WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
    “Ya isa haka! Zata samu lafiya kin ji. Ki bar kukan nan haka yana damuna” gyada kai tai tare da daura kanta a tafin hannun shi.
“Nagode” Murmushi yayi tare da share mata hawaye, sannan ya rakata har dakin ta zauna shi kuma ya tafi, sai da ya biya ta gidan ya ga su Wasilah da Jamilah, sannan ya koma gida da tunani fal ran shi.
A can gidan Alhaji Adamu Abbas Jikamshi, kuwa Hauka sosai Namir yayi sai da aka nimo likita yayi mishi alluran barci kafin ya samu kanshi. Sai dai yasan shima ya zalunci dan shi dan bai zama dole ya kuma samun kan shi cikin sauki ba.
Irfan.
Kallon Nadrah yake da takure kanta a wuri guda.
“Haka kawai kika rabu da ni, na tsawon shekaru huÉ—u, ban miki laifin kome ba. Yau dan iskanci da rashin kunya kice zaki dawo min. Fita daga cikin gidan nan kafin na sab’a miki”
  “Don Allah ka saurare ni”
“Nace ki fita” ya daka mata tsawa, wanda yasata fashe Mishi da kuka, sosai take kukanta, takowa yayi har gabanta.
“Meye nayi Miki me zafi haka? Kinsan yadda nayi kewarki? Kin yadda nake son kasancewa da ke? Shine kika tafi abinki tafi bana son ganin ki..” bai rufe baki ba ta rungume shi, tare da hade bakin su, sai da ta dauki lokaci sosai kafin ta sake shi, daura kanta tayi a kafadar shi tana sauke wani irin ajiyar zuciya.
Rungume ta yayi tare da d’ago kanta.
“Kinsan yadda na damu? Kinsan yadda nake ji? Ok zan kawo kome karshe soon inshallah” ya fada tare da had’a bakin su, ya shiga sumbatar ta. A nutse kamar zai cinye bakinta bata hana shi ba, sai ma fadawa da suka yi wata duniya na daban. Inda suka darje juna na tsawon lokaci da basu tare, kafin ya dauke ta, suka wuce dakin shi.
**
Sai da Ammyh tayi kwana uku tana barci kafin, ta farka duk sun damu Yaran basu da wani aiki sai kuka, musamman Rahmah da ko bakin kofar dakin taki matsawa kome zata yi a cikin dakin take yi, tsoro take kar ta fita ta dawo ammyn ta mutu, Wasilah ma haka, idan tazo tun safe bata barin asibitin sai dare, Jamilah ce dai zuwa biyu tayi bata kuma zuwa ba, bata zuwa ko a ina tana gida, a gidan ma a dakinta bata son magana. Wayarta ma bata amfani da shi, sabida tana buÉ—e social media zata ga abinda ya faru yana yawo.
Baki daya ta zama confusing bata da banbanci da mahaukaciyar da take hauka, a gefe guda mutane uku take jin matukar zata samu dama sai ta aika su lahira, Baba Haliru, Alhaji Adamu Abbas Jikamshi, ukun ba zata jingina kome akan haka ba, musamman mutum ba ukun nan.  Laptop din ta, ta janyo tana bincike. Kafin ta rufe.
“Inshallah ta yadda kasani kuka ta nan zan saka ka kuka”
Satin Ammyh biyu aka sallame ta, tayi wani irin laushi, tun a asibitin take yawan mafarkin Rabi’ah tana mika mata hannu, a madadin ta d’aga hankalin ta, sai ta maida hankali da mata addu’a, sosai tana jin wani irin kewar Autar nata, tasan da tana gaban ta. Ba mamaki da ta zama babban budurwa. Itama ta gama karatu zata shiga jami’a.Â
Bayan wasu kwanaki bata kuma bin takan Jamilah ba, kawai tuntubar Ummin tayi akan idan Faisal ya shirya ya tawo ayi bikin kawai a wuce wurin idan kuma suma sun fasa babu kome, sannan bayan Isha ta shiga har wurin Alhaji Muhammad Lawal Dambatta, ta mishi magana zata tafi gida, wurin danginta, zata tafi da Jamilah tunda taga kamar bata cikin nutsuwar ta.
Shiru yayi kafin ya ce mata.
“Wasilah kan ba zaki tafi da ita ba, ki barta anan idan yaso Rahmah tana Abuja kome zai zama zo karshe kiyi hakuri.”
 “Babu kome!” Ta fada a hankali, haka ta shiga wurin matan gidan ta gaya musu, kudirin ta sun mata fatan Alkhairi.
Koda ta gayawa Rahmah da Wasilah,abinda take shirin yi fitowa Rahmah tayi tana kallon ta, kafin tace mata.
“Babu inda zan tafi ba zanje ayi ta nuna ni ba, ki tafi abinki ai dama baki damu da mu ba, kanki kawai kika damu da shi. Kowa ya zama mugu har da Uwar da ta haife ka tana gudun kaddaran ka”
Ta fada bayan ta wuce su, da idanun suka bita har zata fita ta juya tare da cewa.
“Wallahi duk wanda yake da hannu a cikin abinda aka min sai na tozarta shi”
Lumshe idanun Ammyn tayi, kafin ta sunkiyar xa kanta kasa, tana jin wani zafi a kirjinta. Hawayen da yake shirin zuba mata ya danne tare da d’aga kanta sama. Tana shanye kukan bata taÉ“a zata haka kome zai zamo mata ba, Yaranta an lalata musu future din su, kome nata ya tafi a gigice babu abinda zata kalla ta ce yayi zama mata perfect sai dai ya zama akasin haÆ™a.
**
Moscow
Kujeran da yake kai yake juyawa, kusan shekara biyu baya Nigeria, sabida muhimmancin aikin da ya kawo shi nan Rasha, wayar shi a kunne yake juya kujeran.
“Eh zan shigo sai dai” shiru yayi yana kallon sakon da ya shigo mishi ta Email.
  budewa yayi tare da kallon sakon, ya karanta ya kai sau goma, kafin ya katse wayar. Ya cigaba da kallon sakon. Kiran Khalil yayi tare da cewa.
“Karshen wata nan mu hadu a Paris”
 A hankali ya zubawa agogon hannun idanu, haka kawai yake ji a jikin shi akwai abu me muhimmanci da zai cimma nan kusa, yana jin kamar wannan shine mafarin farin cikin shi, yana ji kamar farin cikin shi yake kara nufo shi.
*
 **
Kusan sati na hudu amma kullum aikin da nake mata kara sakawa yake tana kara min alkhairi, da kanta take min odar kaya, kome nace ina so kafin nace ina so zata bani, sai dai ba mamaki kodan aikin da nake kata ya fita a dokar kasa ne, haramtacciyar aiki ce ta kasada, kuma yana kawo mata kudi, bata yarda na hadu da kowa, amma zata bani aikin nayi mata kuma a sami nasara. Haka ya saka take bala’in bani kulawa.
A cikin sati ukun da nayi samu nutsuwa na kara kiba, sai wani kara habbaka nake, domin cimmar da nake samu nayi ishashen barci, yasa na kara fitowa sosai kirjina ya kuma cika tam kamar dama ina samun kulawar namiji nan kuwa abinci ne me kyau da gina jiki. Man shafawa na me kyau hatta chewgum dinda nake ci na musamman ne.
Matar nan sai da tasan yadda ta mai dani, yar gayu na fitar hankali. Idan zata tafi western club tare muke tafiya, ban da matsala da kome hatta mazan wurin idan na shiga kowa tsorona yake haka yasa na zama kamar wata boss a wurin. A hankali take haÉ—a ni da manyan mutane, masu son a musu aiki sai da ta haÉ—a ni da mutane manyan masu arziki har mutane biyar kafin tace min.
“Ki taimaka ki musu aikin su, ni kuma zan baki wani abun da ba zaki tab’a mantawa ba”
Dariya nayi tare da cewa.
“Mutuwa ko me? Cin amana ko Yaudara wane ne ban gani ba? Zan Miki aikin ki amma ba zan cigaba da zama a nan ba”
Murmushi tayi zata min magana Wayarta yayi kara.
“Ok gani nan.”
“Bayi baki bari na gansu.”
“Toh”
Baki tayi mutane uku daga Africa, sai turawa,mika musu hannu tayi suka gaisa kafin ta kalle su.
“Mun ji Ance kina aikin fashin yanar Gizo? Shine muka zo da niman ki mana. Gashi nan wanda zaki yiwa fashin” suka tura mata tap din.
“Ina yi amma sai mun duba mun gani, idan yayi yadda muke so zamu yi magana.”
“Nan da kwana uku zamu dawo domin nan da kwana biyar zai kasance anan” ya fada tare da mikewa.
“Ba a mana dole kuje wani wurin” ta fada tana Murmushi.
“Ok”
“Sir! Kaf garin nan babu irinta idan kace ba zaka tsaya ayi muku ba, wallahi ba zaku samu nasara ba.”
“Ya tafi mana”
“Shi kenan” ya fada tare da barin falon ta, mikewa tayi tare da nufar sama.
“Madam Tola! Wannan aikin zaki iya ko sai ya zo?”
“Babu damuwa”
Ta fada tare da wucewa dakin da Rebecca take, tana shiga ta mika mata tap din.