NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

“Duk yadda kace Alhaji daya ne, sai dai bata yi kankanta da auren ba?” Ya fada tare da kallon dakin su, Murmushi yayi tare da kallon Mammyn ya ce mata.
“Hajiya Mariyah anya zata yi kankanta?” Ya tambayi Mammyn,
“Mu bata lokaci tayi nazari idan ta samu mafita sai ayi magana dasu ba.” Ta fada tana kallon Ammyn da tayi shiru, haka suka mata sallama, suka fita. A gajiye wasilah ta kalli Alkasim da yake narke mata kamar ruwan gishiri. Wani tsuke fuska tayi tana fadin.
“Malam bude min kofa na fita dama ka dauko ni ne domin ka saka ni a gaba kana min shagwab’a?”
“Allah ya baki hakuri, don Allah ayi min abu bude baki na fita na gaji da zaman motarka” ta fada tana hararan gefe.
  Bude mata yayi ta fita tana mita, domin Allah ya daura mata kananun magana, tunda ta fita ta bita da ido tare da kifa kan shi, haka zai cigaba da bibiyar ta,yarinyar sai kara bashi wahala take.

  ..
Da dare, kuwa suna cin abinci Ammyn ta jefawa Rahmah tambayar da ta kusan kwarewa.
“Kina son Faisal ne?” Da sauri ta d’ago kai tana tari.

“Tambayar ki nake, ko baki ji bane?” Ta kuma maimaita mata tambayar Idanunta yana cika da kwalla.
“Ammyn”
“Eh ko A’a!” Ta kuma tambyar ta, baki daya sai ta rude abin tausayi, ta shiga rike hannun yan uwanta.
“Ammyn ai a hankali zaki bita, a fusace haka ba zai” Murmushi tayi irin na takaicin nan domin Allah ta gani bata son auren amma babu yadda ta iya.
“Ta bani amsar tambayar domin na san abinda zan gayawa Mahaifiyar shi ba zan iya zama mutuniyar zan akan ku ba, ko kuma ni na yanke abinda ya dace”

       Mikewa tayi tare da barin wurin, tana share kwalla,karamin murmushi Ammyn tayi a ranta, domin ba zata hana ta abinda take so ba, amma kuma ba zata iya barin ta ta fada damuwa ba, dan haka zata dakatar da wannan yanayin su,tayi karatu kawai zai fi mata.

    *
Baki daya suka Zubawa Ummin idanu, ganin taki magana sai duk suka shiga damuwa.
“Ummin mu baki ce kome ba?” Ya tambaye ta cikin sanyin jiki,
“Mahaifiyarta tana cikin kewar Y’arta da ta ba’ata,tsoron kar a cutar da sauran yasa taki maganar auren,wai tukun yaushe kuka fara soyayya da yarinyar ne,baki daya yau ta bani tausayi domin da na tambaye ta, tana sonka a cikin Idanunta na ga amsar tambayar amma a bakinta taki magana baki daya, Uwar su ta gina musu rayuwa da kunya da kawaici, amma suyi magana ba zasu yi ba sai hakuri.

   Gaskiya zan so yarinyar a matsayin Matarka, ba a suruka ba, sannan wannan shegen rawan kan naka, dole ka ajiye shi a gefe, kabi a hankali har ta baka auren ta.” Kallon shi Mr Jikamshi yayi yana kallon kan shi kafin ya fara yar dariyar mugunta.

   “Dan iska mugu wato an ce rawan kai shine bari ka kalli kaina kaga ta inda yake rawa.” Ya fada kamar zai daki Mr Jikamshi, murmushi yayi sannan yace Mishi.
“Matsalar ka idan har ka yi tunanin matar nan bata son a yaudari yaranta ne, saboda matsalar da ta samu dayar su, kawai abinda za ayi ka janye daga jikin yarinyar zata fi sauki, sannan suna ga maganar gaskiya ka nime aure karkace sai ita ce dole, domin suka fama da shock ba abinda ya same su, a lokacin da suke kokarin ganin sun warke daga raunin da suka ji zaka zo musu da batun aure kayi nazari mana? Ka fahimci cewa uwar ta hakura da farin cikin ta ne domin gina na Yaranta, kai kuma lokaci guda basu gama warkewa ba zaka zo musu da batun auren Yarta ta biyu, sannan idan na fahimci dalilin hana ka auren Yarinyar abu biyu ne, na farko tana son yayar ta samu nata farin cikin, na biyu tana gudu kar a mata gori akan abinda ua faru da Yaranta na uku tana dakon karamar Y’arta, ka saka wannan a skile kayi nazarin shi ni kuma zan tabbatar maka da haka”

  Sake baki suka yi suna kallon shi,kafin Ummin ta ce.
“Taya ka fahimci haka, bayan baka zauna da su ba?”  Murmushi yayi sannan ya zuba ruwa a kofi, yana kallon su. Sai da ya sha kafin ya kalle su a karo na babu Adadi ya ce musu.
“Abu ne da yake a bayyane, ni kaina nayi fama da irin matsalar su wanda har yanzun nake fama da shi, taya ba zan fahimci halin da suke ciki ba? Karku manta kafin na fita na dawo na samu an kashe mata ta.” Yar karamar Murmushi yayi tare da mikewa, ya kalle su, sannan ya ce musu.
“Har yau a razane nake da niman aure domin ban san me za ayiwa matar da zan aura nan gaba ba, ku basu dama su sha iska ko nan da shekara biyu ne, su dawo nutsuwar su ne”

           Jinjina kai suka yi tare da gamsuwa da bayanin su.

   *
A bangaren Ammyn itama babu wani bayani kawai tace a bata lokaci, kuma kuma suma sun bata samar ta sarara, tunda abin ba na gaggawa bane, za a iya hakuri da hakan.

   A cikin wannan yanayin ne sakamakon Jamilah ya fito, sai dai bata samu abinda take bukata ba, sai aka bata Bussiness administration
Dake Aaman baya kasar Alhaji Muhammad ya gaya mishi abinda ya faru ya mata fatan alkhairi, sannan ya roki baban su ya tura Alkasim da wayar yana son magana da Ammyn.

  Haka ce ta faru bayan an kai mata wayar suka gaisa,.har ya roke ta don Allah ta sayi Wayarta itama haka zai taimaka mishi wurin niman ta, ita tasan ba wai ita zai nima ba, yayi haka ne sabida Jamilah, bata kin wannan hadin gaskiya domin Aaman yayi musu kome a rayuwa, babban burinta bai wuce ayi haka ba, idan har iyayen shi zasu amince da ita Jamilah zata yi farin ciki na har abada .

*
Hajiya Turai.

Shiru yaran suka yi suna kallon ta, ajiyar zuciya ta sauke me nauyi kafin tace musu.
“Ai kunji me nace, dan haka ke  Suhaima zaki shirya shekara me zuwa ina ga zamu fara aiki da Bilal, sannan kai kuma kaji me na gaya maka. Dan haka dukkan mu zamu nime abu daya ne, dan haka karku manta ina nan domin ku”

    “Mommy baki ce min kome akan Faisal ba?” Inji Zuhairah Kabir Wazir,
Murmushi tayi mata, sannan tace mata.
“Bani son dan gidan Atikan nan amma saboda ke zamu had’e da ita”
“Nagode sosai, next week Birthday din Mimih Alfa kuma nasan zasu zo wurin don Allah ko a wurin ne ayi kome.”

     Shafa kanta tayi bayan ta dauki jakarta, sannan ta ce mata.
“Baki yarda da ni bane? Ƙarki damu zan baki mamaki” ta fada tana Murmushi.
“Amma Mommy ina da wcce nake so, kuma idan nayi haka kamar na cutar da ita ne, please bana son ta ga kamar na cutar da ita…”

“Ka yarda nace, idan har ka amince zaka samu wacce kake so amma daga farko ka tafi inda na turaka idan ka kuskura na rasa wannan damar toh ba makawa zaka yi danasanin abinda ka aikataâ€?
Tana gama fadar haka ta haura sama, abinta kallon Suhaima yayi tare da cewa.
“Bilal bai da sauki dan haka kiyi taka tsantsan akan shi, domin mutum ne.  Me matukar hatsari”

“Taya zan yarda da haka bayan, nima ina da nawa hatsarin kawai ka ceto soyayyar ka da Bestie karka sake ka rasata.” Ta fada tana mikewa daga kujeran, ta wuce É—akinta, tana shiga dakin ta rufe kofar sannan ta wuce ban daki. Wayar hannunta ta danna sannan ta kira wani layi, sun jima suna magana, sai dai baki daya maganar taki fada mishi abinda sukayi da Maman ta, karshe ta kashe wayar baki daya ta fito ban dakin ta zauna. Tana murmushi kadan kadan, tare da nazarin yadda zata kama kome a hannunta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button