WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
Cikin matsanancin wahala ya ce musu.
“Sau nawa xan gaya muku kanina kazo dauka? Ku kashe ni ya rayu” kallon Iman din suka yi tare da jiran abinda zai ce ya juya musu baya.
“Su bar nan cikin minti talatin, idan kuma suka kasa, ku buÉ—e musu wuta” Bilal yana jin haka, da gudu ya riko hannun Alman, tare da yiwa sauran sojojin alama su tawo, ai kuwa da mugun gudu suka fita daga sansanin.
“Saura minti nawa?” Ya tambayi Alman.
“Minti daya ya tafi”
“Maza mu bar nan” a cikin minti Ashirin da bakwai suka bar sansanin, suna shiga kauyen mutanen garin suka kawo mishi dauki. Sakamakon yadda jini yake zuba a raunin jikin shi.
“Sannun kaji Yaro, Allah ya baka ladan aikin da kayi.” Nan suka bashi sassanyar madarar saniya, ya sha sannan ya fara amai suka kuma hada magani, tunda ya sha bai kuma sanin inda kan shi yake ba.
“Idan kuka koma gida kar a bashi maganin asibiti sai dai na tt, sannan ga wannan maganin kana dama nashi a madara yana sha. Kayi farin ciki ka samu dan uwa na gari Abinda aka rasa a wannan lokacin kenan.”
 Haka suka ɗauke shi tare da tafiya shi wurin motar bai ma san waye akan shi.
Daga nan barikin sojan kasar Amurka aka tafi da shi, su kuma suka wuce da shi US. Kwanan shi uku babu abinda ake saka mishi sai ruwa, haka suka mika shi ga hukumar tsaro Korea, domin Daga nan America sun tuntubi Jakadar Korea anan din shi kuma ya mika kome aka tabbatar ya fito daga cikin babban gida ne, dan haka aka tafi dauko shi.
Bayan awa ashirin da hudu.
(24 hours)
Sun isa da shi babban asibitin koyarwa na Busan, ana aka shiga bashi kulawa dukda Alman yaso ya musu magana amma ya kyale su, domin yasan girma da matsayin Bilal din.
  Sai da aka b’ata tsawon kwana takwas, akan shi kafin ya fita a coma, domin sun fi zargin ya shiga din zunzurutun azabar da ta shige shi. Bana iya zuwa, domin tun da naje sau daya na gigice, shine kakan shi wai kar a kuma mai dani, sannan yadda ake bashi kulawa ya sani fahimtar wani abu kakan shi yana da mugun karfi a cikin foundation na asibitin domin kana shiga zaka ga katon hotunan kakan shi da wasu likitoci. A cikin wannan yanayin na tambayi Lin shi.
  Take gaya min ai kakan shi ne, board chairman na health care baki daya south Korea, shiru nayi ina kallon ta. Sannan ta ce min.
“Ko Seyo tana aiki ne da Mayor na garin nan, mahaifiyar shi ita ke rike d wasu manyan kamfanonin gwamnati, Kawun shi Baban Ha Na. Yana aiki ne a fadar shugaban kasan nan, suna da karfi a gwamnatin kasar nan. Dan haka babban al’amari ne haduwar ku. Domin daga cikin kasar nan kowa ya kagu yayi aure.”
“Ban gane ba?”
“Bari na miki bayani, kece wacce kika taimaka mishi lokacin da aka zo kashe shi ko? Sannan kin taimakawa Matar Faisal, sannan ana gab da durkusar da shi, a kamfanin shi kika tsaya sai da ya dawo wannan bayanin mun same shi ne daga shi Bilal din. Da kuma CCtv camera da yake hade da titin da suke kewaye da kamfanin shi”
  Wato a wannan zamanin har uwar hanjin ka, gani ake kawa cikin bagarawa nace mata.
“Bani na taimaka mishi ba” na wuce abina.
     Shiru nayi tunda na shiga daki, kafin na mike, na kuma fitowa. Asibitin na tafi da taimakon driver gidan. Shiga dakin da yake nayi yana kwance.
Zama bayi tare da kallon shi yana ta barci, tashi nayi na tsaya a kan shi. Kafin na shafa kan shi.
“Ka tashi haka? Gasu Umma da Kannen ka suna kuka. Nasan ba zaka mutu ba, domin kai din na musamman ne. Ka tashi domin akwai rigima na da kai wallahi” zuwa kusa da kunnen shi nayi na ce mishi.
“Idan ka tashi zan baka wani labari nayi saurayi kyakyawar nan da kuka tawo tare”
   Na fada Idanu na cike da kwalla, can na kama mishi kuka nake, ina jijjiga shi. Fita dani., Ai kuwa muna fita computers din shi suka fara kara, da gudu likitoci suka koma dakin aka fara duba shi, gwaje-gwajen da suke mishi, tare da farin cikin al’amar ya farka yasa aka gayawa mana, sai da suka gama, sannan suka bari aka shiga.
   Tunda aka shiga kowa ya damu, muna cikin wannan yanayin sai ganin Yallabai Faisal muka yi shi da matar shi, tare da Kanin shi nan. Komawa gefen Kanin nayi ina kallon shi tare da cewa.
“Barka kyakyawa.” Share ni yayi Matar Faisal ta ce min.
“Rubi” kallon ta nayi, sannan nace mata.
” Ya kike?”
“Lafiya lau” karasawa suka yi jikin gadon shi.
“Ya Bilal ya jikin ka”
“Da sauki sosai”
Ya fada a hankali, matsowa nayi nace mishi.
“Ya jikin ka Mr Jikamshi”
“Da sauki” ya fada min,
“Kayi karo da maza ko? Ai basu da mutunci.” Shiru dakin ya dauka.
“Kasan babban hatsarin da ka tusa kanka? Kasan yadda ka karya zukatan mutanen da suka dogara da kai? Idan da kasan kuskuren da ka aikata ba zaka so ka kuma yanke danyen hukunci irin haka ba. Kayi kokarin gyara al’amarin ka kasadar tayiwa.
     Kai kaji dadin ka, ni nawa ahalin ma ban san inda suke ba, ka tashi ka kai kanka cikin yan ta’addan da duniya take matukar tsoron motsin su. Ka kiyaye gaba karka kuma irin haka” daga haka na saka kai na fita shiru dakin ya dauka dake duk maganar da nake cikin turanci ne, shiru suka yi kuma kowa yaji me nake fada, a bakin kofar fita muka hadu da Jamilah.
“Happy to see you” murmushi na mata sannan na rab’a gefen ta zan wuce take min.
“Kin shiga jikin Bilal dayawa, bai gaya miki cewa mun yi dating juna ba?”
Murmushi nayi mata sannan nace mata.
“Bai gaya min ba gaskiya!”
“Iko shi din abincin ruhina ne, na jima da sallama mishi jikina baki daya”
  “Toh ina ruwana da haka? Ke ce a dame bani ba” domin ban ji nayi fada ba, asalima abinda take tunanin ba shine a tsakanin mu ba,
Kwafa tayi sannan ta wuce dakin, ina fita na wuce can wurin shan iskar asibitin na zauna, ina kallon yadda marasa lafiya suke yawon su.
…
“Bilal gaskiya Rubih ta fada maka, wannan kuskure ne, karka kuma aikata haka, domin akwai damuwa don Allah” inji Faisal, abin ya b’atawa Bilal rai dan haka yace musu.
“Idan zaku tafi ku tafi da ita na gaji zata kashe ni”
 Shiru suka Mishi, har Jamilah ta shago dakin sai kananun tsaki yake.
**
A bangaren guda kuwa Ni da Rahmah muna shiri ta sanadiyar ta muka fara mutunci da Alman, har muna fita. Tsawon kwanaki uku ban je asibiti ba, dan sun gaya min kar na je yana can yana jirana da tulin masifa, ni kuwa na shirya muka fita da Alman.
  —
“Faisal ina yarinyar nan?” Wacce yarinya kuwa, kunshe dariya Rahmah da NaNa suka yi.
“Mahaukaciya nan ma”
“Wacce fa, kasan mahaukatan dayawa”
“Rubi”
Ya fada a daidai lokacin da suka had’a Idanu da Jamilah.
“Ai tana gi..”
“Wani gida kuma? Ka gaya mishi gaskiya mana, suna tare da Kanin ka. Ai soyayya suke da Alman”
“Ya Jamilah” Rahmah ta kira sunanta cikin fushi.
“SOYAYYA?!!” Ya nanata kalmar.
“Kira min Alman” ya fada cikin fada,
“Maza kira min Alman sai na b’ata mishi rai”
Ita a tunanin ta haka zai saka ya rabu da Rubi, sai dai bata san sake hadewa hakan zai yi ba, a bangaren Mimih itama ta cika tum.
 “Bani wayar! Kai Alman ka dawo min da ita” ya fada a tsawace,. Nan ya shiga masifa kowa ma fadawa yake mishi, ai kuwa abokin cin mushen sa ya kunshe dariyar shi yana faÉ—in.
“Ayi hakuri kasan yarinya ce, shekaru sha shida, ai bata wani girma ba kawai jiki ne da ita ake ganin kamar ta kai wata shekaru”