WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
 “Yaushe zaki dawo? Baki san ana jiranki ba?” Juyawa nayi naga matar nan, a hankali na nufe amma Y’arta nan ta ture ni, haka ina ji ina gani na hakura da zuwa wurin ta. Farkawa nayi naga garin yayi duhu.
“Ashe nayi barci haka?” Na tambayi kaina, kafin na shiga ban daki nayi wanka ma sauya kaya marasa nauyi na fito, muka ci abinci.
Abin da ya faru kuwa, Alman ne aka tura su Afghanistan daga United State. Garin taimakon gaggawa yan yakin altaliban suka kai musu hari shine suna fada tsakanin wasu yankuna da yan ta’addan suke, baki daya an rasa samun shi. Daga nan sojojin nato suka tura abin headquarter din na new York. Su kuma suka tuntubi Bilal.
 Abin tausayi babu wanda ya sani sai shi Bilal din ko Faisal bai gayawa ba. Haka ya tafi United State. Daga nan suka wuce Afghanistan. Duk da an nuna mishi wurin da hatsarin wurin amma ya kafe ya dage sai ya tafi. Sun samu shiga yankin a ta mota, amma bai samu damar inda Alman din yake ba, sai da ya kwana ya wuni. Kafin ya iso wani karamin gari me dan ruwa a ga bakin garin anan aka nuna mishi inda jirgin ya fadi. Shima dalilin da yasa aka nuna mishi ya kwana ya wuni yana sallah gashi ya sake da mutanen gari. Koda ya tambaya nuna mishi wurin aka yi me É—auke da yan ta’addan.
     “Yaro karka shiga wurin, idan ka shiga kashe ka zasu.”
“Ya zan yi? Kanina ne a hannun su zan cigaba da ganin shi a hannun su? Zan tafi koda zan mutu ne!” Wayar shi ta ciro a hankali ya kira Umma sai da suka yi magana da kowa kafin ya ce mata.
“Ina yar kiriniyar ki? Umma ki kula da ita idan ban dawo ba, ki saka Faisal ya rike ta da amana.” A yau da xai shiga hatsari ita ya tuno, dan haka ya mikawa sojan da suke tare ta ce musu.
“Idan na fito a raye xan amsa da hannuna, idan gawa ta ce ko tabbatar ka mika ga mahaifiyata da shi yaron” yana gama fadar haka ya tsallaka tare da nufar sansanin yan ta’addan.
  “Kai ina zaka shiga?”
Suka tambaye shi,
“Nazo daukar Kanina ne da yake hannun ku”
“Baka da hankali ne?”
Sosa goshinsa yayi da yatsar shi kafin ya ce mishi.
“Yanzu xan tabbatar maka!” Ya shiga nufar cikin sansanin,
“Kai mahaukacin ina ne zan harbe ka fa?”
“Idan kana tantama harba mana” haka suna mishi barazana amma baki daya yayi biris da su, har ta tsallaka cikin su, jama’ar gari sai da suka razana domin wannan shine karon farko da aka tab’a samun haka. Yana shiga kuwa suka Mishi kawanya.
Suka shiga dukar shi, kamar Allah ya aiko su kan shi.
Sun dake shi idan suka tambaye shi.
“Meye kazo yi?”
“Kanina zaku bani,yana hannun ku” baki daya bashi wahala suka yi ta yi har sai da ya suma, ta farka suka watsa shi a filin wurin yana farkawa ya kuma mikewa.
A cikin tantin kuwa kallon shi Iman din su yayi ya ce musu.
“Idan kanin shine ya zo dauka ba zai sare ba sai mun bashi idan kuma wani abu ne ku kashe shi”
  “TOh Iman” haka suka fito aka cigaba da bashi wahala, sun mukar da har sai da ya fara aman jini, kafin suka kyale shi. Ganin yadda ya fadi suka ja shi har wani daki suna watsa shi.
  Sai da ya kwana ya wuni, sannan suka fito da shi.
“Zaka tafi ki ba zaka tafi ba”
“Babu inda zani sai da Kanina”
“Ku kawo min shi” suka ji muryan Iman din su, shiga da shi cikin dakin suka yi, yana tsaye suka daki kafar shi ta baya sai da ya durkusa. Wata Æ™atuwar wuka iman din ya dauka ya ce musu.
“Ku kawo min wuta”
“TOh”
Duk tsakar shi ta b’aci da jini,  wutar aka kawo, ya saka wukar a saman wutar, sai da yayi ja, ya ce.
“Ku cire mishi riga, Ya sunan Kanin ka?”
Yasan ko bai gaya mishi ba, babu fashi zasu azabtar da shi, dan haka ya ce mishi.
“Alman Abdul Hadi Shema, H040 sojar kasar Amurika”
” Amma kasan Bama ga maciji da America? Shine kuna musulmai kuke tura yaranku wurin su?”
“Wannan tsakanin ku ne, dan naku shiri bai zama dole muma mu riÆ™e haka ba, karatun soja ya tafi nan”
“Waye kai?”
“Bilal Ahmad Abbas Jikamshi”
“Wow kai kadai da suna haka,duba min background din shi muji ko ya fito daga ina haka” tar sai ga Information na Bilal.”
“Haba shi yasa kake da taurin kai, ashe akwai ruwan marasa imani a jikinka bari mu kashe babin ka”
“Idan haka ne na yarda, amma kanina da? Don Allah ka sake shi ta tafi Imam na yarda da kai kuma nasan kai Musulmin gaskiya ne, ba kana wannan al’amarin bane dan kanka halin rayuwar da aka jefa kune. Ka taimaka dan uwana ya isa gida mahaifiyar mu tana fama da Asthma kaji”
Daukar wukar yayi da ya dauki zafi ya shiga yankar fatar Kirjin Bilal da shi, wani irin ihu yake me cike da tashin hankalin, kafin ta fadi a sume, ruwan sanyin suka watsa mishi ta kuma farkawa, ya cigaba da yankar fatar shi, yana rubuta sunan Alman, sai da suka rubuta mishi sunan Alman a kirji. Sannan suka juyar da shi suka rubuta sunan shi a bayan shi.
“Ku Kai shi dakin duhu, idan ya rayu nan da kwana uku. Zai tafi da kanin shi amma ku sake tambayar shi me yazo yi”
Zunzurutun azaba tayi azaba, sai da suka saka mishi ruwa a jikin shi, ta bude idanun shi da suke gani dishi dishi.
“Me kazo yi?”
“Kanina nazo tafiya da shi”
“Yan uwantaka da dadi, ku tafi da shi”
**
Tunda Naji suna cikin tashin hankali, na kasa barci ko na saka hakarkarina, zan bude Idanu da sauri dan hakan,na sauya kaya. Na rufe kaina na nufi wani church da yake gaba damu, tunda ba shiga na tafi har gaban inda gumkin Jesus Christ. Zuba gwiwowina nayi a ƙasa. Na sake wani irin kuka. Ina shashekar
“Ya taimake ni, yana da uwa yana kanne, Yana da gobe me kyau Yesu Christ ya cancanci ya rayu. Maman shi tana kuka yan uwan shi suna kuka. ina rokon da a bar shi ya rayu mana.”
  Na cigaba da kuka, ina fatan rokon ba nake ya karbu. Haka na gama kukan na koma gida.
  Haka muka kwana babu labarin shi, next day ma, haka sai dinbun tashin hankali, ban tab’a sanin na shaku da shi ba, sai yanzun.
**
Afghanistan
Kallon Yaran yayi ya ce ” ina mutanen American?”
“Suna can dakin”
“A fito min da su”
“Toh Imam” haka aka fito da su. Aka kwantar da su.
“Ina Alman Abdul Hadi Shema” d’aga hannu yayi tare da cewa.
“Na’am”
“Waye Bilal Ahmad Abbas Jikamshi?”
Saka hannu yayi a bakin shi.
“Yaya na ne”
“Idan ya kai gobe zaku tafi da kai da abokan ka. Idan kuma ya mutu toh ba makawa mai É—aya zaka tafi da gawar shi” daga haka Iman din ya wuce aka mai da su dakin su.
Wasa wasa sai da Alman ya kasa zama kai ko abincin da ake saka musu bai ci ba. Yana zaune tun abokan shi suna farin cikin har suka koma gefe suna tausaya mishi, a hankali ya shiga basu labarin kan shi da kuma wanda ya zo daukar shi da girman shi da matsayin shi, yana kai aya yafashe da kuka domin ba makawa idan Bilal ta mutu a nan ba zai yafewa kan shi ba, balle sanin shi Family din su ba zasu yafe mishi ba, dan haka ya shiga kuka har xa shasheka.
 Har aka kira sallah asuba yana kuka, wurin karfe sha biyu na rana aka fito da su, kirjin shi da yasha zanen wuka ya kumbar sosai, sai yayi wani irin jan ruwa, kuma dan mugun ta suka dauki sweater coat din shi suka saja mishi. Kwara mishi wani irin sanyin suka yi sannan suka mare shi sai da ya farka.
“Me kazo yi nan?”
“Kanina nazo dauka!”
“Ba zaka gaya mana ba?”….
3/9/22, 16:49 – Nuriyyat: 65