NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kiyi hakuri mana, wallahi da aikin nan nake rike da yan kananun marayu, idan aka ce yau bani aiki ya zanyi da kannena marayun?” Na fada kamar zan yi kuka.
“Oh ke kika sani” kallon Yomi nayi tare da cewa.
“Ba zan bar shagon nan ba sai ba fasa Miki baki” sun zata da wasa nake sai da suka ga da gaske, na shake ta, tare da zabga mata naushi a bakin ta, sannan na kyale ta, ina ji kamar na rufe ta da duka.
“Muguwar banza kawai yar bakin ciki.” Na fito ina tufke daurin gashina baya.

    A waje na hango shi, dauke kai nayi ya d’ago min hannu yana min magana. A matukar fusace na isa wurin shi.
“Me zan maka?” Na tambaye shi.
“Me ya faru naga Fuskar ki kamar ba dad’i” cizon lips dina nayi tare da hararan shagon abincin.
“Kora ta suka yi, ya zanyi da kannena marayun?” Na fada cikin matsanancin fushi.
“Ayya kiyi hakuri, and idan babu laifi ba Baki aiki a kamfanin mu man?” Kallon shi nayi irin kallon sama da kasan nan. Shiru nayi kafin nace mishi.
“Kuma nawa zaka biya ni? Sannan wani irin aiki ne?”
Tabe baki yayi tare da cewa.
“Biyo ni” bin bayan shi nayi tare da cewa.
“Wai tukun wurin computer zaka kai ni? Idan can ne kuwa akwai gurmi domin sai na kamo wanda yayi kokarin hakkin din kamfanin ku”

Juyowa yayi a dan fusace ya ce min.
“Idan kika cika magana Bilal Ahmad Jikamshi koranki zai yi!” Sake baki nayi tare da kallon shi sama da kasa kafin nace mishi.
“Kuma sai na zama dumb sabida shi? Kawai na fasa ma aikin” juyowa yayi tare da d’aga kafadar shi alamar oho.

   Shiru nayi ina tuna yan kanne na.
“Toh zan yi aikin!” Na fada ina tura baki,
“Muje” shima yayi min yadda nayi mishi, yana dariya. A hankali yake tafiya ina bin bayan shi. Har zuwa cikin kamfanin, haka kawai take mishi yanayi da Rahmah da yan uwanta.
“Rubi!”. Inji baba Tunde.
“Bana tunde” na mika mishi hannu muka tafa.
“Yau baki shagon alaja ne?” Tab’e baki nayi sannan nace mishi.
“Sun kore ni!”
“What!!?”. Gyada kai nayi cikin wasu irin kwal-kwalar idanuna, kamar zan fashe da kuka.
“Eyya! Sorry kin ji” gyada kai nayi tare da cewa.
“Ya wuce, ba gani nan yanzu naxo nan ba”
“Kuma gaskiya ne fa” shi kam Faisal yayi gaba abinshi sai da ya kusan office din shi ya tuna ai tare suka shigo da ita, juyawa yayi ya hangota tsaye tana kallon computer din Baba Tunde tana tab’awa. Tsayawa yayi yana kallon su, har ta gama suka kuma tafawa.bai san me suke fada ba amma ya lura Baba Tunde godiya yake mata.

Murmushi tayi tare da gunkula hannu suka gaisa sannan ta juya tana niman.
“Hmmm” yayi mata gyaran murya yana d’ago mata hannu, da dan sassarfa na isa wurin shi.
“Ke da muke tafiya Meye na tsayawa a can?”  Juyawa nayi na kalli Baba Tunde, na d’aga mishi hannu sannan nace mishi.
“Kawai wani abu ne? Taimako nayi, computer din shine ya samu matsala ba dan na duba ba, abin da yafi haka”

“Sannun Microsoft” murmushi nayi domin ya bani dariya, shiga yayi office din na bishi, ina shiga naga yar karamar office ce, sai tarkacen kayan karatu, dan gaba wata kofa ce. Ya bude a hankali garden ce, har kamshin fure yake.

  “Nan wurin wutar Bilal ne, kawai lambun zaki na kula da shi,muje ba nuna miki staff office,inda zaki ba zama. Ai kin ji na gaya miki nan ba wurin zaman ki bane! Kin ga zan baki dubu talatin duk wata, idan kika yi sanadin da Bilal ya kore ki ke kika sani” zuba hannu nayi a cikin Aljuhun  rigana ina kallon shi kafin nace mishi.
“Nifa ba zan tab’a yin abinda zai kore ni ba, sai dai idan kai ne zaka gaya mishi na cika faÉ—a”

“Ke!” Ya daka min tsawa, tura baki nayi tare da kallon shi nace mishi.
“Ka kawo ni nan ne dan kana min tsawa” na fada kamar zan yi kuka.
“Shi kenan! Koyi yadda ake shiru”  yayi gaba ina bin bayan shi,sai mita nake kamar wata tsohuwar da ta shekara tamanin,babu laifi staff office din Babba ne me É—auke da manyan kujeru sai wata yar karamar Coffee machine. Kallon shi nayi tare da kallon wani locker an zuba snack.

“Yallabai kuma duk wannan kayan dadin duk na ma’aikatan kamfanin nan ne?” Na tambaye shi. Ina hàdiye yawu,
“Kwadayayya kawai”
“Sai masifa kake ta min” na fada tare da ajiye jakata.
“Anyi miki kuma saura kiyi kiriniya dan nasan zaki aikata” sake tura baki nayi ina mita.
“Da kin daina tura bakin nan dan ba kyau yake Miki ba” ya fadi haka tare da barin office din, murmushi yayi sannan ya nufi waje. Wato tunda ya tafi na samu madara da sugar na hada ayar karamin mug, na zuba ruwan zafi ina tafawa a raina zan sha Coffee.

Kai babu abinda yafi yanci dadi yaushe na samu damar shan Coffee a baya, cika kofin nayi na debi snack ba zauna na cika cikina,sannan tayi gyatsa dadai shigowar Amaka da Kamilah suna zuwa wurin cin abincin mu.
“Rubi”
“Na’am! Sai kuka ganni a nan kawai”
“Gaskiya ko babu kome zamu sha dariya” suka tafa, haka muka yi ta hira har suka koma wurin aikin su,ina zaune masijan yallabai Faisal ya zo ya bani wani abin ban ruwa, na shiga lambun na fara ban ruwa, ina yar waka ta. Har na gama sannan na karkabe office din na share na gode da kayan aikin da na gani a cikin shi.

    Karfe hudu muka tashi, da zan tafi gida na ga Hajiya ta fito tare da mika min jakar kayan abincin da nake tafiya da shi gida.
“Nagode sosai”
Sai da na biya ta asibiti na duba Abraham, sannan na wuce gida.
**
Shiru yayi yana tuka motar ya zubawa hanya ido.
“Me yasa baki daya ka sauya?”
Kallon ta tayi a gajiye, kafin ya ce mata.
“Bilal bai da lafiya, sannan ga shi kema baki da lokacin kanki balle na samu natsuwa, baki daya bani da nutsuwar da ta dace kome ni nake handling din shi taya kike ganin zan nutsu?”

A hankali ta narke mishi, tana wasa da hannunta saman nashi.
” Kayi hakuri, muje yau ina da lokacin ka”
Jan hancinta yayi, a haka suka isa gidan Ummin, anan ya gwangwaje matar shi, domin yayi kewarta sosai. Itama tasan halin mijinta,yana da hakuri sosai dan haka bata wani d’aga hankali ba, ta bar shi. Ganin yadda take narke mishi tare da shagwab’e mishi Rubi ta fado mishi a rai. Murmushi yayi sannan ya  shiga bata labarin darune rubi.  Kallon shi tayi tare da zama tana kallon shi sosai a karo na babu adadi.

“Kawai ka gaya min kayi budurwa ce, kawai babu wata me kama dani”  ta tashi tare da barin shi zaune, yana mamakin yadda ta kasa fahimtar ganin idan ya ce zai bata labarin Rubi zata dauki zafi yasa shi kame bakin shi.  Ya bita ban daki sukayi wanka tare.

Bayan sati Daya aka sallami Mr Jikamshi, ko kwana biyu bai yi ba. Ya wuce Korea domin hankalin mahaifiyar shi yayi mugun tashi, gani take kamar yana cikin bad condition ne yake boye mata, shi yasa ya tattara baki daya zai fi samun kwanciyar hankali idan yana tare da mahaifiyar shi shima.

   **
Sai da Ammyn tayi kusan sati biyu kafin ta samu lafiya, aka sallame ta domin Wasilah da Jamilah kamar wuta da auduga, musamman lokacin da Aaman yazo gaida Ammyn, wani fisgar da Jamilah take ne Wasilah ta ce mata.
“Aikin banza harara a duhu, Ya Aaman ya Aunty Husnah?” Murmushi yayi tare da cewa.
“Wasilah Husnah tana gaishe ki, ta bani sakonki”

“Wow don Allah ka bawa Mammyn ta ajiye min idan na dawo zan zo ba amsa, Don Allah Ya Aaman ayi bikin ku a wuce wurin i can’t wait to see your beautiful kids”
“Allah ya shirya ki”.
“Amin Ya Allah”
“Mtseww” jamilah ta ja tsaki tare da kallon su ta watsar.
“A dangin su Baba Haliru anan aka samu tsaka” inji wasilah ta fada Æ™asa Æ™asa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button