BABU SO HAUSA NOVEL

AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

Da dare bayan daddy yadawo daga gurin aiki, bayan yasamu labarin shigar da ‘karar da Hassana tayi, saboda duk illahirin garin ya d’auka Kowa Allah Allah yake gobe tayi suje kallo.

Momy yasamu zaune a falo ta buga uban tagumi, bayan tayimashi sannu da zuwa yake tambayarta “ina Hassana? “Tana d’akinta, momy tabashi amsa a ta’kaice, “kiramin ita, “to kawai tace ta mi’ke tanufi d’akin Hassana, Zaune ta isketa kan abin sallah da Qur’an a hannunta tana karantawa, domin samun nasara akan shari’ar daza’ayi gobe.

Da sallama Momy tashigo, bayan ta zauna gefen gado ta kalli Hassana “kizo daddynki na kiranki, “to ta amsa sannan tarufe Qur’an lokacin Momy ta dade da baro d’akin, a falo suka zauna itada Daddy suna jiran fitowar Hassana, daddy ya kalli Momy “anya yarinyar nan tana cikin Hayyacinta kuwa? “Saboda me kafad’i haka Alhj, saboda yanda ta shigar da ‘kara kotu gashi har ana shirin zama na farko gobe batare data nemi shawarar yin hakan ba,

Murmushi Momy tayi “ai Alhj aikin gama yagama,tunda taji zata iya sai mu barta mugani.
Fitowar Hassanace ta katse masu maganar dasukeyi, cikin ladabi tasamu guri ta zauna, sannan tayima Daddy sannu da zuwa.

Suduka shiru sukayi na tsawon minti biyu kafin daddy yafara magana, “Hassana munji abinda kika aikata, amma amatsayinmu na iyayenki yakamata ki shawarcemu kafin ki yanke shawarar, ita shari’a da kike gani sa6anin hankali ce, kuma idan baka iya kama 6arawoba sai 6arawo yakamaka.

‘Dagowa tayi ta kalli iyayen nata da fuskarta wacce Hawaye suka gama wankewa tace “dan Allah daddy da Momy ku gafarceni akan rashin shawartarku danayi, yanzu ba abinda nake bu’kata agareku sai addu’a inashaAllah naji ajikina nice da nasara, “To Allah ya bada sa’a “Ameen, ta amsa sannan ta kalli daddy, kuma dan Allah daddy ina Neman wata Alfarma agareku, “muna jinki daddy yafad’a, “inaso duk zaman daza’ayi a kotu yazama tare zamu tafi daku.
“InahaAllah zamuje Hassana kada ki damu kedai kije kiyita addu’a.

Nagode daddy, sannan ta kalli momynta Momy nagode, kuma inaso kuma ku tayani da addu’a.

Zuby kuwa tana zaune gidansu itada ‘kawayenta tana nunamasu d’inkunan data amso daga gurin d’inki, tana gayamasu ranar dazatasa kowane kaya, ‘kawayen nata kuwa ba abinda suke sai zuzutata suna yaba duk wani abu data fad’amasu ta tsara…

Ba zato ba tsammani kawai sai ganin yansanda sukayi gabansu, kusan su takwas mata hud’u maza hud’u,
Zumbur zuby tami’ke tsaye dan ba ‘karamin razana tayiba kad’an yarage tasaki fitsarin wando.

‘Daya daga cikin yansandan tace “zuby ko, munzo mutafi dakeU office d’inmu zaki amsa wasu tambayoyi.

Zuby ido ya raina fata zata fara masu gardama suka hankad’a ‘keyarta tanaji tana gani aka sata a mota ‘kawayenta kuwa duk sun fito sunyi cirko cirko, hakan yaba sauran yan unguwa damar tsayawa suma suna kallo, haka akaja motar zuby kuwa ba abinda take sai raba idanu.

Love u all my Fan’s ????????
[4/15, 6:55 PM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….52

Jabir zaune yahad’a hannuwansa duka biyu ya tallafi kumatunsa da alama yayi nisa cikin tunani, a zuciyarsa yana ganin gangancin Hassana da wannan mummunan hukuncin data yanke na maka zuby a kotu batare da tanada wata kwakkwarar shedaba.

mama ce tashigo hannunta d’auke da kula da plate ta ajiye gabansa sannan takoma ta bud’e d’an ‘karamin pridge d’inta ta d’auko ruwan pure water me sanyi guda biyu ta d’ora a plate takawo gabanshi ta ajiye, zama tayi d’an nesa dashi tare da zuba mashi idanu wani irin tausayinshi ya tsirga mata, tana matu’kar tausayama d’an nata shikuma haka Allah ya jarabeshi da rashin dacen mace tagari wacce duk wata harkallar da’ake ciki yanzu Itace sila, kuma gashi bata duniyar ma baki d’aya.

Wata nannauyan ajiyar zuciya tayi sannan takira sunanshi “jabeer… Firgigi yayi ya kalleta kamar Wanda yafarka daga bacci, sannan ya amsa “na’am mama.
“Tunanin me kakeyi haka? Ajiyar zuciya yayi sannan ya maida dubansa ga mahaifiyar tasa “mama Dole inyi tunani abubuwa da dama sun d’auremin kai nayi tunani nayi nazari amma ban hango wata kwakkwarar hujja da Hassana zata kai zuby ‘kara ba.

Shiru yad’an ratsa na kimanin mintuna biyu sannan mama ta sauke ajiyar zuciya “to Jabir yazamuyi da wannan Al’amari tunda sunriga sunyi ‘kara ai bakin al’kalami ya bushe mudai fatanmu Allah toni asirin koma waye ya aikata wannan mummunan aiki.
“Ameen jabeer ya amsa yana matukar jin ciwon abinda yafaru dashi arayuwa, sannan yajawo kular abinci yafara zubawa dan rabonsa da cin abincin kirki tun lokacin daya gane Hassana ba ita bace ainafin matarsa Hussaina.

Haka yafara cin abincin kamar yana cin magani badan yanajin dad’insaba Haka mama tatasashi gaba tana rarrashinsa har yad’anci da dama sannan yakora da ruwa me sanyi.

** ** **

A 6angaren Zuby kuwa tun anar da police suka angiza “keyarta Zuwa office d’insu suka shiga tuhumarta da tambayoyi amma fir ta ‘ke’kashe ‘kasa tace ita batasan kome game da kisan Hussaina ba. Haka yan sandan sukayi ta fama har suka gaji suka tattara kome suka ajiye suna jiran ranar daza’a fara gudanar da shari’ar a kotu.

kotu ????

‘Katon d’akin gudanar da shari’a yacika ma’kil da jama’a maza da mata yan kallo dakuma wad’anda shari’ar ta shafa. Zuby kuwa tana tsaye Inda ake ajiye wad’anda ake zargi a kotu, sai raba idanu takeyi, gefe ga d’ansandan dake tsare da ita,
yan kwanakin datayi a kulle har fatar jikinta tayi duhu sai ‘kuraje dasuka firfito a jikinta wad’anda suke nuna alamun tasha cizon sauro ga wata irin rama datayi

Guri d’aya kuma momy ce zaune Sai Hassana gefenta wacce tunda tashigo d’akin shari’ar take faman karanto duk wata addu’a datazo bakinta dan neman nasara gurin ubangiji.

Daddy shima suna zaune a kujerar gaba yayinda Jabir yake kujerar dake bayanshi,
Kotu tagama cika mutane an kaure da surutu kowa na fad’in albarkacin bakinsa, shigowar Al’kali yasa mutanen gurin yin shiru tare da mi’kewa, haka Al’kalin ya isa mazauninsa ya zauna sannan sauran jama’a suka zauna, wani littafi dake gaban Al’kalin ya bud’e yayi wasu yan rubuce-rubuce sannan yayi gyara murya yace “afara gabatar da ‘kara ta farko.

Me gabatarwa ya mike tare da wata takarda a hannunsa yafara karantawa kamar haka “shari’armu ta farko shine wacce Hassana mansir company take ‘karar ‘kawar yayarta Zubaida wacce akafi sani da zuby akan tana zarginta da kisan gillar da akayima ‘yar uwarta kuma abiyar Haihuwarta wato Hussaina mansir company, bayan yagama karantawa yakoma ya zauna.

Al’kali ya kalli Zuby yace kece Zubaida? Zuby ta gyad’a kai kamar ‘kadangarwa tace “Eh nice ya mai girma mai shari’a, Alkali yace kokinada lauya Wanda ze iya kareki tace “inadashi, nanma Al’kali yayi “yan rubuce-rubucensa sannan yace ina lauyan wanda ke ‘kara da kuma lauyan wacce ake ‘kara.

Lauyan Zuby ne yafara mikewa yafara gabatar da kanshi sannan lauyan Hassana shima yagabatar da kanshi.

Kuyi ha’kuri kufara da wannan inshaAllah kafin kome ya dai-daita, kuma inaso zanyi amfani da wannan dama inmi’ka dumbin godiyata ga masoyana a duk inda suke nagode da kulawar da kuka nuna agareni najina da kukayi kwana biyu shiru kuna ko’karin kirana dan jin lafiyata, banida bakin dazan godemaku sai dai ince Allah saka da Alkhairi ya’kara dan’kon zumunci
[4/17, 8:55 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button