BABU SO HAUSA NOVEL

AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

A falo ta zauna tanata doka sallama, jabeer ne yafito jikinsa sanye da jallabiya milk colour me gajeren hannu “A Nusaiba kece da wannan safiyar, “nice yaya ina kwana
“Lafiya lao.
“Gashi Mama tace akawomaku, kai amma mungode.

“Yaya ina auntyn tamu mu gaisa sauri nake zankoma na tsaida me napep, tana ciki bari na gayama, yafad’a tare da nufar d’akin baccin nasu.

Kwance ya isketa idanunta bud’e ba bacci takeba, “kizo ga Nusaiba nan tazo Mama ta aikota zaku gaisa wucewa zatayi,

Wani yamutsa fuska tayi “haba tunda safe kuma, nikam ba yanzu zan fitaba kawai kacemata tabari mun gaisa wani lokacin idan tazo.
“Sabodame bazaku gaisa yanzuba tunda tazo,
“Ni kawai fitarce yanzu banyi niyyaba kozan fitane saboda ‘kanwarka.
“A’a amma kinsan ba dad’i mutum yazo har inda kake kuma ya bu’kaci ku gaisa kice a’a.

Cikin fushi tatashi zaune tare da d’agamashi Hannu “dakata Malam nifa banison abinda kakemin ‘kanwatace dazakace dole saina fita mungaisa da ita da wannan safiyar, kaida take ‘kanwarka kaje kun gaisa to kace nace ta gaida gida, banison yawan magana tana kaiwa nan a zancenta takoma ta kwanta.

Love u all my Fan’s ????????????
[1/9, 9:14 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….22

Duk abinda suke fada kan kunne nusaiba saboda yanda Hussaina take d’aga murya, Haka jabeer yafito jiki a sanyaye cike da fara’a nusaiba ta kalleshi “Halan aunty tamu bata tashiba, idan tatashi a gaishemin da ita nizan wuce,
“Wani busasshen murmushi jabeer yayi dan yasan Nusaibar tajiyosu kawai dai basarwa tayi, “to shikenan Ki gaida Mama ga wannan ki sallami me napep d’in ya mi’kamata d’ari biyar guda tasa Hannu biyu ta kar6a tare dayin godiya sannan tafice a gidan.

Da misalin ‘karfe goma jabeer yafito cikin shiri, kafad’arsa rataye da jakar laptop, d’akin Husaina yanufa dan ganin kota tashi, wani babban abin takaici shine yanda yanda ya isketa kwance har yanzu kayan baccine jikinta, batada niyyar tashi.

‘Karasawa yayi gab da ita sannan yad’an bubbuga gadon, juyowa tayi ta kalleshi “lafiya Malam,? Ta tambaya cike da rainin wayo.
“Lafiya lao na shirayane zan fita, yakamata ace kintashi ga break fast can Mama ta kawomamu kiyi serving d’ina sauri nake zan fita office muna ayyuka dayawa gashi harnayi latti yafad’a yana kallon had’addiyar agogon dake d’aure jikin hannunsa.

‘Kara gyara kwanciyarta tayi tare da juyamai baya, “kaga Malam idan zakaje kayi break d’inka kawai kaje kayi dan naga Alamar yunwa kakeji ni ba yanzu zantashiba dan bansaba kalaci da wuriba.

“Yanzune da wuri kiduba kiga yanda rana ta fito…
“Kaga malam kaje kawai dan Allah banison hayaniya, tafad’a tare da jawo wayarta wacce takashe tun jiya ta kunna.
Message’s ne suka ri’ka rige-rigen shigowa, wanda yawancinsu duk jiyan akayoamatasu sakamakon jin wayarta kulle.

Jabeer kuwa falo yakoma ya bud’e kulolin wacce d’aya take d’auke da wainar shinkafa sai miyar alayyahu, sannan gudar kular dake d’auke da farfesun hanta, sai plask shikuma d’auke da kunun gyad’a Wanda yaji tsan-tsar madara yayi fari kal.

Zubawa jabeer yayi a gaggauce yaci sannan yazuba kunun gyad’ar duk da son dayakemashi wanda yasha befi Rabin cup ba saboda saurin dayake.

Jakarsa ya d’auka sannan yafice, Har yanzu Hussaina na d’aki tanajin lokacin dame gadi yabudemar get yafice sannan itakuma tafito.

Kulolin data gani ajiye tashiga bud’ewa, take taji tsohuwar yunwar data tara ta tasomata da sauri takoma d’aki tasheka wanka, tazo gaban mirror ta murza lotion da powder sai man le6e tasama lallausan le6enta sannan tanufi wadrope ta d’auko kaya riga da siket na atamfa tasaka, fitowa tayi tazuba wainar tacika cikinta sannan tabi da lafiyayyaen kunun gyad’a Wanda dad’insa saida ya ratsata har tsakiyar kanta, tana gamawa tami’ke takoma kan three seater ta kishingid’a batare data kauda kayan dataci abincin ba.

Wayarta tajawo tafara karanta text messages farko massage d’in Hafiz tafara karo dashi, inda yake cewa.
Haba babyna banyi tunanin akwai abinda zesa kirabu daniba, duk irin so da ‘kaunar danike nunamaki kin d’aukesu ‘karya kinje kin auri wani bayan kinriga kin dasamin bishiyar ‘kaunarki a zuciyata, kin yaudareni Kin cuceni kuma kinci amanata, wama yasani ko inmutu saboda ‘kaunarki, amma kisani idan har haka ta kasance Allah baze barkiba. Kihuta lafiya Hafiz

Tana gama karantawa wasu zafafan hawaye suka zubo a idanunta, tasa hannu ta goge, tana cewa “ina sonka Hafiz ina ‘kaunarka banta6a jin son wani namijiba a duniya bayan kai, ko yanzu ina tare dakai bazan gujekaba komin rintsi.

Sunanshi ta lalubo sannan ta danna kira bugu d’aya ya d’auka nan tashiga bashi ha’kuri “dan Allah kayi ha’kuri Hafiz wallahi ba yaudararka nayiba, har yanzu sonka yana cikin zuciyata ba abinda ya canja, kaine kaja Hafiz da farko na d’auka karabani da budurcina saida naba wani namiji kaina sannan na tabbatar dabahaka bane, kaja na mallamakama wani namiji kaina bakaiba.

“Kada ki damu babyna ni inasonki haka kuma zan iya kasancewa dake akowane hali kike, kedai kawai kicigaba da ‘kaunata kamar yanda nike ‘kaunarki.

“Kada kadamu babu wani namiji a zuciyata sai kai, tafad’a tana goge hawayen dake fuskarta, to shikenan yimin murmushinnan naki me sanyayamin zuciya, wani ‘kawataccen murmushi tasaki kamar Hafiz d’in yana gabanta, wani lafiyayyen kiss yasakarmata ta wayar Wanda yaratsa dukkan sassan jikinta, taji inama kawai taganta tare da Hafiz yanzu ya shayar da ita zumar ‘kaunarsa.

Love u all my Fan’s ???????? shoki ????????‍♀????
[1/11, 6:47 PM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….23

Da misalin ‘karfe hud’u na yamma me napep ya sauke Zuby ‘kofar gidan Hussaina, megadi tafara yima magana sannan ya bata izinin shigowa bayan yanemo hakan daga gurin matar gidan, da dallama zuby tashigo ‘kawataccen falon, mutuwar tsaye tayi saboda yanda falon yayi amasifar burgeta, batayi tunanin zata tarar da ‘kawarta cikin wannan daular ba tunda taga Auren ba cikin shiri akayishiba.

Hussaina ta katsemata tunaninta ta hanyar yimata “welcome my friend, tafad’a tare da kamo hannu Zuby ta xaunar da ita kan d’aya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun dake zagaye da makeken falon.

Bayan sun gaisa Hussaina ta gabatarma da zuby da ruwa da lemu, nan zuby ta zuba lemun tanasha amma duk hankalinta nakan yanda aka kashe dukiya aka ‘kawatama Hussaina d’akinta, nan take wani ‘kululun ba’kin ciki yazo ya tsayama Zuby a wuya, a zuciyarta tace “tabbas dole inyi yanda nayi na raba Hussaina da gidannan, idan bansamu Hafiz ya aureniba, zan dawoma jabeer, ‘karama jabeer d’in ai dan yafi Hafiz kamun kai da kamala, nasan idan har nayi nasarar rabashi da Hussaina nikuma zanyi yanda nayi ya aureni inyi zamana cikin jindad’i da farinciki nima inhuta da l’ikema yayan masu kud’i danikeyi, muddin idan nasamu nasarar auren jabeer zan mallakeshi kota halin ‘ka’ka sannan dukiyarsa sai yanda nayi da ita nima lokacin zan faso gari ‘ya’yan talakawa zasu ri’ka likemin kamar yanda a yanzu nake li’kema wasu……..
Wani shu’umin murmushi tayi dan lokacin har hangota takeyi zaune a wannan babban falon a matsayin matar gidan tad’ora kafa d’aya kan d’aya ga yan’aiki durkushe gabanta tana bada owk…. lol

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button