NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

    Bayan tafiyar su Ammyn da kwana huÉ—u, sai gashi kamar mahaukaci, haka ya zo mata, jikinta yana rawa ta kalle shi har ta bude baki zata mishi magana. Cikin wani irin sassafar ya rungume ta, tare da had’e bakin su. Jikinta ne ya dauki wani masifaffen rawa, ta fara kokarin kwace kanta amma ina ya had’a ta da bango. Yana mata wani passionately kiss, wanda yasa baki daya numfashinta ya shiga fita da mugun gudu, rike rigar shi tayi da mugun karfi hawaye na zuba mata.  Kara k’amk’ame ta ya yi kamar za’a kwace mishi ita, a hankali ya sake ta yana kallon fuskarta da yake zubda kwalla. Sumbatar goshinta yayi yana faÉ—in.
“Na gaya miki ba zan iya rike kai na ba, matukar zan ga wani abu ko naji wani abu ba mamaki, na zama mara adalci a wurin ki, amma sonki shine sanadin kome” ya karshe maganar yana me sumbatar bakinta. Kamar zai cinye bakin gabaki É—aya. Sai zafi yake mata, gashi ta kasa hana shi, ganin haka yasa shi sake ta, sannan ya bar dakin baki daya.

  **
Red line life orphanage.

“Kelly Clarkson! Kinga abinda shegiyar tayi, yanzun zata isa gidan Nicole Brohna, me zata yi”

      Wayar da yake gaban ta, ne yayi kara.
“Harkalla ta fada, nan da kwana uku zan shirya kome, amma kafin nan bari mu gani ta shiga garin” ta faÉ—a tare da kallon hoton Rebecca da take tafiya hankali,  tana ganinta ne ta tauraron dan adam. Sakamakon wani karamin na’uran da suka daka mata a jikinta bata sani ba.

      “Karka damu, an gama kome nan da wani lokaci, zan gaya maka yadda za ayi” daga haka ta kalli Andrew Cuomo ta ce mishi.
“An kusan gamawa”
**
Mexico.
Ganin ana harbe-harbe,.yasa muka tarwatsa kowa ya kama gaban shi, dakyar na fada hannun wasu yan daba, garin gudun ceton rai.

   Mikewa babban su yayi, yana kallon na daya ya ce mishi.
“Tawa ce”
“Taka ko tawa!” Kafin kace me suka shiga fada da dambe kamar me, ganin haka suka shiga har bin juna, karshe haka kusan dukkanin suka mutu, sai mutum daya ne ya rayu, shi kuma ya tasa kaina sai Nicole Brohna club. Yana cewa.
“Da alamu guduwa kika yi daga hannun mutanen da suka kamo ki, domin ga shi nan, an saka stamp na an saye ki ne” ya fada tare da shafa kafadana, yana me kallon serial number jikina.

Tun daga nesa nake hango shi, tabbas shine mutumin da ta saka a jikin allon É—akinta.

     Muna isa ya wurgani a gaban shi.
“Ga wata kyakyawar ina ga gudu tayi, mai gida ka bani duk abinda zaka bani.”
“Ku bashi kyautar mutuwar shi.” Dattijo ne sosai, ya kalli wasu yan mata yana faÉ—in.
“Ku  Kai min ita turaka.”
“Maigida don Allah kar ka saka a kashe ni. Kayi hakuri ban yi kome ba” haka suka zabga mishi albarushi a kwanyar shi, kafin suka dauki mushen gawar shi, suka fitar a club É—in baki daya.

   Suna kai ni dakin matan suka shiga duka, tare da kwallo dani sai da suka tara min gajiya kafin suka shiga duba jikina, basu ga kome ba, suka fita can dayan ya dawo, tana zuwa ta dauki sabon reza, ta shiga tsaga kafadana daidai inda stamp din nan yake, ta zaro wani abu. Zata fita ta ce Min.
“Daga yanzun ki shirya yakin niman Yanci!”  Ta fita a hankali na lumshe idanuna, barci yayi gaba dani.

Bayan awa uku. Aka watsa min ruwan sanyi, bude idanu nayi, ina gani dishi dishi, komawa nayi na kwanta.  Aka kuma watsa min ruwan,
“Itace aka Turo kashe ni?”
“Bamu da tabbacin haka!” Suka gashi amsa, “ku kaita dakin horo”

   A cikin sati biyu na sha mugun walahar da har na fara zaucewa, na fara fita a tunanina.

Wata alƙaryan ita ce mafarin ƙaddarata. Akwai mutane da yawa a duniya waɗanda kowanne da kalar da yadda ƙaddara ta zana masa rayuwarsa. Wasu sukan tafi a cikin miƙeƙƙen layi mai faɗi da taushi wadda zai tallafawa rayuwarsu ta yi kyau da sauƙin cimma ƙaddararsu.
A yayin da wasu sukan tafi cikin hargitsattsun layuka masu Æ™unci da matsi da kan bar kwazazzabo mai girma da hakan sai ya zama saÆ™aƙƙiyar igiyar wahalarsu na cimma Æ™addararsu, har sai sun fidda rai a kan “Anya rayuwa zata basu damar tsayuwa a kan diga-digansu?”
    Ni kaina ina cikin waÉ—annan mutanen, kamar yadda nake hasashen ‘Anya akwai wani mutum a duniya da ya fini shiga garari duk a sanadin Æ™addara?’ Nakan ji a raina babu, duk da cewa a kwai mutane da yawa a duniya.

     Mutanen duniya dukkansu iri É—aya ne, É—abi’a da halayya kan banbance kamancecceniya ta iri É—ayan da suke ciki.
  Kamar dai yadda Unguwanni, Gari, Ƙasa,ya banbanta, haka al’adu ma sukan banbanta yanayi na al’umma, ina ji a jikina na tafi kenan, sai daiIdan na É—aga kaina naga yadda tsintsaye suke gudu a sararin samaniya sai naji ina ma ace ni ce! Ina ma a ce zan zama sakakkiyar tsuntsuyar da ke yawo a sararin samaniya! Sai dai nasan har abada ba zan zama kamar ita ba.’ Hawaye mai zafi ya gangaro a kan idanuwana.
     Zafin bulalar da na ji a gadon baya na, ya yi tasirin dawo da ni daga duniyar tunanin da na lula, kafin kuma na rarrabe na sake jin sauƙar wata sabuwar bulalar a gadon bayana, wadda na ji zafinta har tsakiyar kaina, naji kamar numfashina na ƙoƙarin ficewa a jikina saboda zafin dukan.
   Duk yadda na so na farauci numfashina daga ƙin ɗaukewa na gagara riƙe shi, saboda yadda ake min ruwan duka ta ko ina, ga kuma numfashina da ya daɗe da tafiyar burgu a tare da ni.

  Saukar ruwan sanyi ya sani jan numfashi, tare da kallon matar gabana, fasashen kwalbar da yake gabana na kalla, kafin ta fahimci abinda nufi tuni na farmake ta da kwalbar, tare da yanka gefen wuyarta ta fadi, tsallaka ta nayi na fita, ina fita na ga hanyar doguwa. Ina isa wani babban falo na hango shi zaune da wata mace akan cinyar shi, tana zaune tsirara.

    Ina shiga falon nayi sauran datse kofar, kallona yayi yadda ruwa da jini yake diga daga jikina.
“Ke me kika zo yi?”
“Nazo biyan bashin da kaci ne”

“Waye ya turo ki?”
“Jessica Simpson!”
“Ba ta mutu…” Kafin ya kai aya na harbe shi ka a gefen zuciyar shi itama yarinyar a tsora ce ta boya, shi kuwa faduwa yayi, na bi ta, tare da cewa.
” A ina muke?”
“Kina gidan shi ne da ake sayar da sassan jikin mutum.” Gidan bindiga na buga mata nayi fita na, duba harsashin bindigin nayi naga akwai saura ashirin da wani abu na rufe.

       Kafin yau ban tab’a kashe kiya shi ba, amma domin niman yanci na kashe rai babu iyaka, sannan na fito a cikin gidan, sai a lokacin na lura ai gidan a bakin teku yake, jirgin ruwa na gani da ake shirin tasar da shi, yayi lodin, ana shirin katse hanyar shiga jirgin na tafi da gudu na fada masu jirgin suka taimake ni. Ina shiga suka ta ce min.
“Sannun” gyada musu kai nayi, sannan suka kai ni wani daki.

Abinci aka bani na ci, kafin suka bani bargo na kwanta.

Ban san iya lokacin da na dauka ina barci ba, amma tabbas nayi barci me mugun nauyi, a hankali na bude idanu na.

Matar da ta kashe Maama sai Priyanna,
“Barka dai kyakyawa” tashi nayi zaune, ina kallon su.
“Sannun kin gyara mana kasuwancin mu ta hanyar kashe Nicole Brohna, daga ke har Jessica Simpson baku San gaskiya ba, amma tunda kullum aikin ku gyara mana Hanya ce, kin kyauta sosai. Ai duk abinda ya faru shirin mu ne, mun kashe Jessica domin ba zata bamu hadin kai bane wurin cimma nasarar mu, ke kuma saboda abinda kika gani na sirrin Jessica sai kika dauki aniyar fansa toh Nicole ba shi ya kashe iyayen Jessica ba Mr Andrew Cuomo, kin zama yarinya me sa’a tunda Jessica ta dauke ki, baya akwai Yaran da suka rigaki niman ta dauke su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button