WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
Murmushi yayi tare da cewa.
“Hajiya Shuwa ina ganin girmanki” daga hakan ya wuce wurin Mimih da take kallon za a wargaza mata bikin karin haihuwar ta, takowa yayi tare da mika hannu, aka saka mishi wani kwali dan haka ya mika mata, murmushi tayi sannan ta ce mishi.
“Kumayo”
Yar karamar Murmushi yayi sannan yaja kumatunta.
Sannan ya bar wurin, karshen dai Irfan ya lalata shirin Hajiya Shuwa, duk da yadda taso a wannan wurin zata bada komarta domin kama Bilal sai dai Allah ya wargaza mata shirinta.
 Bayan an ci an sha, Hajiya Humaidah ta kalli Yan uwanta sannan ta ce.
“Ni da mahaifin Nadia da ita kanta muna muku Barka da zuwa bakin mu, sannan muna farin cikin zuwan ku, sannan wani hanzari ba gudu ba, ni da Alhaji Alfa Muhammad mun bawa Bilal Ahmad Jikamshi auren Nadiah Muhammad Alfa. Nan da duk lokacin da ya shirya yayi magana, itama tana aji uku a jami’a, sannan zata hada da master duk lokacin da ya shirya za ayi kome cikin amincin Ubangiji”
“Kutmar Uba!” Inji Hajiya Turai tana wani irin tsuma, kallon Juna Nadrah da Suhaima suka yi.
“Kin ji abinda ya faru?” Nadrah ta tambayi Suhaima,
“Eh naji mana, ko ke baki ji ba? Meye naki a cikin haÉ—in? Naga Kema kina da Irfan wannan ni ya kamata na shiga damuwa domin mahaifiyata tana da burin na auri Bilal Ahmad Jikamshi”
“Taya? Bayanin nima burin mahaifiyata ce na auri Bilal, Don Allah mu bar maganar nan.” Ta fada tana dafa kafadar Suhaima, ture hannun ta tayi tana kallon cikin idanunta, sannan ta ce mata.
“Me zaki bawa Bilal? Ko kina sun na gayawa duniya cewa You Are lust, karyar da ta bawa namiji kanta.” Tass Nadrah ta kifa mata mari.
“Idan har ni karuwa ce da nake bawa Dan uwan ki, kaina yana ci ke kuma Meye sunanki? Wacce take bin Abokin mahaifinta, kuma mutumin mahaifinta. A lokacin da kika san sirrina a lokacin na Miki wani irin sanin ban mamaki ko an gaya Miki cewa ban san duk abinda kike yi ba? Ni abin kunyar da nayi ban zubda cikin shege ba, ke kuma na samun haka a wurin da aka ganki zubda cikin. Bani da burin na gaya miki haka but na fahimci kudin zuma ne sai an shaku da wuta”
   Daukar jakarta tayi tana jin wani irin ɓacin rai, daga yau zata tsaya a bayan mahaifiyar ta, ta tayata faɗa. Wurin taron ta nufa tare da kallon Bilal.
“Bilal ashe ka zama gwanjo kowa so yake ya haÉ—a harka da kai, so na tayaka murna. Amma ka kula da kanka!”
Murmushi yayi sannan ya ce mata.
“Kina kishi ne?” Da sauri ta kalle shi, kamar zata yi kuka ta ce mishi.
“Akan me zan yi kishi? Ai sai kana son abu kake kishin sa, dan haka ka bar tunanin haka”
“Ni kuwa bana jin haka ne, tunda gashi zaki yi kuka”
“But” kai bakin shi yayi kunnenta yayi mata magana, kawai sai gashi ta fashe da dariya, kamar ba ita ba ce ta ke kuka, Hajiya Turai da ta ga yadda yake kula yarta take ta nime É“acin ran da take ciki ta rasa, tare da alkawarin sai ta ruguza Yar uwar ta, koda kuwa haka zai tab’a zumuncin su na har abada.
 Haka aka ci aka sha, ita kan Mimih karshe jikin shi ta dawo da taga Nadrah tana kusa shi, haka akayi ta daukar su hoto, sosai musamman yan jarida.har aka watse.
Washi gari
Sai gashi lokaci guda akan sake hotunan su, su uku tare da ajiye ayar tambya, shin leken faru ne a cikin family Jikamshi. An bawa JIKAMSHI NADIAH MUHAMMAD ALFA AMMA BA WURIN AN GA HANKALIN SHI YA KARKATA GA NADRAH ALI RUMA SHIN ME HAKA YAKR NUFI?
A take aka shiga muhawara me zafin gaske wanda shi kan shi Mr Jikamshi sai da yaji kamar kan shi zai fashe dan haka yana zaune a building kamfanin shi, aka kawo dan jaridar da yayi rubutun, tunda ya shigo ya zauna yana kallon shi. Ganin har zuwa lokacin hankalin shi yana kan Jaridar, ajiyewa yayi tare da nad’e hannu a kirji ya zuba mishi ido. Daidai ana Zubawa dan jaridar ruwan tea.
“Karka saka mishi sugar sosai, sabida yana da ciwon suga” ya fada yana kallon dan jaridan wanda jikin shi yake rawa.
“Me yasa sai ni?” Ya kuma tambyar shi.
“Me yasa kake son duk lokacin da aka ayi abu ka fitar da suna na?” Bawan Allah nan jikin shi kaman wanda aka saka mishi lantar ki.
“Ok tunda ba zaka yi magana ba, zaka iya tafiya” ya fada da fuskar shi ma’abociyar nutsuwa da kamala, fita dan jaridar yayi, sannan Faisal ya shigo yana kallon shi.
“Meye kake ganin zai iya faruwa?”
Shiru yayi yana kallon Jaridar gaban shi.
“Ka shirya min zama da ita, ka bawa Khalil kome da ya dace, zan gana da ita.”
  **
Hajiya Humaidah
“Mamie fanfon dakina baya yi fa? Ayi wani abu” tsaki yayi tana mita, tare da nufar dakin mahaifiyar ta.
“Toh bari na yi magana a Turo masu gyaran” ta fada tana kallon ta. Wayarta ta dauka ta kira akan a zo a gyara masu fanfon.
    Bayan minti talatin sai ga masu gyaran sun shigo, suka fara aikin har suka gama, sannan suka fita ita kuma ta shiga cikin dakin.
Bayan wata guda da yin haka makarantar Jikamshi Model school, daga ma’aikatar ilimi da Shari’a, suka turo da wasu manyan mutane aka fara bincike akan makarantar domin an samu korafin ana sayar da kwayoyin, ita kanta Mimih a ranar ta fito gida zata tafi makarantar, aka tare ta ana binciken motarta anan aka samu hodar iblis da wasu kwayoyi, abin tausayi kuka bata san da su ba, a take aka nufi gidan Hajiya Humaidah, aka samu Manyan laidojin kwayoyi a dakin Mimih wannan abun ba karamin al’amari bane domin an rufe Hajiya Humaidah….
Abin tausayi da tambaya shin taya haka ya faru? Shi kan shi Mr Jikamshi sai da ya girgiza domin ya fahimci ba zai yiwu a kashe Mimih bane amma idan aka B’ATA sunan mahaifiyar ta, shi kan shi zai iya zama abin tuhuma a idanun duniya da yan kasuwa dan haka, suka yi shiru tare da kokarin fitar da Hajiya Humaidah daga cikin tarkon da aka danna mata mata, kuma Alhamdulillahi domin sun shiga sun fita har dai aka samu matsaya. Amma an kai maganar kotu nan da wata biyu.
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
Mai_Dambu
3/1/22, 18:57 – Nuriyyat: 43
Bayan wata biyu.
An shiga kotun idan suka yi nasarar bude musu makarantar su, sai dai kuma an dakatar da shigar Hajiya Humaidah harkan makarantar baki daya ita kanta Mimih jami’ar da take sun koreta, dan haka Bilal da Faisal suka mai data korea, domin sanin ana bibiyarta kuma za a iya kashe ta yasa suka dauke ta, ita kanta Hajiya Humaidah tayi danasanin biyewa yan uwanta domin tasan kome daga wurin su ne.
**
Rahmah sun gama makaranta, yayin da Jamilah ta cigaba da karatunta a Jami’ar lagos, itama Rahmah tana jiran result ne, domin ta fara karatunta na gaba da secondary. Wasailah ce shekara me zuwa zata gama, idan ka cire kewar Rabi’ah da take nukurkusa Ammyn dan bata rufe sati bata kwanta jinya ba, ta saka damuwa sosai a ranta.
Sannan bata cika shiga kome ba, babban burin ta a duniya Allah ya sadasu da Rab’iah domin har yau bata ji a ranta zata iya amincewa yarta ta mutu ba, shi yasa tun wuri ta hana Yaran kuka, tsakanin su da Hajiya Atikah zumuncin ake sosai kamar an zama yan uwa. Dan ma ita Ammyn bata cika zuwa gidan Hajiya Atikah baz amma babu laifi ana zumunci sosai. Sanan kuma gefe guda an gama maganar Rahmah da Faisal, domin Ammyn ta fahimci Hajiya Atikah mutuniyar kirki ce, bata da giraman kai da d’agawa.