NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

“Koda wasa ba zan lamunci duka ba”  ta fada tana mata dariya kamar zata zauce. Shi kam yana cikin mota yana waya da Rubi, bai san wainar da ake toyawa ba, sai da ta shiga taji yana cewa.
“Ke dalla can sai baki hakuri nake, bani nace ki dawo ba? Kuma wallahi idan baki dawo ba kika sake nazo inda kike zan baki mamaki kin san halina kowa? Toh wallahi ki zo gobe na ce miki.”

Cikin narkakken murya ta ce mishi.
“Wallahi ba zan zo ba, nazo wancan ne me kama da bishiyar dogon yaron ya saka yan sanda Kamani. Kawai na daina aiki a kamfanin ku”

“Oh Allah toh gobe wallahi idan baki zo ba..” fisge wayar Rahmah tayi cikin fushi ta ce mata.
“Dan Ubanki karki zo inda Mijina yake domin wallahi sai na kashe ki” wurga mishi wayar tayi tare da fita daga motar duk yadda yaso su koma gida fir taki,  haka Ammyn ta saka baki amma ta fashe da kuka tana rike cikin ta, dan dole ya hakura. Jamilah jan dariya har da kwanciya a Æ™asa.

    …
Sake baki nayi ina mamakin wannan yanayin da nake fuskanta a wurin mutanen nan sam basu da mutunci, kashe wayar nayi ba kwanta.
“Allah sai naje office din sai dai ku mutu amma zuwa dole ce a gare ni….

🔥🔥🔥🔥

Yaran Ammyn sun kama da Wuta….
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/7/22, 12:47 – Nuriyyat: 61

Washi gari.

Kamar Faisal ya sani ya fara zuwa gidan Ammyn,a nan ya karya.  Tare da rarrashin Rahmah,har Ammyn ta saka baki. Baki daya taki magana dan ta rantse sai ta ci Uban yarinyar da take waya da mijinta.

“Muje na kai ki asibitin,tunda baki jin dadin jikin ki” ya fada cikin lallashi.
“A’a kayi tafiyar ka ba zani ba” riko hannun ta yayi yana kallon ta. Ita kuwa fir taki kallon shi.
“Kin ga koyi hakuri mana, wallahi babu abinda ya hadani da ita kawai taimakon ta nake saboda kamar da kuke da ita, amma wallahi babu abinda yake tsakanin mu”

    Kallon shi tayi a sace duk ya wani sukurkuce.
“Nace ya wuce kaje idan ka tashi kazo ka mu koma gida”

“Nagode Lovely”
Murmushi tayi mishi, har ya tashi ta karaka shi ya bar gidan, bayan fitar shi ne ta zauna tayi ta kuka. Kafin Jamilah tazo fita.
“Cow girl kin zata yana sonki ne? Koda yake nasan yanzun haka yana can…”
“Munafuka algunguma, wallahi kin yi asara ke bayi auren ba bari ki kashe mata nata auren Ya Jamilah kiji tsoron Allah munafuka kawai, ke kuma zauna tayi ta gaya miki maganar banza akan karya mijin ki da yana niman mata wallhi ke baki isa ya ajiye ki a matsayin mace ba, dube ki har kina kuka akan mutumin da ya iya hakuri domin ki yi karatu banza irin ku.wallahi sai na zabga miki mari idan kika yi magana banzaye mutanen wofi” sake suka yi da baki suna kallonta domin basu zata zata iya musu fada ba, sannan ta kalli Jamilah da bakinta yake motsi ta ce yayi magna ya gani idan bata mata mugun duka ba. Dan dole tayi shiru tana kallon su. Kafin ya fita Allah ya sani tana Masifar tsoron Wasilah sai yarinyar da ta targada mata yatsa.

   Fita tayi tana sauke ajiyar zuciya, idan da zaka tambaye ta, Meye yan uwan ta suka mata bata da amsa domin Ita dai ba wani abu suka mata ba, kawai ta tsani ya bude Idanu taga suna farin cikin ita kuma tana rayuwa da kunci, baki daya gani take kamar suna jin dadin halin da take ciki ne, shi yasa take tsanar su. A da can kafin Rahmah tayi aure tare suke da Ita, amma tunda tayi aure ta koma hidimarta da wasilah bata damu da ita ba, bata damu da jin wani hali take ciki ba. Haka ma Wasilah ta masifar rena ta,ba halin tayi abu zata shiga mata rashin kunya wannan sune abinda yake mata ciwo yasa itama sai ta huce haushin ta akan Rahmah,kuma Ammyn tana ganin duk abinda zasu mata bata magana haka ya kara mata tsanar yan uwan ta sosai.

   Bayan tafiyar ta Wasilah ta cewa Rahmah.
“Dama ita ce take son ki kashe auren ki lallai na yarda baki da hankali, ok ba damuwa kashe auren idan dan sabida Jamilah zaki kashe kan ki ko a jikinta domin rayuwar ta zata cigaba. Aikin gani ta d’aga miki hankali tayi tafiyarta. Idan yaso ki mutu ma she don’t care. Ai ko da gaya miki tayi Faisal bai kaunarki Æ™aryatatta zaki yi ina zaki kai cikin jikin ki? Kina da Uban da ya wuce na cikin jikin ki ne? Gaskiya baki da hankali baki daya nayi nan ki zauna kiyi ta kuka karki koyi fada domin kwace kan ki”

  Tana gama fadar haka tayi ficewar ta,zuwa cikin gidan. Domin ba zata iya da kayan haushi ba.

**
Da wuri na tashi nayi kome na, dan haka ina gamawa na nufi kamfanin. Ina isa tun a bakin kofar shiga ake gaishe ni. Ina shiga cikin kamfanin kamar na shekara bana nan, wani rungume ni, suka yi tare da d’aga ni sama.
“Oyoyo little Queen ta dawo, Barka da dawowa gaskiya jiya mun yi bakin ciki dan ko babu kome mun shiga wani hali.” Inji Kamilah.

   “Zo muje ki duba min computer na, yana bani matsala.” Inji Baba Tunde.
“Kai Baba Tunde daga zuwa na, wale duba mishi, ina da aiki” na fada ina dariya.
“Wallahi ba zan duba min ba kece zaki duba”  buga kafa nayi a kasa tare da nufar computer din na fara aikin shi.
“Tunde she look sexy?” Cak na tsaya tare da juyawowa ina kallon shi.
“Bola kasan me? A ina kankantar shekaruna nasan ciwon kaina, idan ka Kum kallona ka fadi abinda yake mind dinka sai na maka rashin mutunci”

“Ba a kamfanin nan ba.” Inji Matar da ta mare ni.  Kallon ta nayi na cigaba da zuba mishi kashedi.
“Na gaya maka wannan ya zama na farko da na karshe idan ba haka ba zan daki wadancan garden Eggs din” na fada ina kallon shi cikin Idanu.

   “Ke Yar gidan Uban waye a lagos” kallon ta nayi sannan na wuce abuna,ganin  nufi dakin hutun ta biyo ne.
“Waye ya baki ikon shiga cikin shi?”
“Ni ne?” Inji Yallabai Faisal, da yake shigowa.
“Good morning Sir”
“Morning Rubi,ki gama da wuri ki same ni a office dina.”

     “Ok sir” na fada bayan na shiga lambun muka barta a wurin a tsaye, cire mayafin nayi dama riga jikina wrape gown ce, maroon colour sai mayafin da matar ta bani na yafa akai.

Ina aiki ina kallon wayata da na kunna gidan Radio, ina bin wakar da aka saka. Aikuwa nayi dacen sun daka wakar Di’ja, ina son wakarta sosai. Dan haka. Ina cikin bin wakar naji an bankado kofar. Da sauri na juya. Ganin shi bai sa na fasa abinda nake yi ba sai juyawa da nayi ina wakar.

“Zo ki fita” juyawa nayi na Kalle shi, tab’e baki nayi tare da É—aukar jakata na makala mayafina.

“Daga yau kar na kuma ganin ki anan?” D’ago kai nayi na Kalle shi na wani lokaci kafin nace mishi.
“Ta kwana gidan sauki” na fita ina yar waka ta ran shi ya É“aci domin baki daya yana ganin Faisal ya kawo mishi damuwa ne kamfanin shi.

Ina fita na wuce wurin su Baba Tunde muka buÉ—e dandalin hira, ashe ina fita ya wuce office din Faisal ne.
“Kazo ka kore ta, domin wallahi ba zan bata kwandalar ta ba”

“Baka da hannu ne? Ka kore ta mana, ba sai Lallai ni ba.” Ya fada yana aikin shi. Haka yayi ta mita da kananun magana.
“Sai na kore ta idan tayi fada da wani wallahi” sai ka jira tayi fadar ko?”
Fuuu ya bar office din, yana mita.

   .. aikan abincin yan office din na amsa, har na kawo musu na hango yallabai Faisal suna magana, shiga nayi na bi kowani table ina ajiye musu.
“Rubi idan kin gama kizo” ya fada min..
“Toh”  ina gamawa na nufi office din shi, ina shiga na same shi da Matar nan.
“Zauna.”
Zama nayi ina kallon shi.
“Tazo baki hakuri ne. Idan kun gama zoki duba min computer ta na”
“Kiyi hakuri da abinda ya faru, kuskuren fahimta ne.”
“Babu kome, ka juyo min computer na gani.” Juyar min da computer yayi  bana gani.
“Ok kizo nan mana”. Ya fada min, wallahi babu kome a raina domin ni kallon Yaya nake mishi, na nufi wurin na fara aikin,matsa min yayi yana waya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button