WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
 Jamilah kuwa daukar su hoto take, musamman yadda suke a wurin, ta turawa Rahmah. Ina gama abinda nake na ce mishi.
“Yallabai ana Æ™oÆ™arin tracking din kamfanin ku, kuna ta wasa da haka idan aka so a cikin awa ashirin da hudu za a durkusar da ku. Don Allah ku mai da hankali akan na’uran ku” ma fita, har waje dan ban tsaya hankalina yana kan waya ta. Ina fita na wuce shagon Abincin mu, ina shiga
.
“A xubo min amala miyar oyodu.” Na nemi wurina zauna, aka kawo min naci na koshi. Sannan na tashi na nufi wurin Hajiya muka gaisa ina tsokanar Natasha. Ina fitowa na nufi cikin kamfanin, ina shiga naji ana tambayar wata.
“Ina Rubi?”Â
“Gani nan!”
Kawai sai ganin hannun ta nayi zata mare ni, na rike tare da juyar da ita, bayan ta yana kirjina, na murde hannun ta. Wani mashin naga me shi yasaka hilmet, wuka ce a hannun shi kuma ita yake hari ban san ya akayi ba kawai na tsinci kaina da juyar da ita ne, sai jin wukar nayi a gefen cikina.
“Ahhhhaa!” Na sauke ajiyar zuciya, wannan ne karo na farko da aka soke ni da wuka. Kallon ta nayi lokacin da ake kokarin tare mutumin, zama nayi a hankali.
“Wayyo Allah Jini” ta fada da Æ™arfi. Lashe bakina nayi ina kallon ta.
“Rahmahhhh” kallon shi nayi bayan na Kalle ta. Zare nayi sakamakon hango mutumin yana kokarin haura katangar kamfanin na tashi ina dafe cikin na wurga mishi sai da ya samu shi a bayan shi. Ji nayi an kifa min mari.
Tare da riko wuyata.
“Dan Ubanki kin so a kashe min Yar uwa ce da cikin ta?”
“Kin ga wallahi ban san kome ba,kuma ba dan Allah ya kare ba ita zai samu.” Na fada ina kokarin tsayuwa.
Yana kallon abinda ya faru a cikin CCtv camera da yake office din shi,hankalin Faisal yana kan matar shi. Fita yayi a karon farko da yake da yakinin itace ta taimaka mishi, bama yakinin bane ita cin ce!
Wacece ita? Me yasa take bawa kamfanin shi da shi kan shi kariya? Me yasa ta zabi kyautattawa sama da bakantawa? Bai dame ba shi amsa haka yasa shi fitowa da sassarfa.
Koda ya fito ya samu Jamilah tana mata mugun duka, gashi jini nake zubdawa. Yana fitowa ya cire hannun ta a jikina. Kai hannun shi yayi ya dauke ni cak ganin haka Khalil ya bude motar shi ya sani a cikin gidan baya.
“Muje asibitin JF” babu musu ya shiga jan motar, shima Faisal motar shi ya kai Rahmah suka rufa mana, sai da suka shiga motar ya fara kokarin niman dalilin zuwan ta.
Aikuwa bai kuma magana ba, ya cigaba da tuki, asibitin ya kaita aka duba ta, sannan ya dawo da ita gidan Ammyn.
“Idan zan kara aure kin isa ki hanani ne? Ko idan mace zan nemi mace zaki hanani ne? Wallahi kin bani kunya kin bani mamaki da har Jamilah zata tura miki hoton mu ki zata zan iya cin amanar ki. Tun kafin na ganki ban bi mata ba,kuma har yau da nake tare da ke bana jin akwai macen da ta kai ki quality a rayuwata, amma haka kika watsa min kasa a ido kika tsaya zaki yi fada da ita, domin ta ceci rayuwarki shine ta saka nata a hatsari dame zaki biya ta? Kallon da nake mata wallahi kallon kanwarki Rabi’ah nake mata, ban san hotonta ba, amma idan tana wani abu gani nake kamar ke da Wasilah ne a gaba na, idan tana magana tunanina kan Ammyn yake. Kin zo kina kokarin dukar ta, idan wani abu ya same ta auren ki zai taba ba wani abu ba,fitar min a mota.”
Wani irin kuka ta sake mishi,baki daya sai tsintar kan shi yayi tare da rike hannun ta.
“Why? Baki yarda da nagartar da take tare dani bane? Ko kin ji na tab’a baki labarin ina da budurwa? Kece farko kuma kece karshe ko baki yarda bane? Ina sonki ba irin so na a boye nan ba, ina son ki da gasken gaske. Kije ki kwanta zan zo an jima.” Haka ta fita tana kuka, baki daya ran shi yana kara É“aci.
Asibitin kuwa Da kan shi ya dauke ni, lokacin har na suma. Yana shiga dani, suka shiga kokarin cire min rigar jikina.
“Karku cire iya wurin da aka soka mata zaku yanka.” Ya fada yana kallon su, sanin waye shi yasa suka yi yadda ya ce,sannan duka shi
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
Mai_Dambu
3/7/22, 12:48 – Nuriyyat: 62
Ruwan da yake hannun ta ya fadi sakamakon labarin da Rahmah take bawa Wasilah.
“Wai me yasa Faisal bai sake ki ,ki auri Jamilah ba? Banza dakikiya kin kashe musu yar mutane wallahi sai na kare hakkin ta tunda kun zama jahilai marasa kan gado.” Wasilah ta gaya mata magana son ranta sannan ta bar ta a wurin, jikin Ammyn ne ya dauki rawa.
“Rahmah me ya faru?”
“Wata yarinya ce take bin Faisal shine Ya Jamilah ta turo min hotonsu.” Nan ta gaya mata abinda ya faru, wani irin sanyin jikin Ammyn yayi Masifar yi, kallon Rahmah tayi tare da cewa.
“Kuma kika biye mata? Kika tab’a yar mutane? Allah ya ganar daku baki daya”
**
A can asibitin kuwa a Haukace Faisal ya shiga emergency yana me niman Bilal, can ya hango shi yana goge jikin shi musamman rigar shi da ya b’aci da jini. Da sauri ya karaso wurin shi.
“Ya jikinta?”
Tab’e baki yayi kafin ya dauki Jacket din shi yana faÉ—in.
“Tana ciki” yayi gaba abinshi yana tasbihi a ran shi. Yana jin wani irin bugun da zuciyar shi take. Har ya shiga motar Khalil ya ja shi.
 Anan Faisal ya zauna har aka fito da ita, ganin yadda take barcin wahala yasa shi sauke ajiyar zuciya. Kafin likitan ya kalli Faisal.
“Ana bukatar jinin da za a kara mata,dake aikin gaggawa ne yasa bamu fada ba, muna da wani extra muka saka mata,aka yi aikin da shi yanzu kuma tana bukatar kari kamar leda biyu”
  “Ok a gwana nawa mana” inji Faisal,
“Sister Kubrah kai shi lab a gwada…”
“Sai dai ya je office din ka ya Zauna, baka san waye shi ne? Shi din babban lauya ne na JF Groups da Hospital baki É—aya” inji Namir da ya shigo asibitin.
“Namir” Faisal ya kira shi, murmushi suka sakarwa juna, sannan suka wuce office din Namir, Anan aka zo aka gwada jinin shi aka fita, can sai gashi ta kuma dawowa lokacin suna hira da Namir.
“Sir jinin ka A+ ne kuma ita majinyacinyar jinin ta O+ ne?”
Dafe goshinsa yayi tare da kallon Namir ya ce mishi.
“Bilal ne kawai zai bata ba?”
“Eh wallahi mara mutunci yayi gaba abin shi bari na tab’a shi” a hankali ya tab’a wayar ya saka a kunnen shi.
“Kazo ana bukatar jinin ka”
“Ni bawan ku ne?”
“Ok bari na nemi ko na wani irin mutum a saka mata, tunda haka mutane suka b’aci da rashin tsoron Allah”
Kashe wayar yayi, suka ci-gaba da hiran su, har zuwa awa daya babu Bilal babu alamar shi, sai da ya je dakin yagan shi a zaune kafa daya akan daya, yana cikin abincin. Ko kallon Inda Faisal yake bai kalla ba. Ya cigaba da cin abincin shi. Ganin jinin da yake sauka a jikin ta.
  “Dan iska kawai kasan kazo amma ka zauna anan.” Inji Faisal yana hararan shi, bai da lokacin sa ma baki daya sai da ya gama cin abincin sannan ya mike yana kallon ta.
“Ka kula da mutanen da kake saka damuwa kan su, suna sane da wani abu kawai zasu iya kome dan su rayu ne.”
 Ya kuma kallon gadon, yana me daukar ƙatuwar sweater coat brown colour, ya daura akan wata sleever shirt da black jeans din jikin shi, ita kanta rigar har zuwa wuya ce irin highneck din nan ce ta maza, yayi mishi mugun kyau, ya daura rigar sanyin akai, sak ya fito kamar dan garin su Maman shi. Ya fita a hankali.