WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
   Wurin shi na koma, na Kalle yadda suka yi da motar shi. A hankali na Kalle shi domin ina cike da haushinsa.
“Ko awa ashirin da hudu ba ayi ba, da na fidda kamfanin ka daga matsalar durkushewa, bawai ban san me nake bane, na tsaya ku bani hakkina ka wuce nasan me zanyi da shi? Haka bai maka ba,nazo cikin daren nan Niman hakkina ka ki kula ni , karshe kayi tafiyar ka.” A hankali na bude motar na zare shi tare bashi damar ta cire sit belt din shi. Dakyar ya cire,
  Fitar da shi nayi a cikin motar na kwantar da shi a ƙasa, na durkusa a jikin shi, ina kallon fuskar shi.
“Ah.. Ah…” Saka hannun nayi a jikin shi na lallubo wayar shi, na ce mishi.
“Akwai key ne?”
Juyar da kan shi yayi, a hankali na bude wayar na shiga wurin kira anan naga Faisal Bro.
A hankali na kira wayar na saka a kunnen. Yana shiga daga can ya ce mishi.
“Bilal lafiya?”
“Hm bashi bane, yana kan babban titin kamfanin shi yayi hatsari, kazo akan lokaci domin kamar zai mutu ne”
“Ok…ok…ok…ok.” ya fada tare da kashe wayar, mikewa nayi domin dare yayi nace mishi.
“Duk inda ka ga mutum karka rena mishi domin baka san wani irin baiwa Allah yayi mishi ba.” Na saka kai nayi tafiya ta.
  Wacece haka? Wacece ita?
Da wannan tunanin ya suma. Nayi tafiyar da ban tab’a ba, karshe dakyar na samu motar taxi da ta mai dani gida. Ina shiga na kawo mishi kudin shi, ko ta kan su ban bi ba, nayi kwanciya ta.
  …
Tana barin wurin Faisal da motar asibiti,suka iso aka dauke shi aka kai shi JF Hospital. Cikin gaggawa aka rufa akan shi. inda suka ceto rayuwar shi dakyar,sannan suka mai dashi ICU.
Anan Faisal ya kwana, washi gari sai ga Ummin su, nan suka shiga damuwa .
..
Karfe tara na tashi, wanka nayi tare da fita domin ban karya ba, na nufi asibitin. office din Likitan na nufa.
“Dr akan Yaron nan ne ba za a kara mana kwanaki ba ko nan da sati”
“Gaskiya nan da kwana huÉ—u zan iya kara muku domin idan ba a wanke kodar ba mutuwa zai yi”
  Kwalla ne ya cika min Idanu na, dan haka na fito, tare da isa dakin, rike hannun shi nayi kwalla na zuba min.
“Ki daina kuka Allah yana kallon mu”
Gyada mata kai nayi tare da cewa.
“Eh Mama, bari na tafi wurin aikina”
Haka na bar asibitin na tawo wurin aikina, anan nau’ie labarin abinda ya faru. Shiru nayi domin yadda naga ana kara maggi da su onga a labarin yasa na share kowa na cigaba da aikina. Da aka tashi na leka ko zan samu wanda zai biya ni babu labarin haka na koma gida.
  Mutum ba zai gane halin da nake ciki ba, sai ranar da kaga irin halin da nake ciki, a wannan lokacin domin ceto rayuwar Abraham nayi fatan koda jikina ne na bayar a kwanta da ni domin rayuwar shi.
Yau sauran kwana É—aya ya rage min, dan haka na rasa me ke min dadi, haka na wuni a wurin aikina.
**
Tun jiya ya farka kalaman yarinyar ce ke mishi yawo a kai ya cewa Faisal.
“Ka biya yarinyar nan da tayi aikin nan?”
“A’a ina jiran ka ne”ya bashi amsa,
“Me yasa baka biya ba? Kasan halin da take ciki a lokacin? Haka kawai ba zata yanke zunzurutun kudi haka domin kawai jin dadin ta, ka tabbatar ka biya yau, sannan ka bibiye al’amarin ta ina jiran ka daga yau zuwa gobe”
  Mikewa yayi tare da daukar jacket din shi, ya fita yana faɗin.
“Nasan sun kusan tashi bari na hanzarta”
 Fita yayi da sauri, koda ya fita banki ya fara zuwa ya cire kudin. Yana isowa gidan Abincin a motar shi, ya hangota ta fito daga kamfanin, tana tsaye sai wasa take da kafarta, hannunta sanye cikin wandon ta, a hankali ta saka bayan hannunta ta goge fuskarta, cikin shashekar kuka. Ta juya zata tsallaka ta nime abin hawa, ya isa gaban ta. Sauke glass din motar yayi tare da cewa.
“Yan mata, shigo na kai ki gida” kallon shi tayi sam bai mata kama da mutumin banza ba, dan haka ta shiga motar. Kallon ta yayi sosai yadda take kokarin danne kukanta. Kamar Rahmah. Da yadda idan tana kuka take share kwalla da bayan hannu.
“Kina kama da da mata ta” d’ago kai tayi tana kallon shi kafin ta ce mishi.
“Ni”
“Eh ke”
Saka mata yar karamin ledar da kudin yake ciki yayi sannan ya ce mata.
“Kiyi hakuri, gashi inji me kamfanin ya manta ne, kuma bai da lafiya Maybe kin ji labarin yayi hatsari, ina zaki na ajiye ki”
Bude kudin nayi tare da cewa.
“Da gaske nawa ne? Toh maza kai ni asibitin” na fada mishi. Sai share kwalla nake ina murmushi har muka isa asibitin da aka kwantar da Abraham, na fita a motar tare da kallon shi na ce mishi.
” Na gode Allah ya bani damar biyanka kai ma” na kwasa da gudu, sai cikin asibitin. Juyawa yayi abincin.Â
Office din likita na nufa, na bashi kudin da kome ya ce min.
“Ki je can ki biya, sai ki dawo min da risit”
“Toh Nagode” na fada da gudu na fita. Murmushi yayi yana faÉ—in.
“Wannan yarinyar ba dai tausayi ba”
 Ina zuwa biyan aka ce dubu dari uku da hamsin ne, mika mata kudin nayi nace.
“Dauki naku ki bani sauran” haka ta bani na koma wurin shi na biya, sannan na shiga dakin da suke da Ihu ba fada kan Mama ina tsalle, na gaya mata na biya kudin, kallona tayi tare da juyar dani, kafin tace min.
“Me kika bayar haka aka baki kudin” saka hannu nayi a bakina nayi ina fadin.
“Na rantse da Yesu Almasihu ban yi kome ba, Mama ki yarda dani ko hannunsa ban bari ya tab’a ni ba, ki yarda wallahi ban yi kome ba”
Rike hannuna tai tare da cewa.
“Taya zan yarda ke dai kiji tsoron Allah” ta gaya min. Jikina a sake na juya tare da fita, murmushi tai tana cewa.
“Rebecca nasan ba zaki tab’a bada kanki ba” ta fadi haka tana kara jin kaunar Yarinyar a ranta,domin iya gaskiyar ta, ta hango ba wai kawai taimako ne da ita ba, tana da tausayi da kawazuci.
     Ai kuwa daga nan gidn mu na wuce na zuba kudin a wurin Mama na ce mata.
“Mama gashi na biya wancan, wannan kuma a sayi abincin muci ko” na fada cikin farin cikin.
“Allah yayi Miki albarka.” Su kan basu san me suka yiwa Allahya kawo musu Rebecca ba, amma sun san dai basu yi aikin da Allah zai jikan su, ya basu ita a matsayin me taimako a gare su.
  *
Kallon shi Faisal yayi yana faÉ—in.
“Kai yarinyar nan babu abinda ta rage Rahmah wallahi hatta yanayin kukan su.”
Share batun yayi yana kallon sama, kafin ya ce mishi.
“Ka samu yarinyar da ta taimaka min jiya”
“A’a ban same ta ba, a wurin wallahi amma kai kaga fuskar ta ne?”
Dafe goshinsa yayi tare da cewa.
“A’a,saboda raunin nan wajen ya hanani ganin ta sai dai dishi dishi na gan gefen saman Idanunta”
“Allah ya kyauta amma ban danganta ba”
“Toh taya aka yi har haka ya faru” ya fada yana kallon Faisal.
“Akwai mutanen da suke bibiyar ka”
“Ban sani ba, amma kuma ina da yakinin Hannan ta sani”
Maganarta ne ya dawo tunanin shi.
Idan ka cigaba da rike ni, tagwayen hare hare zasu cigaba da zuwa maka bazata, idan kuma kana ganin wasa ne na kara maka lokaci kayi tunani da kyau
Dafe cikin shi yayi tare da cewa.
“Akwai mutanen da ban san dasu ba, amma kuma suna farmaka akan me?” Kiran wayar Thomas.
“Kuji da ita sai tayi magana, ku kyale ta zan zo idan naji sauki”
“Wacece?”
“Hannan” ya fada mishi,. Kallon tuhuma Faisal yayi mishi,a hankali ta bashi labarin haduwar su, kafin ya kara da cewa.
“Ba iya yau ba ta jima tana nima na, sannan idan ka lura da kyau, wannan farmakin an jima da shirya shi, dan haka ba sabon abu bane”