BABU SO HAUSA NOVEL

AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

   *Bayan wata 2*

Shirye-shiryen biki ya kankama tsakanin 6angarori guda biyu, Maman jabeer hidima take sosai dan jin bikin take kamar shine tafarayi a rayuwa, kallo d’aya zakamata ka tabbatar da farinciki tattare da ita.

Momy kuwa dama wannan shine bikin dazatayi na farko dan lokacin bikin Hussaina ba’ayi wani shagaliba.

6angaren jabeer ango kuwa kullum cikin hidima yake dan yau saura sati bikin yariga yagama gayyatar duk wanda ze gayyata.

6angaren amarya kuwa wata ‘kawar Momy ce ta d’auketa tatafi da ita gidanta can akeyimata gyaran jiki na amare, tsawon sati biyu ana abu guda tundaga kan dilka halawa, da sauran nau’ikan gyaran jiki, sai ingantaccen tsimi me kyau wanda ke gyara mace kullum tajita cikin ni’ima.

Ana saura kwana bakwai d’aurin aure Hassana tadawo gida, da niyyar saura kwana biyu bikin zata koma ayimata gyaran gashi da lalle, wani sihirtaccen ‘kamshi ketashi daga Jikinta ga wani haske da santsi da fatarta ta’kara, dole ko mace ta kalleta takuma kallonta dan fuskarta har wani shek’i takeyi. Zaune take d’aki Momy tatasata gaba da wani tsimi da aka had’a na fruits tanaso ta shanye itakuma sai shatake tana 6ata fuska kamar zatayi amai, sotake Momy tabar d’akin ta ajiye.

Lokacin wayarta tayi ringing sunan Hubby tagani akan wayar, kasa d’agawa tayi tana kallon Momy.
Momy tace ki d’aga mana kinbar waya yana ringing, murmushi tayi sannan tace ina tunanin yazone dan munyi waya dashi yacemin gashinan zuwa yanzu.

Daure fuska Momy tayi minti goma nabaki kiyi ki dawo, ince nafad’amaki ya daina zuwa haka, idan kukayi ha’kuri sati d’aya yarage ami’ka mashi ke baki d’aya.

Cike dajin kunya Hassana ta d’auki wani madaidaicin hijab tasaka sannan tafita tsaye ta iskeshi jikin motarsa, batace yashigoba dan taji gargad’in Momy datace minti goma tabata, tana karasawa kusa dashi yaji wani sihirtaccen ‘kamshi yadaki hancinsa, ahankali yadago idanunsa yakai dubansa gareta, yasalam yafad’a tare da sauke wata ajiyar zuciya.
Jiyake kamar ya rungumeta yahad’ata da jikinsa yacigaba da sha’kar daddad’an kamshinta

“Sannu da zuwa tafad’a cikin sassanyar muryarta, kanta sadde tana kallon kasa, “yauwa sannu dai amarya, yakike ya kuma hidima?

Murmushi tayi “Hmm hidima ai tana wurinku angwaye, “haka kike gani koh, amma ni a tinanina biki ai na amare ne.

Murmushi kawai tayi dan bataso firar tasu tayi tsayi, shiru yad’an ratsa na yan mintuna sannan jabeer yace “dama zuwa nayi inji dame-dame kk bu’kata na hidima dan naga idan nayi shiru ke bazakice komeba.

Eh ai bana bu’katar kome dan bawani bidi’a za’ayi a bikinnamuba walima kawai zamuyi, tonaji amma baki bu’katar kome na walimar?
“Eh bana bu’katar kome dan momy tagama had’a mana kome.
“Lallai Allah sakama Momy da Alkhairi amma dukda haka ga wannan kirike gurinki koda zaki bu’kata bandir d’in yan d’ari biyar yami’kamata sannan sukayi bankwana yawuce tana d’aga mashi hannu harya ‘kule sannan takoma gida.

Love u all my Fan’s ????
[4/27, 3:01 PM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….59

Yau yakama saura kwana biyu d’aurin auren Hassana da jabeer, yau ne kuma taje akayimata had’add’en gyaran gashi, tare da zana mata flower me kyau a hannunta, wani sihirtaccen kyau tayi dan idan ka kalleta sau d’aya dole ka kara.

Washe gari ana gobe d’aurin aure ‘yan’uwa da abokan arziki da yan tsirarun ‘kawayen Hassana sun taru a harabar gidan, domin walimar da wa’azi da aka shirya.

Da misalin ‘karfe hud’u aka fara gabatar da wa’azin inda wata shahararriyar malama tayi nasiha kan zaman aure, amarya Hassana kuwa tasha kyau dan wata tsadaddiyar atamface Jikinta sai babban hijab data saka.

Da misalin ‘karfe shidda aka kammala wa’azi aka rufe taro da addu’a tare dayima amarya da ango fatan zama lafiya da samun zuri’a tagari.

Rana bata ‘karya inji masu iya magana, sai dai uwar d’iya taji kunya

Dandazon mutane manyan yan kasuwa da ‘kusoshin gwamnati ne tan’kam ‘kofar gidan Alhj mansir company, wad’anda suka halarci d’aurin auren Jabeer da Amaryarsa Hassana, wanda aka d’aura kan sadaki dubu hamsin.

Ansha shagalin biki taro yatashi lafiya, amarya ta tare gidanta mutane Kowa yanatasa Albarka.

** ** **

Bayan Wata takwas

Tunda tatashi take faman kuka kamar zata cire ranta, idanunta sun kumbura sunyi suntum sakamakon rashin baccin datake samu, kusan wata da watanni, kullum cikin damuwa take amma da alama damuwar tayau tafi ta kullum.

Wasu yansanda kusan su hudune suka tsaya kanta, d’aya daga cikinsu ya kwatsa mata tsawa da alama Hausa bata zauna Mashi a bakiba, “oya les go, jiki a sanyaye Zuby ta taso tabisu a mota aka sakata, saida akayi tafiya me nisa sannan suka tsaya gaban wani ‘katon get megedi yabud’e masu get suka shige, daga nan suka ajiye motar sannan sukayi tafiya me d’an nisa wacce tasadasu da wani d’aki Wanda anan suka iske wasu ‘kattin ba’ka’ken mutane tsai-tsaye sunata mazurai wani dogon bencine sai wata igiya ta zuro anyi kullin ‘zarge da ita dai-dai yanda kan mutum ze shiga.

Zuby na tsaye ta d’aga kai ta kalli gurin wasu zafafan hawaye suka sauko kan fuskarta, batayi ‘ko’karin gogewaba haka suka ri’ka zuba wasu nabin wasu. Wata mace daga cikin yansandan aka mi’koma wata ba’kar hula me zurfi tasaka kan zuby ciki bayan and’orata kan wannan dogon tebur, sannan aka sa’kalo kanta cikin wannan igiyar, wani ba’kin d’ansandan fuskarsa bako annuri yasa ‘kafa yature tebur d’in haka yaba igiyar damar tsuke wuyan zuby tayi sama da ita, saiga ‘kafafunta suna lilo tanata harbe-harbe kafin daga nan rai yayi halinsa.
Wannan shine ‘karshen muguwa Zuby maci amana, kuma yar ta’adda

Hafiz kuwa tun bayan da yabada sheda a kotu ya tattara yanashi-yanashi yakoma kaduna da zama, ya canja hali, yazama mutumin kirki kullum zaka sameshi yana istigifari, a haka Allah yahad’ashi da wata yarinya yar mutunci cikin ‘kan’kanin lokaci suka sasanta bayan wata biyu aka d’aura masu aure, suna zaune a unguwar dosa Kaduna.

** ** **

Ahankali take takawa saboda nauyin da cikinta yayimata, cikin wata shidda amma idan ka kalleta yanayin Girman cikin saika d’auka yayi wata tara,ga kumburi tana fama dashi,
kitchen tanufa dan sama masu abinda zasuci na rana.

Lokacin jabeer yayi horn megadi yabude masa get, gurin ajiye motoci yayi parking sannan yashigo gidan da sallama, shiru yaji kuma be ganta a faloba bedroom yanufa nanma bata nan, can yajiyo motsinta kitchen can yanufa isketa yayi tanata ha’kilon had’a musu jalouf din kus-kus harma ta kammala tana shirin d’aukowa takai kan dining, da sauri ya amshi kular hannunta, ya ajiye sannan ya rungomota jikinsa bayanta had’u da ‘kirjinsa sannan ya d’ora hannunsa kan ‘katon cikinta yana shafawa ahankali, “haba my sweet nafad’a maki baniso kina wahalar da kanki kina wahalarmin da baby, bari kigani, hannu yasa ya d’auki kular abincin yakai kan dinning table yadawo ta mi’ko mai plate yakai sannan yadawo tami’kamashi cup din fruit salad d’in data had’a yaji ‘kan’kara sai ra6a jikin jug din

Bayan sun kammala wannan da kanshi yahad’a mata ruwan wanka sannan yarakata har toilet, yana zaune harta gama wanka da kanshi yashafamata lotion me sanyi sannan ya d’uko mata wata doguwar riga me saukin nauyi ta sanya.
Kama hannunta yayi ya zaunar da ita bakin gado “ina zuwa bani minti goma yafad’a toilet yashiga yashe’ka wanka yafito ya murza lotion sannan yasaka wasu ‘kananan kaya riga ash marar hannu sai bakin wando three quarter, sannan yakama hannunta suna takawa ahankali kamar makaho da d’an jagora har kan dining.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button