin wurin ta, sai daga baya Rabi’atu ta biyo su, zama tayi a saman dest tana murmushin jin dadi ta ce musu.
“Destined  can choose three step for you in your life, whatever you like whatever you need, whatever you don’t need it, anymore you most agree with it!” Ta fada tana dariya, sake baki Rahmah tayi tare da kallon ta,.dukkan su kallon ta suke dan itace karama kuma mara yawan magana.
“Da alamu zamu samo Professor na falsafa ce! And muna jiran three step din?” Inji Jamilah,

Mikewa tayi tare da kallon su, kafin tace.
“Love,Caring, hatred” tana gama fadar haka ana buga ka rarawan shiga aji, da sauri Jamilah ta rike hannunta, ta sauka akan kujeran, tana murmushi.
“Muje maza na kai ki aji, kuma maza muje” wannan dabi’ar su ce, idan yau suka zo ajinsu Jamilah gobe na Rahmah zasu jibi kuma na wasilah kafin na Auta, Ammin su ta koya musu yadda zasu so juna su kuma kaunaci junan su, yadda idan babu É—aya a cikin su ba zasu yi farin ciki ba. Wannan dalilin yasa sun yanzun kan su a hade yaÆ™e. Sai da suka raka Rabi’atu sannan suka raka Wasilah kafin Jamilah ta rako Rahmah ajin su, dab malami zai shiga tayi maza ta tura ta.
“Yaya kema kiyi sauri kar malamin ku ya shiga baki ajin”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button