NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

 Wannan ya kuma ya saka Ammyn ta sake jiki da ita, kuma tana jin daÉ—in mu’amala da ita, itama Hajiya Atikah tayi matukar kokarin wurin nunawa mutane Ita mutum ce me mutunci kuma dukiya da nasabarsu bai tab’a sakawa jin kamar tafi Ammyn ba, kuma dama can tun fil azal bata da kawa sama da Kim Eau, yanzun kuma a sanadin Faisal da Rahmah ta kuma hadu da Amin dan haka ta rike Ammyn da Hannu bibiyu.

  .
Jikamshi House.

“Azzalumai macuta ma’ha’inta ina cikin ku daya da abinda zaku saka min kenan, fiye da wata biyu ina fama da tashin hankali, akan laifin da ba nawa ba, kun zata Allah zai bar ku ne. Allah sai ya saka mana ni da mijina da Y’ata kuma wallahi na rantse da Allah sai na tona muku asiri dukkan ku. Dani kuke zancen” inji Hajiya Humaidah da take kuka, kafin ta mike tana faÉ—in .

“Annamimai, kuma ku saka idanu ku ga ikon Allah, fasikai marasa tsoron Allah”
Cikin fushi Alhaji Abubakar ya ce mata.
“Amma baki da lafiya? Ko kwayar kika watsa ne?” Ya tambaye ta yana dariya.
“A’a maciyi Amana ba kwaya na hadiya ba, dan abu kazr-kazar Ubanka mara mutunci da hankali” mikewa yayi tare da nufarta,ai kuwa tana tsaye kamar filla taki motsi.

“Abubakar kyale ta, abokin mutuwa take nima ta gayawa duniya cewa an kashe ta” inji Hajiya Turai,

   Abin tausayi baki daya suka manna mata Hauka, haka ta dauki jakarta tana share kwalla,ta fito daga cikin dakin. A bakin kofar fita suka hadu da Bilal da Faisal, suna tsaye.
“Kiyi hakuri” inji Faisal bayan ya mika mata hanky.
“Wai ace abinda aka min da saka hannun Yan uwana”

Girgiza mata kai suka yi, sannan suna fita, ta juya tana kallon window hall É—in. Wanda wani yake tsaya, zaka iya ganin alamar ana tsaye, amma ba zaka iya fahimtar waje a wurin ba, dan haka ta shiga motar ta, suma su Faisal suka shiga nasu.

         Suna fita daga Jikamshi House, suka tsayar da motar, tare da cewa driver ya tafi kawai, bayan Bilal ya amshi wayar shi, yayi wasu yan danne-danne sannan ya ce mishi.”ba sai ka tafi gida ba, ka kai motar Apartment dina gamu nan zuwa da ita”
Kallon su tayi tare da zare idanu.
“Me yasa kuka hana ni shiga?”
“Muje mana” wani ikon Allah bin bayan motar suka yi, wanda yayi tafiyar da bai wuce minti goma kacal ba, suka samu an buge shi. Tare da watsa mishi dutsen garahul. ? Kune kuka kashe shi?” Ta fada da Æ™arfi Idanunta yana tsiyayyar da kwalla, kallon shi tayi tana kuma kuka.
“Bilal you are monster!”
“Fay don Allah shiga da ita kai na ciwo” shigar da ita motar suka yi, tare da barin wurin, kuka take tana karawa. Juyawa yayi tare da mika mata tap din shi.
Ya umurce ta da saka play. Hannun ta na rawa ta ga mutumin da take kukan an kashe shi.
“A ranar da fanfon Mimih be kawo ruwa ba, waye ya shiga cikin gidan?” Kallon Faisal yayi tare da sunkuyar da kai.
“Ni ne na shiga a matsayin me gyaran bayan an turo min da kayan da aka samu a wordrob din Mimih.” Ya fada a matukar firgice.
“Har tsawon wani lokaci ka dauka kana zaluntar ta bayan tana iya kokarinta akan ka?”
“Wallahi ban sani ba, nima bani aikin akayi.”
“Toh amma kasan zasu bibiyeka? Daga kai.har ita ba zaku tsira ba” daga haka ya tsaya cak.
“Ni ba Monster bane, sabida ba zan iya kashe mutum ba, amma a cikin yan uwanki an rasa waye yake kashe ni a kowani rana a kowani wayewar gari Meye nayi musu da zafi har haka?”

     “Kayi hakuri” ta fada tana kuka me mugun ban tausayi har gidan Ummin suka kawo ta, tare da cewa.
“Nan babu wanda zai iya cutar dake tunda mijinki baya kasar, amma ki sani zamu magance wasu abu dole zamu waiwaye ki” daga haka suka wuce abin su. Domin kuwa suna da uzirrruka a gaban su.

   Jikamshi House.
“Innalillahi wai kun ji motar Atikah yayi hatsari.” Inji Hajiya Shuwa, tana kallon wayar ta da aka Turo mata sako yanzun yanzun nan, ta wani Bussiness partners din su, kafin kace me har labari ya bazu Hajiya Humaidah Abbas Jikamshi ta rasu, abinda yan uwanta suke bukata kenan, sai da aka gama yayyata labarin kafin da suka isa Asibiti labarin ya sha banban, domin Dr Namir Adamu Abbas Jikamshi ya tabbatar da babu ita cikin motar driver ne kawai ya mutu. Shiru suka yi tare da cewa.
“Tabbas Allah ya kare ta.”
  Bayan sun bar asibitin yayinda wasu abun bai musu dadi ba, wasu kuma sun ji dadin haka domin ko babu kome an tauna tsakuwa kuma aya taji tsoro. Dan haka ba zata kuma d’aga musu murya ba, dan haka suka kirata suna mata jajje, zunzurutun ta razana ma baki daya ko maganar arziki ta kasa yi. (Shi rai daya ne matsalar baka san irin mutuwa da zaka yi bane Hajiya Humaidah ban ga laihin ki ba😭)

    Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a bangaren Yaran Ammyn shekara da ta zagayo ta fara karatunta a Jami’ar Abuja, a gefe guda kuwa Namir da Jamilah, sun kulla wata irin soyayya me mugun shiga rai da tab’a zuciya kuma iya makarantar abin nasu yake tsayawa, sai kuma wani lokacin idan babu makaranta tana dan yiwa Ammyn karya ya tafi wurin shi, a hankali soyayyar su ta fara sake layi ta hanyar da wani lokaci zai rungume ta, ko ya sumbaci wuyarta so irin dai dirty romance love. Abu daya taki yarda da shi, wato suyi having fun and sex, domin tana mugun tsoron Allah tana tsoron Ammyn. Amma duk da haka ta sauya sosai, a da tana zaman daki ne a takure, a yanzu har shigar da yayi mata, shi take ganin haka da ta sake yasa Ammyn rabuwa da ita domin tana ganin kamar ta fara dawowa cikin farin cikin rayuwa shi yasa bata hanata, amma idan da Rahmah zata zo Hutu tayi ba daidai  ba, nan Ammyn zata yi ta fada kamar zata buge ta, shi yasa Wasilah bata cika zaman gidan domin ta ce, zata iya yin laifi.

     **
Bayan shekara Hudu

UK.
Mr Jones Brinda ya kalli Dan wan shi Mr Joe Brinda.
“Kana nufin yau ba zaka kwana a London ba sai a Nigeria?” Jinjina kai yayi sannan ya ce mishi.
“Na gaji da rike dukiyar Ishaq gwara na mai da mishi kayan sa., nima ba lafiya ce dani ba, Cancer nan ba zata bar ni ba”

   Shiru yayi yana kallon kayan shi, kafin ya cigaba da cewa.
“Tun da na dawo, bani da kwanciyar hankali, sannan gashi ina yawan mafarkin Ishaq, kuma kaga yadda kome ya hab”aka babu amfanin rike su dukiyar sa, akwai estate guda biyu duk na shi ne, kuma ga kamfanoni biyu shima, nasan Ya gaya min bai da Yaro namiji, duk Yara mata ne gwara na kai musu, su zo su kula da kayan su, rayuwa babu tabbas kullum ciwon kara ta’azzara yaÆ™e.”

“Kuma gaskiya ne, ya ci ace kai mai da mishi kayan shi, domin da Amana ta maka kome, kai kuma ka cigaba da rike kayan shi.”

Mr Jones Brinda, dan asalin London ne, dan kasuwa ne da yake fita yankunan Afrika domin kasuwanci da cinikayya, mutum ne me gaskiya da Amana, nagartaccen mutun ne da yasan darajar mutane, da kan shi.

Abinda ya faru kuwa, matar shi da Ya bari da tsohon ciki, tayi hatsari shine dalilin da yasa aka kira shi, tunda ya zo ga mahaifiyar shi itama bata da lafiya dan dole, yasa ya tsaya yana nan matar shi ta mutu da babyn, bayan watanni biyar, itama mahaifiyar shi ta mutu, wannan yanayin ya saka shi jin wani irin yanayi yayi ya shan giya, a gefe guda kudin da ya kasance hakkin Ishaq ne, ya tattara ya zuba mishi a kasuwanci tare da bude mishi asusun shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button