BABU SO HAUSA NOVEL

AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

Yana fita Hassana tafashe da kuka tare da fad’awa jikin Momy “yanzu Momy me hakan ke nufi, daddy yana nufin yarabani da ‘yar’uwatane ko miye.

Kiyi ha’kuri hassana ba hakan yana nufin anrabaki da ita bane akwai dalilin dayasa Daddynku yahana muje amma ki ‘kara ha’kuri inshaAllah bada dad’ewaba ze barki kije, haka Momy tayita rarrashin Hassana tana kwantar mata da Hankali.

** ** **

Da misalin ‘karfe Hud’u na yamma Hussainace Zaune tanacin abinci jalouf d’in taliya tadafa da busashshen kifi, gefe kuma ga lemu tanaci tana korawa tana gamawa nan tabar sauran abincin tare da cup d’in datasha lemun, ringing d’in wayarta taji dake ma’kale jikin soket tana charge da sauri tatashi dan ta d’auko wayar tayi kwallo da kwalin lemun data rage Wanda ko rufeshi batayiba, nan yafad’i ya zube kan carpet amma bata damuba saurin Isa tayi ta d’auko wayar ganin sunan Hafiz yasa tayi saurin danna OK tare da karawa a kunne.
“Hellow dear
“Haba babyna wannan wace irin rayuwace, Hafiz yafad’a cikin zafi-zafi.
Ace kullum muna tare a waya sai inkiraki yakai sau biyar arana amma kwata-kwata kin’ki kiyi dubarar dazamu had’u, gaskiya nalura kinfara son wannan mijin naki nike haukan banza, idan hakane kawai kifad’amin ni inha’kura.
Yayi ‘kasa da murya kamar me shirin yin kuka “Amma idan kikamin haka kin yaudareni, tsakanina dake sai…. Be ‘karasa maganarsaba ta tsinke wayar sakamakon jin Alamar shigowar mutum datayi,

Nan jikinta yafara kyarma dan ance marar gaskiya ko cikin ruwa yayi ji6i,

Sanye take cikin wani matsiyacin wando pencil, tare da wata d’amammiyar riga wacce ta sakko har gwiwa, kanta tayi rolling da wani shararan gyale Wanda behana ka hango gashin attach d’inda ke kanta, ga wasu muggan takalmi masu tsini dake ‘kafarta. Zuby kenan ‘yar duniya Haya’kin taba

Tsayawa tayi bakin ‘kofar shigowa falon tana ‘kara ‘karema falon kallo, wani shu’umin murmushi tayi a zuciyarta tace “Allah kai damo ga harawa kobeciba yayi birgima, ma’ana idan nayi ‘ko’karin raba jabeer da Hussaina koda be aureniba zanja ra’ayinshi ko zaman bariki muyi nikuma lokacin zan samu damar kwashe duk wani Abu daya mallaka in’kara gaba.

Love u all my Fan’s ????. Oya sagem ????‍♂????????‍♀
[1/13, 9:56 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….25

Wannan shafin nakune masoyan wannan littafi
My Bestyn Nana, da kuma Ilham
nagode da kulawarku Allah bar zumunci

“Welcome ‘kawata ashe kece, Hussaina ta fafd’a tare da kamo hannunta ta Zaunar da ita kan kujera, Zuby tayi murmushi tace “wlh kuwa hanya ta biyo dani nace bara na le’ko mu gaisa,
“amma kin kyauta kuma naji dad’in zuwanki domin dama ina Neman shawararki dan kobakizoba dama zan kiraki a waya.

To ai gani nazo ‘kawata miye matsalarki?
Shiru Hussaina tayi kafin ta numfasa, “Zuby kinsan dai irin son danikema Hafiz kuma nagayamaki muna waya dashi, to halin da’ake yanzu kullum idan mukayi waya sai yanunamin tsananin 6acin ransa akan na’ki yarda muhad’u, nikuma a gaskiya ina tsoron Daddy, kuma nasan jabeer baze barniba, kuma kinga nan gidan mijinane bekamata inkawoshi nan ba.

Murmushi zuby tayi a zuciyarta tace “Anzo wurin, da wannan damar zanyi amafani inraba Hussaina da jabeer,
“haba ‘kawata wannan aiba matsala bace zuby tafad’a tana kallon Hussaina.
“Husaaina tace kamar ya ba matsalaba kinsan fa akwai igiyar auren wani akaina kuma nike tarayya da wani namiji ina ‘ko’karin had’uwa dashi kuma kice ba matsala bace.

Matsowa zuby tayi gab da Hussaina tare da kanga bakinta dai-dai kunnenta ta rad’amata wani magana. (wanda koni zee bansan me tafad’a mataba)

Suduka suka kyal-kyale da dariya tare da tafawa, Hussaina tace “Kai amma wannan shawarar tayi ‘kawata shiyasa koda yaushe nake alfahari dake, kinga idan nayi haka zanje gurin masoyina inyi ko kwana nawa nakeso batare da wata matsala ba.

Nan take ta d’auko wayarta takira Hafiz bugu d’aya yad’aga tun kafin yayi magana tarigashi “hellow my dear ka shirya tarbar babbar ba’kuwa gobe-gobe.
“Kai haba da gaske? Hafiz ya tambaya cike da farin ciki.
“Da gaske mana kuma idan nazo kwana biyu zanyima.
“Wow babyna amma naji dad’i kice intashi inyima gidana general cleaning saboda zuwanki,
Nan suka gama wayar zuby kuwa sai kallonta take tana wani shu’umin murmushi.
Kafin ta mi’ke “to ‘kawata nizan wuce kome kenan zamuyi waya, “to shikenan sai munyi wayar ko, har kusan get Hussaina tayima zuby rakiya, sannan tadawo.

Hussaina na dawowa ta d’auki wayarta takira Hassana
“Hellow sister kina lafiya?
“Lafiya lao Husaina tafad’a, wai dan Allah sister yaushe zakizo gidana shikenan ace tunda aka kawoni keda Momy ba Wanda yazo.
“Hmm kedai bari sister wlh ko ranar nan saida mukayi maganar zuwana gidanki nida Momy wallahi bakiga fad’an da yayiba wai lokacin zuwa beyiba, idan lokacin yayi ze gayamin da kanshi.
“Hmm sister kema bakiyi niyyar zuwaba, kodayake nasanki da tsoro kamar farar kura, amma in bacin haka me zai hana idan kinfito islamiyya kitaho alabashi idan lokacin tashi yayi saiki koma.

“A’a sister nikam gaskiya bazan iyaba, kinsan halin dady muddin nayi haka yagane kinsan bazemin da sau’kiba,
“To shikenan sis yanzu nagane baki ‘kaunata, amma danice ai duk yanda zanyi inzo gurinki zanyi tafad’a tare da fashewa da kuka…..
Hasaana Har cikin ranta taji tausayin ‘yar’uwarta yakamata, “shikenan kibari zanyima Momy maganar idan ta amince inanan tafe goben,
“To shikenan nasan ma Momy bazata’ki amincewaba, Allah kaimu goben ina jiranki.

Suna gama wayar jabeer nashigowa, tana ganin shigowarsa tayimashi wani mugun kallo up and down tare da buga wani uban tsaki “mtswww badai Zuciya, tafad’a tare da shigewa bedroom, kallo jabeer ya “karema falon yanda yayi kace-kace can plate nan cup nan robar ruwa, can ledar biscuit can kwalin lemu, ga kuma inda lemu ya zube ba’ayi mopping ba, girgiza kai kawai yayi sannan yanufi d’aki sai gashi yadawo sanye da best da wando threequter, plate da cups yafara kaudawa yakai kitchen sannan yad’auko mopper ya goge lemun daya zube, cikin ‘kan’kanin lokaci yagyara falon fess, sannan yashiga kitchen yadafama kansihi indomie dan yadawo da yunwa, cikin minti goma ya gama ya zauna falo yaci.

Love u all my Fan’s ???? oya sagem ????‍♂????????
[1/14, 8:13 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….26

gaisuwa gareku masoyan wannan littafi
Mmn Ummi
mummy Ramadan
Mmn Zee
Mom Afreem
Allah rayamaku yaranku yayima rayuwarsu Albarka, Nagode Allah bar Zumunci

Washe gari tunda ‘karfe biyu na rana Hussaina ke faman bugama Hassana waya dan ta tabbatar da zatazo d’in kokuwa bazatazoba,

Hassana na zaune kan kujera tana gyaran farce ta kalli Momy “Hmm kinga Hussaina ta isheni da waya A’kalla yau takirani yakai sau goma, wai dan Allah inzo gidanta kuma na gayamata daddy yahana yace lokaci beyiba amma ta nace da magiya, wai dan Allah in taimaka idan nafito islamiyya inje idan antaso sai indawo ai bazesan najeba shine nikuma nace gaskiya inajin tsoro amma bari in tambayeki idan kin amince sai inje.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button