NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Mai_Dambu

3/4/22, 08:27 – Nuriyyat: 54

Zunzurutun tsoro da fargaban abinda zata gani,.kawai bata san lokacin da tayi sallama zata fita ba, ya ce mata.
“Ina zaki?”
“Hmm! Hmm! Dama… Dama…”
“Relax, koma ki zauna” ya nuna mata bakin gadon su, kamar zata fashe da kuka tsabar tsoro da tashin hankali.

    Fita yayi har tazo bakin kofar, ya juya tare da dage mata gira.
“Ki shiga wanka mana Doctor” hàdiye yawun tsoro tayi, sannan ta sunkuyar da kanta, yana fita ta juya da sauri ta shiga ban daki, tayi wanka sai da ta gyara jikinta sosai ta fito.  Tana cikin shafa turare da humra ya shigo. Tsabar kidima bata san lokacin da ta daka tsalle zuwa gadon ba, tare da jan duvet cover ta lullube kanta, kashe wutar dakin yayi, sannan ya kashe wayar hannun shi domin fadar Ummin yake sha ya dawo mata da Yarinyar ko ranshi ya b’aci, shi kuwa yayi mirsisi kamar bashi ba.  Gadon ta haura yana kallon yadda take kokarin boye kanta, share ta yayi bai kuma juyawa gare ta ba.

    Haka janyo ta jikin shi, yana jin yadda jikinta yake rawa, har kamar zata shide. Bai ce mata kome ba sai hiran da yake mata,tare da shafa bayan ta, hira sosai har da dariya, a hankali tasoma sauke ajiyar zuciya ganin yadda take narkewa a jikin shi yasa shi cigaba da bata labarin rayuwar shi da ta Bilal, haka tayi luff a jikin shi, yana bata labarin hannun shi yana saman Boons, yana wasa dashi. Babu laifi wannan yanayin ya haifar mata da wani matsanancin sha’awar da bata tasan tana da shi ba.  Sai kara narke mishi take yana kara hura mata wutar kaunar shi a ranta. Tare da tab’a gangan jikin ta. Da hira da dabarar Faisal ya shiga Niman matar shi sai da ya samu itama Likita munafuka ce, domin kuwa sunan likita ne a baki, amma itama a lungu guda gari ne da kasuwa.

         Ganin yadda yake kara sakata wani hali na jin dadi bata kawo a ranta zai tafi wata duniya na daban ba, sai da ya gigita mata lissafi ya saka yar Ammyn wani irin yanayi. Wanda tasan haka zai faru, ta karanta a likitanci, amma bata taÉ“a sanin dadin da yanayin haka yake ba, sai da bawan Allah ya juyar da ita tana kallon saman dakin shi kuwa ya zabga addu’ar sudawa da iyali, ya shiga  niman hanyar sadarwan zamani da ta gargajiya.

   Wayyo Allah kafin kace me Rahmah ta birkice mishi, har da kuka da rokon arzikin ya kyale ta.
“Ya Faisal wallahi ranar ban ga kome ba, na rantse da Allah ban gan ka ba, idan na ganka karka kyale ni”

“My Angel Aiko ki ganni ko karki ganni Allah ya nufa sai na ratsa tsakanin cinyoyinki,  Ya Allah kar ka kashe ni akan wannan koramar daÉ—in.” Ya fada yana furza da wani irin nishi, domin baki daya ji yake numfashin sa a iya wuya yake tsaya mishi. Sam bai tab’a niman mace ba, barshi idan ya tashi da jarabar shi sai ya hàdiye Æ™wayoyin shi, ya shiga ban daki yayi ta sake fitsari, yana yi yana gyada wuya.

     Amma yau gashi a saman halalin shi, ga shi akan maji dadin shi. Kawai abinda ya sani yayi ta durzanta sai yaji ta koma cikakkiyar mace. Haka ce ta faru, Rahmah tayi laushi. Tayi kuka har ta godewa Allah. Dan haka tayi shiru, tare da maida kanta pillow sai da ya gama, sannan ya kifa kan shi a saman kirjinta yana kara matsa kirjinta, tare da sumbatar kirjin.

“Nagode sosai! Nagode Rahmatullah! Nagode da kiyaye muhallina, Allah yayi Miki albarka, Ubangiji ya biya miki bukatar ki, Ammyn kuma Ubangiji ya biyata da gidan Aljanna, Abba kuma Allah ya gafarta mishi, sannun kin ji” ya fada a lokacin yana  zare jikin shi daga nata.

Zama yayi sai da ya huta, kafin ya shiga ban daki ya haÉ—a mata ruwa yazo ya shiga da ita, tana kuka tana kome sai da ya gasata sosai, sannan ya fito ya cire zanin gadon, gyara gadon sannan ya koma ban dakin ya dauko ta.
“Barci kike ji ko? Dan tsaya na kawo miki ko black tea ne”
“A’a barci.”
“Toh wallhi sai na kuma”
“Zan sha” kwantar da ita yayi, ya fita ta kawo mata, sai da ta sha. Sannan ya  bata magani, tasha sannan ya shiga ban daki yayi wanka, ko da ya fito ya samu har tayi barci, kofin ma a side bed ya samu.

**
Namir Adamu Abbas.

Duk yadda yaso ya samu jamilah suyi magana taki kula shi,  ya biyo ta gida amma fir taki yarda su haɗu, bai taɓa sanin cewa yana sonta ba, sai yanzun da ya ganta da Bilal.

   A Haukace ya tafi har kamfanin Bilal, yana office ita Jamilah.
“Jamilah” juyawa tayi tana kallon Namir,
“Wani abu ne?”
“Idan ba wani abu bane meye zai kawo ni nan? Kizo muyi magana” kallon Bilal tayi in romantic moment, shima d’age mata gira yayi, tare da tab’e baki, fitowa tai har wurin motar Namir.
“Meye oya ka gaya min ina da abin yi” ta fada bayan ya nade hannu a kirjin ta.
“Mutumin nan yana da hatsari domin za a iya farmakan rayuwar ki, saboda shi”
“So what?  Idan kuma ba haka ba akwai wani abu ne? Kasan abinda ake kira bakin ciki? Toh bari na gaya maka wallahi sai ka gan shi maza bace min a nan” ta juya zata tafi ya riko hannunta.
“Ina son ki. Wallhi ina son ki” a hankali ta tako gaban shi ta ce mishi.
“Wallahi bana sonka, wallahi bana son ka. Kaje mahaifinka ya baka Yar masu arziki da kyakyawar asali ni kabar min rayuwata nayi rayu cikin salama.”

   Daga nan tayi tafiyar ta, domin baki daya bata ma ta shi, kuma har yau ita kanta bata san waye take so ba, domin zuciyarta ba bata barta ta fahimci waye take so ba. Tana shiga ta samu yana waya, zama tayi bayan ta sakar mishi murmushi.
“Ok! Nagode sosai, idan dai kika samu wani labari kome kankantar shi ki gaya min”

Haka ya kashe wayar shi, sannan ya kalle ta, Murmushi yayi mata kafin ya shiga gaya mata abinda zasu yi,na kasuwancin da hannun Jari, zuwa rana can ya umarce ta su je ya kaita su ci abincin.

  A dan jikin kamfanin akwai shagon wata me abinci, dayawa ma’aikatan kamfanin shi anan suke cin abincin rana.
Haka suka fita a tare, har shagon. Abincin da take so shi yayi musu oda, taci amma shi bai wani ciki sosai ba, haka ya biya suka fita ya kaita gida.

A bangaren Rahmah da Faisal wallahi wani irin soyayya yake mata kamar zai maida ta cikin jikin shi,ga kulawa da tattali, sai da aka kwashe sati Daya ana amarci domin baki daya zama yayi ya koma kamar wani abun tsoro.

   Sun yi shar da su, amma kuma ta rame.  Amma kuma tayi kyau ta kara nutsuwa. Haka ya mai da ita gidan Ummin bayan ya gama hada mata zafi da gajiya. Tunda ta shiga falon yan uwan shi da su NaNa da Seyo, suka lullube ta da hira wanda duk rabin hiran da turanci ne.

Ga wani irin kaunar da Uwar mijinta take Mata, shi kuwa Faisal sai wani cika yake yana batsewa. Koda Bilal ya zo ya kai ƙarar Ummin, a sace ya kalli Rahmah, sai da gaban shi ya fadi domin yanayin da tayi mishi kama da yarinyar nan sai da ya kuma kallon ta, kafin janye idanun shi yana dafa goshinsa.

   **
Tafiyar sati biyar da kwana huɗu, ya kawo mu babban tashar jirgin ruwa na Lagos,  kallon mutanen nayi tare da cewa.
“Yanxun ina xan zauna?”
“Zamu kai ki gidan Marayu ne, kafin ki samu garin ku.”

“Yawwa me sanko, ka kawo shawara kuwa.  Daga yau bani ba, karku manta kowacce mace tana da kimarta, sannan abinda kuka kuka yad’a zina ne, kuma bai dace ba  dan haka a kiyaye gaba” na fada ina kallon su.
“Toh ko Maah”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button