NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

   Cikin tantama da abinda Yaya Haliru ya fada, ya kalle shi kafin yace mishi.
“Ina ruwan ka da su? Idan ba karambani ba irin naka Meye zai kai kai, yo ko q gabana suke iskancin su indai ba Yarana na cikina ba, wallahi babu abinda ya dame ni, dan haka. Babu ruwana da hidimar yaran Ishaq kome za su daya ne, basu gabana balle su hanani rawan gaban hatsin, kuma ba zan musu magana na, domin ina da abin yi a gabana.”

  “Idan kuma aka yi rashin sa’a dan tauren ne ya barbari yar dan uwan shi fa? Ana yi ana tuna akwai Allah fa.” Inji matar Yaya Haliru.
“Sabuwa wannan wacce irin magana ce? Taya zaki jefe ni da irin wannan maganar?” Ya fada a fusace, dariya tayi tana kallon shi.kafin ta ce mishi.
“Mutumin da bai iya dauke kai akan Æ´aÆ´an makota ba, nashi ma Dan ya yasan duniya zata yi MISHI tofin alatsine ne yasa ya dauke idanun shi, amma dan tauren ina zai iya dauke kan shi.”

   Tana gama fadar haka ta bar dakin, da harara ya bita da shi, yana jan numfashi. Domin tabbas gaskiya ta fada, amma a gaban dan uwan shi bai isa ya fadi cewa shi yayi yunkurin cutar da Yarinyar ba. Dan haka bayan tafiyar Badamasi, ya cigaba da Nazarin yadda zai rama abinda aka mishi.

  *
Bayan kusan wata biyu da farun haka, hankalin Ammin ya dawo kan Yaranta, a gefen Jamilah kullum tsoron haduwa da Baba Haliru take, amma haka bai hanata kokari ba, domin kuwa malaman makarantar su, suna yaba mata, shi kan shi Malam Aaman tausaya musu yake, musamman yadda yaji labarin su, da yadda yaran suka kasance masu biyayya da nutsuwa, shi yasa da aka yi exam din first term, sune  Yaran da aka bawa kyauta na musamman, domin suna cikin Yara masu tsafta, marasa hayaniya balle fada, gasu da mugun kokari.. wannan ya sanya Malam Aaman, kara saka mata ido bayan Hutu har kofar gidan yake zuwa sayan kosai, duk da farkon hutun ya tafi garin su, sai da yayi sati biyu ya dawo.

  
    Lokacin da ya dawo da farko iya kofar gidan yake tsayawa kamar kowa, ranar da ya fara zuwa ne yayi sallama Jamilah ta fita da kanta. Tana ganin shi, jikinta ya dauki rawa, kamar yace mata wani abu yazo mata,.
“Uncle wani abu ne kake so?” Duk ta rikice, tana ganin kamar wani abu tayi da zai kawo shi gidan su. Sai da ya ce mata.
“Relax! Kosai na zo saya!” Bata amshi kudin ba, ta koma ta ciko MISHI laida, ta kawo mishi, ya mika mata kudin bata amsa ba.

Tun daga ranar kullum sai yazo amsar kosai, tun da ya fahimci bata son amsar kudin, ya cigaba da zuwa domin yana son kosan da kunun.  Ammin kuwa bata san cewa ana karya mata jari ba, dan ma Abin akwai albarkan Ubangiji. Ana sati Daya zasu koma makaranta. Da yamma garin ya dauki hadiri, duk da farkon damina ce, amma ko ina ya dauki kamshin kasa, alamar nan da wani lokaci za’a fara samun saukar ruwan sama.

     Suna zaune a tsakar gida, suna hira aka yi musu sallama, Wasilah ta fita.
“Wa’alaikumun salam, kuna niman waye?” Ta tambaye su,
“Aiko mu aka yi, da wannan kayan” buhun wake me L, sai buhun gero shima L, sannan galan din Mangyada.

   “Inji waye? Anya nan gidan ne? Ba b’atan kai kuka yi ba?” Ta kuma tambyar su.
Driver da ya kawo kayan ya ce mata.
“Eh TOH wurin Jamilah aka turo mu, kece?”
“A’a Yayata ce bari na kirata” ta juya da sauri, tana shiga cikin gidan.
“Ya Jamilah Kinyi da wani ne zai kawo miki kaya daga wani wuri?” Ta tambaye ta, zubur Jamilah ta mike tana zare ido suka fito tare, tana kallon mutanen. Ganin yadda suke a tsaye kamar wasu askarawa yasa ta komawa gefe tana kallon Kayan. Mika mata takarda suka yi.

Ta amsa jikknta yana rawa, a hankali ta bude.
Hidimar tana Yawa, Æ™arki rena don Allah kuma Æ™arki dawo min da shi domin zan ji babu dad’i a gaida min Mama

Damke takardan tayi tare da sunkuyar da kanta.
“Mun gode!”
Ta fada, tana kallon kasa kamar yana gabanta.
“Mu shiga da kayan cikin ne?”
“Hm” tace musu, haka suka shiga da kayan cikin gida, Ammin tana alola ta ga ana shiga da kaya. Bayan sun gama ajiye kayan, suka fita tabi Yaranta da ido.
“Ammih… Wallahi ban ce ya kawo ba, kinga abinda ya turo min da shi” ta mika mata, bata amsa ba. Ta shige dakinta sai da tayi Sallah suma suka yi nasu sallah.

Har lokacin bata ce musu ci kanku ba, shirun da yayi yawa ne, jamilah ta mike zata fita tace mata.
“Dawo ki zauna” jikknta na rawa ta zauna, tana kallon su sannan ta ce mata.
“Duk abinda nake ina tsare mutunci kune, ina tare daku ne domin kare mutuncin ku ne, har kin girma haka? Da namiji zai turo Miki da kaya masu mugun yawa me kike so na cewa mutane? Dan haka maza keda Rahmah ku tafi ku nime shi yazo ya amshi kayan shi. Idan kika sake raina ya b’aci zan Miki abinda sai ya saki kuka”

      Da sauri suka fita, kowacce su kuka take son yi amma babu bakin kuka.
“Ya Jamilah baki san gidan shi bane? Don Allah ba zan iya jure yanayin da Ammin mu take ciki ba”

Mai_Dambu

3/1/22, 18:51 – Nuriyyat: WATA ALKARYAR…!
The Beginning of Destiny
Na
Mai_Dambu
EWF
”’Albishir ku.. kuce min goro…ko kusan S.squar Fashion &More
Sun kuma kawo muku ingantattun kayan su kyau da rahuwasa…
Turaren wuta na zamani.
Milk candy
Hijabs da gowns tare da kayan Yaran ku masu kyau da inganci💋💃🏼Http://wa.me/+234 703 003 7697”’

Kaddararren yanayi<6>

Share kwallar fuskarta tayi tana me cewa.
“Yana gidan da yake bayan makarantar mu” ta fada da sauri suka nufi hanyar makarantar,  sun isa filin makarantar inda yake tsaye tare da mutanen da suka kawo kayan, har wurin ta isa tana me share kwalla.
“Don Allah kazo ka gaya mata ni ban roke ba, don Allah ka gaya mata ban tab’a rokon ka ba, Don Allah kazo ka amshi kayan ka, Ammin tana fushi sabida kayan da ka Turo.” Ta karshe maganar tana kuka sosai, kallon ta yayi sam kukan bai dace da ita ba, dan haka ya kalli Rahmah da take share kwalla.
“Me ya faru?”
“Ammin ce tace kazo ka É—auki kayan ka”
“Ok muje, bani key Sadam” mika mishi keyn mota, bude mata gaba yayi ta zauna. Rahmah kuma ta shiga baya, a hankali yake jan motar,.mika mata hanky yayi bai kuma  ce musu kome ba, har suka isa kofar gidan.  Kallonta yayi na dan lokaci kafin ya bude motar ya fita, ya zagayo ya bude mata itama, sannan Rahmah ta fito daga Motar. A kofar gidan ya tsaya su kuma suka shiga cikin gidan. Suna rab’e rab’e.

      Tana dakinta inda Rabi’ah da wasilah suka cure wuri guda, sabida yadda ta b’ata rai. Dake sun yi sallama kasa shiga cikin suka yi yasata ce musu.
“Ba zaku fitar min da kayan ba sai na fito da kaina?”  Yadda tayi maganar a tsawace yasa Rabi’ah fashewa da kuka, tare da k’amk’ame Wasilah tana tura kanta a jikinta, ita kanta Wasilah da zata samu wanda zata biya a jikin shi da ta makale,  domin sun san bata fushi haka, yau kuwa har da daka musu tsawa.

   “Ammih, gashi yazo daukar” Inji Rahmah da take tsaye a tsakar gida. Fitowa Ammin tayi tare da cewa.
“Maza maza ku ce ya shigo ya dauki kayan shi bana son ganin su.”

   Da gudu suka fita zauren suna haki, kallon su yayi yadda suke zare idanu.
“Don Allah zo ka É—auki kayan ka, wallahi Ammin mu duka zata mana matukar baka dauka ba” yadda Rahmah take magana, Jamilah kan ta kasa magana, sai kuka take yi Kamar wacce tayi mugun abu, ta kasa tsayuwar ma. Shiga gidan yayi da sallama. Ammih tana tsaye ya shiga.
“Assalamu alaikum! Barka da yamma Ammin mu” yadda yayi sallamar da kuma yadda ya danganta kan shi da ita, yasata dauke kan ta tare da b’ata rai, shima sai da ya kame kan shi cikin madaidaiciyar fushi tace mishi.
“Bawan Allah, don Allah ba dan na isa ba, karka cutar min da Yarana. Sune farin cikina, idan wani abu ya same su ba zan yafewa kaina ba, don Allah karka tab’a min su, nasan Yarana matsorata ne, komi kankantar barazana yana iya sawa su fita hayacin su, don Allah idan ba wani abu a tsakanin ku maza kwashi kayan ka mun gode sosai”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button