WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
  Ban tsaya ba, na shiga taxi abin na.
A can mall kuwa bala’in da Jamila take yasa baki daya hankalin kowa ya tashi, ganin tana yi da Hausa sa turanci wata mata ta ce mata.
“Amma ke Yar iska ce, uwar naki bata fi aikin ki ba, shegiya da fuska a kode Allah yasa yar yankan kai ce ta tafi da ita irin ku baku da amfani a cikin al’umma, Allah kadai yasan wahalar da ta sha dake amma kika saka mata da haka sakarya kawai”
  Haka matar ta zage Jamilah tass, sanan suma kore ta, tunawa da tayi an bata number matar yasa ta koma cikin motarta ta kira layin.
Aikuwa Rubi ta dauka.
“Ke dan Ubanki ina kika kai min Uwata”
“Tana gidan koyan tarbiyya banza sakarya mara hankali har ki dauko uwarki a cikin wannan yanayin ki kawo ta, dan rashin Imani sannan ki zauna kina zagin Ubana jaka dabba kije gida na kai ta useless kawai”
Ta kashe wayar a fusace Jamilah ta tadda motar, tana isowa Ta samu Faisal da su Wasilah sun iso, cikin borin kunya ta fara magana.
“Ammyn na me yasa zaki biyo wanda baki sani ba, idan wani abu ta faru dake fa?” Nan ma bata yi magana ba.
“Wai Meye ya faru ne?”
“Wallahi dan uwa Faisal kawai mun shiga Mall ne aka kirani, shine nace ta jira ni gani nan zuwa kafin na dawo har na damu wata yar iska yar tasha irin yan shaye shayen nan wai ta kawo ta gida, kana jin muryan ta kasan ba mamaki tazo ne taga inda Ammyn take a biyo dare ayi fashi. Ya kamata a shigar da hukuma cikin maganar”
“Amma baki kyauta ba, wallahi akan me zaki barta a mall? “
“Ah toh idan ma fashin ne su kare a kan ki banza wawuya Irin tashin hankali da muka shiga akan ki saboda rape din da aka miki, wanda sanadin da muka rasa Little sister, amma wai har kina da damar da zaki aikata kome yadda ranki yake so? Why? Kome kin ruzuga? Yanzu ba dan Allah ya takaita ba a wannan condition din idan wani abu ya faru da ita fa? Idan kin zama useless ki tsaya ina kan ki domin wani abu ya samu mahaifiyar mu zamu gwada miki danyen kai”
Inji Rahmah, kura musu ido Ammyn tayi bata iya magana ba, karshe Faisal fita fa matar shi yayi,kamar yadda ta bukata haka aka zuba Yan sanda suka tafi Mall din, domin har Washi gari Ammyn bata yi magana ba, number rubi aka bibiya har kamfanin, Dan sanda ya kira Faisal ya gaya mishi. Lokacin shi yana airport, dan haka ya ce su jira shi ya ga waye, sannan ya kira Jamilah ya gaya mata, itama tace zata kamfanin ta ganta.
 Shi Faisal dama dauki Bilal zai yi, da ya dawo daga Korea shi da Khalil, suna isowa suka rungume Juna, sannan suka nufi wurin motar, kafin Matar shi ta kira shi, nan yake gaya mata abinda ake ciki. Har yake labarta Bilal.
“Ai taimako tayi da tayi niyyar cuta ba zata bada number ta ba, kawai idan muka isa ka saka a kyale ta”
 **
Washi gari
Ina cikin ban ruwa aka kira wayata, dauka nayi, bayan mun yi mgana. Nace gani nan fitowa na gyara wurin shan iskar, har da kayan kamshi na saka.
Sannan na fito, sai da na tsaya muka yi wasa da dariya da mutanen office na fito waje, sake kirana aka yi na dauka.
“Madam kece a tsaye?”
“Eh nice”
Na kashe na saka cikin Aljuhun Jacket dina. Na isa wurin su tare da cewa.
“Lafiya?”
“Kece kika taimakawa wata mata a mall?” Hannu nasaka a cikin Aljuhun Jacket din na dauko sweet na jefa a baki nace.
“Eh! Akwai matsala ce!”
“Eh yanzu ki jira Surukin matar da Babbar Yar matan sun shigar dake kara, domin tun jiya matar bata yi magana ba”
“Toh sai aka ce wani abu zan mata?”
“A’a kawai dai ana zargin wani abu ne”
Murmushin gefen baki nayi tare da hard’e hannun a kirjina, ina jiran zuwan su.
Wata mota ce kiran Audi CRV7 ta shigo, tana fitowa ta nufo mu, bata yi wata wata ba, kawai ta kai min mari. Sai da na fadi daidai shigowar wasu mota, tashi nayi ta kuma kai min duka, cikin fusata na kama hannunta sai da na murdeta shi a baya, ina huci.
“Ba a tab’a marina ba, who are you da zaki mare Ni” na kama yatsar ta sai da naji yayi kara. Fisgo ni aka yi, dake raina a bace yake kai mishi duka nayi a fuska yayi maza ya tare dukar, tare da murde hannun, ya amshi handcutt yace musu.
“Ku buÉ—e file akanta sabida tayi laifi bayan bata amshi laifinta ba, ta kuma karya hannun Innocent lady.”
D’ago kai nayi ina kallon shi. Ina huci kafin na ce.
“Haka dama musulmai suke da zaran ka taimaka musu?”
Kura min ido yayi, Yallabai Faisal ne ya iso yana faÉ—in.
“Bilal duk da abin kai haka ba, kai kunce ta, bata da matsala gashi Ammyh ta kira ta ce a bar maganar lafiyarta lau”
  Hawaye ne ya xubo min, ana kunce ni, ban tsaya ba nayi tafiya ta.
Ita kuwa Jamilah tsayawa tai, tana nazarin fuskar Rubi.
“Oh… Oh.. oh.. Rabi’ah” kamar wacce aka kira ni, na juya ina kallon su, sannan na tokari get din shiga kamfanin na fita abin na, ban tab’a jin kuka dan wani Æ™addara ta fado min ba, amma yau mutumin nan shi yasa a tafi da ni, office din yan sanya.
 “Baka kyauta ba wallahi Sam baka mata adalci ba, muna shigowa da kai akan idanun ka Jamilah ta mare ta, sannan ita da bata da galihu ka hukuntatta Why?”
Banza yayi mishi ya bawa Iska ajiyar shi ya juya ga Jamilah da take rike da hannunta, tana matsar kwalla.
“Sannun kin ji, Khalil kaita asibiti a duba hannun.”
“Zaku iya tafiya an gama ai” ya juya ta fadawa Yan sanda.
Yayi shigewar shi cikin kamfanin. Baki daya sai yan kamfanin basu yi wani murna da dawowan shi ba, dan ko babu kome Rubih tana dauke musu wasu damuwan. Kawai sun mishi Barka ne ba irin da idan ya dawo zasu zo, kamar su gaske aka mishi murna. Sai ya s saɓanin haka. Kallon Faisal yayi yaga shima ya wuce ko a jikin shi. Share su yayi tare da shiga elevetor ya kai shi can babban office ɗin, yana jin haushin Faisal.
Ni kuwa da na wuce gida na wuce Abina,ban kuma tunanin kome ba, sai jakata kawai da na bari kuma nayi zuciya ba zan kuma zuwa office din su.
**
Yana shiga ya zauna tare da dafe kanshi, yadda ta kai dukar, kamar yasan inda aka tab’a yin hakan, girgiza kai yayi…🔥
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
Mai_Dambu
3/6/22, 08:44 – My Mtn Number: 60
Ganin zai bawa kan shi wahala, ya mike yana faÉ—in.
“Ya Allah” ya nufi wurin window office din, yadda ta mishi wani irin kallo cikin b’acin rai ya sashi dafe goshinsa da yatsu biyu. Ina jin kwayar idanun ta, har cikin jinin jikin shi yawo take.
 Kamar zai yi ihu, baki daya ya manta inda yasan irin wannan kallon, tashi yayi ya fito. har ya sauko kasa, ganin ma’aikatan kamfanin yayi kawo yayi jungum-jungum. Fitowar Faisal daga Office din shi yasa suka juya kan shi har da shi Bilal din.
“Oga Faisal don Allah ka dawo mana da Rubi” juyawa yayi yana kallon su Baba Tunde. Take suka koma kan aikin su.
“Yanzu yadda tayi fushin nan ku kyale ta zan dawo mana da ita” inji Faisal,
Sauke idanun shi yayi akan bakin Faisal.
“Nan kamfani na ne ta nime aiki kamar kowa” ya fada yana fita abin shi.
“Don Allah oga Faisal kayi wani abu yarinyar tana da kirki”
“Ai kunji me yace? Zan dawo da ita dole ne? Dole sai ya amince zan dawo da ita.”
“Kayi hakuri zata dawo koda yardar ka”
Haka ya fita ha bar su, ya nufi gidan cin abincin, ya same su Jalilah basu san Bilal din ya shigo ba, suke zagin shi ya cika girman kai.
“Haba dalla yarinyar tana da kirki fa, da bamu zo da kan mu ba ita duk take mana wannan hidimar shi kuma daga zuwan shi ya wani saka an kama ta sabida son kai. Ni ta burge ni da ta murde hannun Jamilah nan”