NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

*
Rome.

Bayan kwana biyu.
ÆŠaukata, tayi muka tafi Red line life orphanage, aka bani unifoam da jakar makarantar, sannan aka kai ni ajin. Sai da aka gama koya mana karatu kafin aka fita break, a wurin break din ne, na amso abinci na zauna, dan wasu Yara suka fara fada, duk da sun fimu girma, amma a kan idanun mu wanda yafi karfin Daya yake dukar shi har sai da ya daina numfashi, sannan aka zo aka dauke shi, shi wanda yayi dukar ya koma gefe yana,.irin bai so haka ba, babu yadda ya iya ne.

“Haka tsarin gidan yake, idan kayi laifi toh wanda yafi karfin ka, shi zai sake ka har ka suma, idan kuma kana da karfi ka kwaci kanka. Amma sai idan Mss Jessica Simpson bata gidan nan ake wannan ta ce mu kasance in unity and loyalty. Babu damar mu farauci juna kamar dabobbi, ya kamata mu girmama juna da kyautattawa domin gidan marayun da muke yana da kafafen tarihi,na shekaru aru-aru.” Inji wata yarinya bayan ta gama ta mika min hannu.

“Suna na Priyanna daga India” ta fada, Murmushi nayi sannan nace mata.
“Rebecca daga Nigeria”

“Zamu zama kawaye”
“A’a ba zaku zama kawaye ba, domin babu wani abinda zai kare ku sai kashe juna”

“Meye!!?” Muka tambaye ta,
“Kun ga abinda ya faru da Rowd da Herry abokai ne, bai hana a saka shi ya kashe shi ba, kuna son karshen abotarku ta kare da kisan juna”
“A’a” muka fada da sauri,
“Toh Babu abota a gidan nan kowa ya kama gaban shi.” Daga haka muka yi shiru,muna gama cin abinci aka wuce damu, wani daki babu kome a cikin shi sai koyar fada, dan haka kowa faÉ—a yake da dan robon da aka sa mishi.

Haka muka wuni tun da muka gama aji muka sunkuya a wurin.  Sai dare muka koma gida, na gaji sosai ina shiga cikin dakin ko kayan ban cire ba, sai barci ita ta cire min kayan ta sauya min na jikina, can cikin dare ta shigo ta tashe ni. Wani daki ta kai ni, anan ta fitar da wasu irin roba wanda suna motsi ta ce min.
“Daga yau idan kika taso, muna da special class shi zamu fara bayan kin gama wancan abin…

300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/1/22, 18:57 – Nuriyyat: 42

Kallon robon nayi da yake tafiya, sannan na kalle ta.
“Yes Mah”  tun daga lokacin ban kuma barci na awa takwas ba, domin kuwa tun ina faduwa ina kuka, idan na fadi tayi ta zane ni da bulala, sai da ta kai hatta tafin kafana, da wani irin bulala take dukana, haka yasa ni kare zage dantse wurin koyar abinda take koya min, har ta kai idan ana son a rage wasu mu a cikin gidan Marayun kawai sai a saka manyan mu, su shiga dukar mu har sai sun tabbatar kun mutu, shi kuma zama irin na gidan bba karfi bane a’a zuciya ce da sanin yadda ake fada, sau daya aka dake ni har na suma, Mss Jessica Simpson ita ta É—auke ni zuwa wurin Mr Andrew Cuomo ta ce mishi.

“Idan kana son zaman lafiya, a dakatar da wannan zalincin idan kuma ka cigaba na rantse zan yi report din abinda kake yi, a haka za a cire maka zakwakuran da kake so?  Bayan kana kashe su kamar dabobbi, ya isa haka.” Ta fada da Æ™arfi sannan ta fita daga cikin office din shi tana rike da ni.

       Wato asalin gidan marayun ya ginu ne akan wasu kungiyoyin ne, da suke kasance miyagun Mutane a cikin al’umma, idan har zaka zauna a cikin gidan ba zaka iya tausayin kowa ba, sanan a cikin gidan ma ana horarr da karuwanci lesbians, maza yan homo, barayi masu fashin bakin, barayi masu yankar aljuhu, hackers, da asalin ma kasa masu kashe mutum da kuma yan leken asiri . wannan shine asalin gidan sannan shi kan shi Shugaban gidan Mr Andrew Cuomo cikakken dan Homo ne, dan haka gidan da Yaran gidan baki daya kowa fitinannen kan shi ne. Sannan akan bada horo ne na tsawon shekaru huÉ—u zuwa biyar, daga lokacin za’a iya turaku aikin da ka kware a kai.

           Sannan manyan mutane suke daukar nauyin kowani dalibi a cikin gidan, sannan a maganar gaskiya babu tabbas akwai wadannan mutanen, wani abun da zai kuma baka mamaki shine ana cire yaran da basu iya kome akan su, ana kai su Lab, idan za ayi wani gwaji ko wani abu kamar had’a magani ko kuma wani abu da ya shafi rayuwar dan Adam, da wadannan Yaran ake gwadawa kasancewar su ba zasu iya daukar kome ba akan su.

Mss Jessica Simpson gwana ce a horar da fadar sunkuru, babu ta inda zaka Duba ka samu bata yi ba, sannan  cikin team na yan lesbian, domin suna zuwa gidan.

*

Lagos.

Hajiya Turai.

“Nadrah ban gane kina da wanda kike so ba?” Ta tambaye ta bayan tana shiryawa domin zuwa Birthday din Mimih Alfa.
“Mommy ki janye maganar Bilal wallahi bana son shi, kawai ki bar ni na auri wanda nake so, don Allah” ta fada kamar zata yi kuka.
“Ki shirya mu tafi, domin nasan Bilal ma zai zo wurin.”

   Girgiza kai tayi tare da cewa.
“A’a ba zan tafi ba sai…” Kifa mata mari tayi.
“Baki isa ki min bakin ciki ba, bayan kasadar da na gama dauka kice a’a, sai na kashe ki babu abinda zai faru”

    Ta fadi haka da mugun karfi, ita kanta Nadrah sai da ta razana, cikin shashekar kuka ta ce mata.
“Toh”

Sannan suka shirya sai gidan Hajiya Humaidah, wurin karfe takwas na dare, harabar gidan ya cika da manyan mutane, dan haka aka shiga hidima har ita kanta Mimih ta fito, ita da Zuhairah, Nadrah Ruma kuma suka kebe da Suhaima Kabir Wazir.

     “Ina cikin matsala Bestie” inji Nadrah,
“Akan Ya Irfan ne? Ko akan haÉ—a ki aure da za ayi da jikamshi?” Rike hannun Suhaima tayi tare da cewa.
“Kai na ya kulle.”
“Gwara ki sake shi ya bude domin a wurin nan abubuwa dayawa zasu faru.”

       Kallon rashin fahimta Nadrah tayiwa Suhaima.
“Ban gane ba?”
“Zaki gane bari kome ya kankama” shiru tayi, tana kallon Waje da mutane suke, can kamar minti goma, aka sanar Bilal Ahmad Jikamshi zai shigo shi da Hajiya Atikah Abbas Jikamshi da Barista Faisal Abdul Hadi Shema. Wurin ne ya dauki wani masifaffen shiru ana gulma kasa kasa, dama irin wannan al’amarin yana samun kanannun magana da gulmace-gulmace, dan haka bayan minti biyar kuwa sai gasu sun shigo cikin gidan.

Daukar su hoto aka fara, fuskar shi kamar kullum a kamile, nutsuwar shi da cikar kamala ya kuma kara fitowa, sai gashi duk wadanda suka shirya za a kawo mishi maganar banza, kwarjinin shi yasa sun koma gefe cike da jin babu dad’i. Ganin shi yasa Nadrah Ruma tayi maza ta nufi wurin shi. Haka ba karamin bakanta ran Irfan yai ba. Dan hakan ya kasa boye fushin sa, har inda Mr Jikamshi yake tsaye, ya zo ya tsaya kafin ya ce mishi.
“Sarkin hadd’ama mata nawa zaka aura su mutu? Itama wannan zaka bada ita ne domin karin arzikin ka”

Murmushi yayi tare da cewa.
“Eh toh, tunda jinin matana ne da sauki ba jinin mahaifina bane” ya fada yana kallon Irfan cikin jin haushi ya ci kwallar Mr Jikamshi, abinda ya janyo hankalin dukkanin mutanen Wurin.
“Wallahi sai na ruguza ka, sai na ruguza kome na ka, sai na mai da kai mara amfani sai na saka an manta da sunan ka.”

“Tunda ka iya kashe mahaifin ka Meye ba zaka yi ba, karka damu ina jiran ka” wani irin ihu Irfan ya saka bayan Faisal ya raba su, dakyar aka fitar da Irfan Kabir Wazir daga cikin gidan, cikin wani irin takaici Hajiya Turai ta kalli Mr Jikamshi.
“A matsayin na wacce ta auri mahaifinka ashe zaka iya cin mutuncin Yarona Bilal ai ko dan albarkacin Ahmad Jikamshi zaka d’aga mishi kafa.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button