WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
“Ki bari kawai kamar na make shi ya cika jijji da kai, sai kace akan shi aka fara kudi. Ai naji an ce ta kai mishi duka ya tare da ta naushi wannan kananun idanun naga ta tsiya”
“Hmm!” Yayi gyaran murya, da sauri suka mike, jikin su na rawa suka fita da mugun sauri. Shigowar Faisal shagon ya zauna a kujeran da yake fuskantar shi.
“Don Allah idan akan wannan yarinyar ce ka min shiru bana son magana” ya fada a gajiye, dan ya fara gajiya da kanannun maganar mutane, kallon menu na abincin yayi, a tare aka kawo musu abincin. Wayar Bilal ce tayi kara ya dauka.
“Hello Madam, kin samu labarin ta ne?”
“Eh na samu sun tabbatar min tana nan Lagos,. A daya daga cikin gidan Marayun da suke garin. Yallabai ja cika maka alkawarin da na dauka maka Nagode”
Wani irin ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa.
“Karki damu Nagode sosai, Nagode da taimako na da kika yi?”
“Daga yau zan rufe layin ka.”
“Ok Nagode ma haka” sai da suka gama wayar ta kashe ya tuna bai tambayi sunan ta ba,koda ya kuma kiran layin an kashe. Ya gwada da layin Faisal haka a kashe.
  Tashi yayi bai yi magana ba ya fita abin shi. Haka yayi ya zaga garin lagos da gidajen marayu bai same ta ba, asalima kasa musu bayanin yake haka ya dawo gida yamma likis. Bai je masallaci ba, a gidan yayi sallolin shi ga kwanta. Wurin sha biyu ya farka da yunwa. Kitchen ya nufa ya samu an zuba mishi kayan shi musamman na firij din, bude firij din yayi ya dauko Kimchi soup. Sannan ya bude gefen firij din ya dauko roban noodles ya tara ruwa sai da ya taru ya saka ledar Kimchi soup din ya koma gefe ya kunna microwave ya saka noodles din shi ya fita, can sai ga shi ya dawo tare da ɗaukar ciro noodles din ya bude bakin shi ya juye a wani collender. Sannan ya dauki fry pan,ya juye kimchi soup din ya shiga duma ma shi. Yana gamawa ya juye noodles din a kai ya dauko maggi ya fasa a kai,.
Sannan ya koma gefe yana ya kunna ketlle ya haÉ—a Black tea, din shi ya zuba brown sugar. Sannan ya shirya a tiren ya kawo waje ya kashe kome na kitchen din ya fito waje, ya zauna yana ci yana me duba wayar shi. Faisal ya gani a online ya tura mishi.
Hi! Kana aiki ne?
Aikin uwar me zan yi a wannan daren ?
Tab’e baki yayi sannan ya tura mishi.
Ai sorry Ya Madam?
Madam gata nan sai kukan banza take min tunda taji kayan aikina
Allah ya kyauta kayi a hankali dai kasan masu karamin ciki basu son takura dan sai ka aikata abinda zai saka ta tsane ka
Wallahi kuwa! Amma Bilal matar da kake masifar so baka gajiya da ita amma karka damu akwai lokaci ka kwanta kaji
Shiru yayi yana nazarin abinda Faisal ya gaya mishi, duk matan shi da ya aura babu wacce yake takurawa da yawan kwanciyar aure kamar Muneebah, domin tana da wani irin yanayi ne, bai sani ba amma yana da yakinin zuwan su Korea bayan auren su ta koma haka me dadin al’amari a rayuwar aure.
Haka ya taba abincin karshe ya koma daki ya kwanta, bayan yayi brush. Dan nazarin da yayi da hiran su da Faisal ya ɗan sauya mishi mood din shi, wanda yake matuƙar buktar mace a wannan daren, kuma shi ba wai kowacce ba. Yarinyar nan ta kasar paris yake bukata, ita din dai take son jin yanayin jikinta. Dan haka ya tashi ya bude drower din shi ya ciro roban maganin shi ya hà diye yayi ya kora da ruwan da yake gefen gadon a gora.
 Sai da ya kwashe minti talatin kafin ta ji ya fara zufa, dan haka ya kwanta yana ajiyar zuciya. Kafin nan ya yayi addu’a tare da kauda duk wani tunani a ran shi. Tuni barci yayi gaba da shi.
**
A bangare na kuwa tunanin Matar da aka ce na mata wani abu na kwana, idan na tuna marina da wannan matar tayi ji nake kamar ba zan kwana a raye ba, dan haka kasa barci nayi har kusan daya na dare, kafin shima wancan mara mutunci ya fado min a rai,tsaki nayi tare da gyara kwanciyata.
“Da ban karya hannun ki ba shine babban kuskure na, amma da na karya zan ga da wanda zaki kuma dukar mutum.”
   Tsaki nayi tare da juyar da kaina, har barci yayi gaba da ni. Koda gari ya waye baki daya sai naji zaman gidan ya gundure ni, wajen sha daya na rana ba shirya na fita, ban tsaya ba sai gidan matar nan na samu gidan a bude, cikin tsannanin tsoron abinda zai biyo baya na shiga gidan babu kowa, sai matar tana kallon kofar falon. Kunya ce ta kama ni.
“Kiyi hakuri! Na shigo babu wata alamar nazo, ya gida ya kuma jikin ki Yarinyar ki ta zo. .. a’a ta min magana akan ban kyauta ba so that shine na zo baki hakuri.”
Na durkusa kasa tare da hade hannuna.
“Waye ya gaya miki nayi shiru ne, saboda ina jin kamar nesa tazo kusa ne. Kina da kyau me yasa baki daura dan kwali? Ga gashin ki ma baki gyarawa,me yasa kika dauki lokaci a haka?” Murmushi nayi ina shafa crazy hair dina na ce mata.
“Ina son shi ne haka, sabida yanayi da na yan Ethiopia ne”
   Shiru tayi tana kallona, karar wayata yasani mikewa dan yana cikin Aljuhun wandon jikina na dauko Yar karama ce toh. Kallon wayar nayi ban san number ba, kamar ba zan dauka ba, na dauka tare da sakawa a kunne.
“Gani a gidan ku nazo Ance kin fita.”
   “Eh amma kayi hakuri nayi nisa ne,ka dawo irin karfe bakwai din nan” na fada ina kashe wayar.
Kallon hannunta nayi tare da ganin farcen ta, yau ban zo da side bag dina ba. Mikewa nayi na ce mata.
“Bari na dan fita shago” ina fita ba sayo reza, na koma gidan. Zama nayi ba gyara mata farcenta, ina jin kamar kewar da nake ji yau ya kare, har na gama kallona take tana murmushi.
  “Mama na gama, zan tafi gida.” Na gaya mata.
“Toh ina zuwa zauna.” Ta nuna min wuri, cikin dakinta ta shiga can sai gata da jaka, har da wasu kaya a wani jaka. Mayafi ta cire ta nad’e min kaina. Tana murmushi.
“Kin fi kyau da mayafin nan ki daina yawo babu mayafi shima kamar kariya ce ga Y’a mace ki gaida min iyayen ki!” D’ago kai nayi ina yar dariya.
“Zasu ji” na faÉ—a, tare da barin falon ina godiya. Sai da nayi tafiyar kafa sannan na samu abin hawa, muka nufi gida.
…
Karfe hudu na yamma Wasilah da Rahmah suka shigo gidan, hango Ammyn suka yi a kan abin sallah.
Da sauri wasilah ta shige kitchen.
“Ina ga kawai ki dawo lagos kawai domin nima ina jin MD yana cewa anan zan yi IT na.” Inji Rahmah.
“Kai haba? Keda Abuja sai bayan kin haihu ma wow” ta fada tana kunna gas. Ta shiga kokarin daura abincin rana, dan ma suna da miya dan haka aikin bai bata wahala ko daukar lokaci ba, tana gamawa ta shiga cikin falon ta samu Ammyn da Rahmah suna hira sama sama.
“Ina Ummin ku?”
“Ummin ra tafi ganin likita a korea”
“Allah ya dawo da ita lafiya”
“Amin Ya Allah!” Ta fada tana me kwanciya a cinyar Ammyn.
“Sauka akan cinyata, me a cinyar tana nan zuwa ba zaku rage mata dumin shi ba”
“Wayyo Ammyn don Allah bari na danna cinyar”
Haka tayi ta mita har Wasilah ta kawo abincin suka ci.
“Ammyn Ina Ya Jamilah? Ba hannun ta yana ciwo ba?”
“Eh amma ta tafi gyaran gashi”
“Wannan yawon dai yayi yawa, sai kace mara mafadi”inji Wasilah,ita kan Ammyn bata yi magana ba asalima shiru tayi tana kallon su. Yadda Wasilah take Masifar kamar Jamilah tana wurin.
Har zuwa dare Kafin Faisal yazo daukar Rahmah, sai lokacin Jamilah ta dawo, ganin yadda Rahmah take tafiya a hankali shi kuma yana mata sannun cikin so da kulawa.
“Dan uwa Faisal. Dan bari nayi magana da ita mana.” Wucewa mota yayi tare da cewa.
“Ok”
Yana wuce su ta kalli Rahmah, kafin tayi dariya.
“Kin zata son ki yake? Eh toh bayan ya samu abinda yake bukata zai lallaba yayi maneji dake…” Bata kai karshen maganar ba, Rahmah ta wanke ta da mari.
“Ƙarki sake kiyi mention din sunan Faisal Abdul Hadi Shema,a cikin abinda bai sani ba, domin zan iya watsar miki da hakoranki dakikiyar Æ™waÆ™walwar ki bata gaya miki gaskiya” ta saka kai zata wuce.
“Abin dariya mijin ki dai bin mata yake kuma idan kina ganin karya ne, ki duba Whatsp na Turo Miki evidance, sannan uwa Uba. Idan ya gama amfani dake zai watsar ta dauko wacce take da kome a kanta infact ma jinin ki yake yawo a jikinta.” Cikin fushi ta juya aikuwa ta kauce tana mata dariya.