WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
Shiru yayi yana kallon kasa kafin maganar ta ya zo kan shi.
Naji labarin kayi budurwa Har kuna Bussiness tare,ya zaka ji idan aka ce wani abu ya same ta? Ko bata da ahali ne?
“Oh Allah, don Allah maza ka tafi gidan su Rahmah ka É—auke Ammyn su da ita kanta Jamilah ka kawo ta gidan Ummin ka tafi da jami’an tsaron farin kaya,zasu fi baka haÉ—in kai”
  Fita yayi da sauri, kafin Bilal ya kuma kiran Thomas.
“Zan kira ta Video”kashe kiran Yayi ya kira ta Video call.
    Hasko fuskar Hanan ta sha wahala, amma baki daya taki magana.
“Hannan! Ki Kalle ni, zan sake ki amma babu ruwan Jamilah a cikin maganar mu”
“Kace zaka hakura sabida ita ko? Shi kenan.”
   Haka yasa aka sake ta, sannan ya kira Faisal ya tambaye shi su Ammyn.
“Kasan bata da lafiya, toh gata ma zan kawo su asibitin idan taji sauki sai na kaita gidan Ummin”
Kashe wayar yayi baki daya jikin shi yayi Masifar sanyi,. Bayan wasu mintina. Sai ga shi sun iso, tambayar shi Jamilah ta fara ya tsuke fuskar shi dole tayi shiru.
An kwantar da Ammyn, tare da saka mata ruwa, tunda tasaka Rabi’ah a ranta ta daina barci, dan haka Faisal da kan shi ya tsaya tare da kiran Lubnah ta turo mishi Rahmah.
  **
Washi gari
Akayi Aikin Abraham, ranar kamar zamu yi yayya dan murna, ko aiki ban je ba, sai Washi gari.
Ina zuwa matar da take da asalin gidan Abincin tazo. Sai dube dube take.
    “Rubi sai yau” inji Natasha.
“Kin san anyiwa Abraham aiki koda, shi yasa ban zo ba jiya”
“Ok ya jikin shi?”da sauki.
“Sun biyaki kudin kenan?”
“Eh sun biya ni”
Juyawa matar tayi da taki muna magana kasa ƙasa.
Kallona tayi nima na d’ago kai, tare da zuba mata ido. hà diye yawu nayi kamar na santa.
“Meye sunan ki?”
“Rebecca”
Gyada kai tayi, sannan ta fita bayan ta kira Hajiyar da take kula da abincin,
“Ki kula da yarinyar nan.”
Sannan tayi tafiyar ta.
Haka muka gama aikin mu anan ne suka ce mu tafi mu gaida da Me kamfanin nan,domin shi yana da mutunci.
Babu yadda muka iya, haka muka shirya bayan mun sauya kaya,muka tafi asibitin.
  Akwai abinda ake kira Kaddara, dan haka zan iya cewa itace mafarin kowacce yanayi da na tsinci kaina, mun isa asibitin, a hanyar shi takalmina ya tsinke, durkusawa nayi na dauka, daidai wucewar wasu yan mata,.kawai sai jin kar’ar gyara kunamar bindiga nayi, a kunne na,nasan shi na san Meye ake kira da target. Ina d’ago kai na hango wani matashi rike da bindigar. Dutsen garahul na dauka da mugun sauri na na jifa inda nayi karan yana fitowa, kafin kace me, ya same shi a goshi, yake yayi harbin a sama, sai kawai karan bindigar aka ji tauu… Abinda ya ankara da mutane kenan, aka fara guje guje. Security din asibitin suka nufe shi, ni ma nabi yan ayarin gudu zuwa cikin asibitin. Eh mana.
Shi kuwa mutumin an aiko shi ya harbe jamilah ce, dan haka ita da Wasilah sun fita bakin hanya sayan fruit, suka dawo dama yana bibiye da su, shine suka wuce Rebecca tana gyara takalmin,
Wannan kenan.
Shiga asibitin nayi ina niman inda suka bi, a kidime naga Natasha.
“Ke ina kika tsaya?”
“Wai naji harbi ne na je dubawa naga Meye ya faru”
Jan hannuna tayi ka nufi can cikin asibitin. Wani part daban muka nufa, inda aka rubuta VIP Wards. Tab’e baki.nayi tana shiga kamar zata yi kuka ta cewa Hajiyar.
“Kin ga shahshanci wai tsayawa tayi ta kalli harbin fa? Sai kace wani abin arziki harbin ma abin kallo ne?
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
Mai_Dambu
3/4/22, 16:02 – Nuriyyat: 57
“Hmm kone dai baku dauka da muhimmanci, amma ni da kin barni sai na nimo yadda harsashin yake fita, kawai daga jin kara mutane sai gudu suke,kawai ina son naga yadda ake.”
“Ki mana shiru” suka daka min tsawa, tura baki nayi ina kallon su,
“Alhaji ashe abinda ya faru kenan? Allah ya kiyaye na gaba”
“Amin Ya Allah” ina gani suka gaishe shi, amma ban ko kalli inda yake ba, shima kuma bai damu da ya kalli inda nake ba.
“Ba zaki gaishe shi ba?”
“Ke kyale ni” fada bayan na kalli inda yake,kamar ban san ya faru ba. Na ce mishi.
“Barka dai! Ikon Allah wacce irin sarauta aka baka ne haka? Irin wannan gamon da ka sha sai kace sarauta. Ok Yanzun gaya min taya akayi ka sha uban daurin nan? Kut mukami” make ta Natasha tayi, tana mata magana Æ™asa Æ™asa.
“Baki da lafiya ne?”
“Nice gadon asibiti, kin ga kun wani zo kun saka shi a gaba kuna gaishe shi. Shi kuwa fuska kamar an matse lemo da idanun shi ciki ciki kamar yan China….”
Tushe min baki Natasha tayi muna fita kamar zata mare ni.
“Baki da hankali ne?” Tura baki nayi ina fadan cewa.
“Daga turu nake. Idan baku son haka ku daina mishi abu kamar kuna bauta mishi dan yana da kudi ba yana nufin yana da kome Bane mutumin da ya kasa kare kanshi taya zan gaishe shi”
 Wuce ta nayi abu na, ban kuma bin ta kanta ba, sai da nazo bakin daya Wards din naga sun cure wuri guda suna kuka, dauke kai nayi ina jin tausayin su. Ina tafiya gaba kadan Naji ana cewa.
“Eh lokacin da abin ya faru, tabbas naga ya fadi kafin yayi harbin amma ban san waye yayi sanadin faduwar shi ba.”
Dauke kai nayi ina jin dariya yana kama ni, yadda nayi kome cikin tsanake babu wanda ya ganni, har na fita sai yan sanda da sauran É—ai É—anku mutane.
  A bakin asibitin na samu taxi, har asibitin da aka kwantar da Abraham, anan muka zauna sai dare muka dawo gida. Aikuwa washi gari da nazo aiki kamar hajiya zata dake ni dan jin haushi, ni kuwa sabida samun lafiyar Abraham yasani jin kamar na samu yancin.
 Yancin sosai, dan kiriniyar da ban yi ba da shi nake, yi wasa da dariya tare da niman magana da tsokana nasa su a gaba, a hankali sai ga jama’a sun kara cika wurin cin abincin. Domin kuwa idan aka zo nayi ta saka su dariya.
  Akwai wani mutum Ashe saurayin Yomi ne, abokiyar aikina. Dan mutumin nan kawai ganin yadda nake kawai ya shiga bina har da nuna min shi fa sona yake. Tun ina share shi har na fito na gaya mishi gaskiya. Jin Haushin haka ashe ya gayawa Yomi. Ina shigowa shago domin na makara ban zo da wuri ba, sai karfe biyu.
“Hajiya kiyi hakuri, Kanina ne bai da lafiya jikin shi ya tashi sai yanzu na bar asibitin.”
“Ok ya kamata ki nime wata gaskiya domin zai taimaka Miki koda baki kusa za’a sani”
  “Nagode zan saya” fitowa nayi naga an cika shagon. Ban yi aune ba sai ji nayi an saka abu an farka riga na ta baya. Kowa yaji karan yagar kamar abu aka saka aka ja da karfi. Daidai na dauko abincin mutane. Wani irin duka kirjjna ya fara, ina kallon kasa.” A hankali nake tafiya da baya, ji nayi kamar an tsaya a baya. Kwalla ya cika min idanuna.
“Ki tsaya” jikina ne ya dauki rawa, haka ya cire Jacket din suit din shi ya saka min, a hankali ya amshi abincin. Ban iya kallon shi ba, na koma dakin da muke ajiye kayan mu,na dauki karamar jakata, na fita daga wurin cikin abincin.
   Sai da nayi kwana uku ban zo ba, ranar da nazo ya kama ranar Juma’a, ina shiga na mutanen cikin shagon suka fara murnan dawowa na.
“Rubi! Yee ta dawo, mun yi kewarki”
“Nima haka”
Na shiga na ajiye jakata, ko dan ta ga nayi yarinya ce kawai sai naga ta taso min zata buge ni, kallon ta nayi tana zuwa na take kafarta sai da yayi ƙara. Kafin na sake kafana a kan shi. Aikuwa ta sake ihu, da niman a gaji ban kuma bin kanta ba, na fito abuna.