BABU SO HAUSA NOVEL

AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

Zuby ta lula duniyar tunani Hussaina nata faman yimata magana amma ko Alama batajitaba, saida Hussainar ta ta6ota “lafiya ‘kawata Tunanin me kikeyi…

Saurin dawowa zuby tayi daga duniyar tunanin data Lula, “a’a ba kome kawai ina tunanin halin rayuwa, yau gidanmu tashi mukayi bamu d’ora tukunyaba ga babanmu bayada lafiya, tana kaiwa nan ta fashe da kuka.

Wani irin tsananin tausayinta Yakama Hussaina dan tasan abinda Zuby tafad’a ba ‘karya ko yanayin gidan dasuke zaune kad’ai ya Isa ka gane suna cikin Halin rayuwa.
“Kada kudamu inshaAllah idan jabeer yadawo zansa ya taimaka maku.

Zuby ta’kara fashewa da wani kukan munafunci kamar da gaske “nagode ‘kawata Allah saka da Alkhairi, “ba kome ‘kawata kada kidamu ai munzama d’aya tafad’a tana bubbuga kafad’ar zuby alamar lallashi.

Suna cikin haka suka jiyo sallamar suduka suka maida hankalinsu ga ‘kofar tare da amsa sallamar, Jabeer ne yashigo da sallama, ko kallon inda yake Hussaina batayiba saima kauda kanta datayi gefe tana danne-danne a wayarta.

: Da sauri Zuby ta sauka daga kan kujera ta dur’kusa har ‘kasa ta gaida Jabeer da Fara’a ya amsa “Zuby ce yau a gidanmu kice kinzo gun mutuniyar taki kenan, “eh wlh munzo shan manshanun amarya tunda haka akayi Auren ba gayya sai dai kawai mukaji a sama, murmushi jabeer yayi yace “wlh kuwa kinsan Al’amarin ubangiji muma yanda abin yazomaku haka yazo mana, mudai fatanmu atayamu addu’a.
“To Allah sanya Alkhairinsa yakuma bada zamanan lafiya, “Ameen ya amsa sannan ya wuce bedroom.

Saida Zuby ta tabbatar da shigewarsa sannan ta kalli Hussaina “kawata amma yanaga kamar baki murna da dawowar angon naki naga ko irin tarbar nan ta sabbin ango da amarya bakiyimashiba.
Yamutsa fuska Hussaina tayi “ai wannan tarbar sai idan akwai soyayya tsakani akeyinta, nifa yanzu babu soyayyar jabeer ko d’igo a cikin zuciyata, dan wallahi daze sakeni danafi kowa farinciki.

Saida Zuby tad’an razana dajin maganar Hussaina a zuciyarta tace “nifa ta fad’i gasashshiya dan naga Alamar raba Wannan shashar da Jabeer abune mai sau’ki, amma a zahiri sai tadafa kafad’ar Hussaina cikin tsananin nuna damuwa tace “Amma Hussaina sabodame kike son rabuwa da jabeer, yanzu kina tunanin akwai macen dazata samu gwarzon namiji kamar jabeer tayi fatan rabuwa dashi? Amma bansaniba wai hausawa sunce duk wanda ta ‘kone rumbunsa yasan inda toka ke tsada….. Bansaniba ko kinada wanda yafishine.

“Yauwa ‘kawata anzo wajen, inada Wanda yafi jabeer nesa bakusaba,
“Waye wannan? Zuby ta tambaya.
“hafiz mana, shine namijin da babu wani namijin daze maye gurbinsa a cikin zuciyata.

Wani sanyi Zuby taji ya ziyarci zuciyarta, dan tasan ‘kawar tata zatayi ba one ba one, dan kuwa tasan Halin Hafiz sarai baze ta6a Auren Hussainaba, tunda hartayi aure kuma wani namiji ya jusanceta bashiba, dan itama abinda tahanshi aurenta kenan dan tariga tabashi kanta, shikuma tsarinshi baya auren macen da yasani a mace kafin aurensu, yasha fad’ama zubyn haka lokacin datake kwakwar ya aureta, to barantana kuma wacce wani namijin ya kusanta bashiba.

Kallonta zuby tayi, “wow ‘kawata nafa manta da wannan guy d’in, gaskiya dole kike rud’ewa ki susuce akansa dan ya matu’kar iya soayayya, ga kuma iya……..

Alamar tafiyar dasukaji yasa zuby yin shiru, jabeer ne yafito cikin shigar ‘kanan kaya bakin wando da milk d’in riga sai ‘kamshin turarensa ke tashi da Alama shigarsa wanka yayi, ganinshi yasa Zuby mi’kewa to ‘kawata nizan wuce sai wani lokaci kuma.

Saurin tashi Hussaina tayi “d’an jirani mana, kallon jabeer tayi bako fara’a a fuskarta inason magana dakai, batajira amsarshiba tawuceshi zuwa bedroom, binta yayi daga baya, basufi minti goma da shigaba saiga Hussaina tadawo hannunta d’auke da bandir d’in yan d’ari biyar-biyar Sabbi fill tami’kama Zuby “kawata ga wannan akaima Baba, amsa Zuby tayi hannu na ‘kyarma “nagode ‘kawata nagode “kada kudamu ‘kawata kunzama d’aya.

Nan tayimata sallama ta tafi tana mamakin sakarci irinna Hussaina ace kasamu miji wanda zaka juya haka amma har kana ‘ko’karin rabuwa dashi.
Wani shu’umin murmushi tayi tare da cewa “Ni zuby zanyimaki Hankali Hussaina sai kingane ni Makira ce (na Fiddausi sodangi) wataran sai kinzo gidannan namiki korar kare……

Love u all my Fan’s ???????? shoki ????????‍♀????????
[1/12, 4:24 PM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page———————- 24

      *Bayan Sati biyu*

Hassana tana zaune gidan jabeer ne kawai amma babu wata kyautatawa irin ta ma’aurata dake shiga tsakaninta dashi daga 6angarenta.
A nashi 6angaren kuwa be tauyemata komeba, dan ba abinda tanema tarasa, abinci kuwa har jabeer yasaba da cin na restaurant dan ko sau d’aya Hussaina bata ta6ayin girki da sunan faranta ranshiba, kullum sai dai tadafa dai-dai cikinta tazauna taci idan tagama tatashi tabar plate nan, kullum haka zatabar gidan kace-kace hatta da gadon dasuke kwana batasan tagyaraba, duk da wannan abubuwan datakema jabeer amma bata Hanashi kanta idan yabu’kaci hakan, sauran abubuwanma tanayinsune wai kozeji haushi yasaketa amma ko kad’an beta6a nuna alamun ze rabu da itaba sai dai idan abin yademeshi ya zaunar da ita yari’ka mata nasiha,

zata zauna ta saurareshi yana gamawa zatace “Allahu Akbar, kaga Malam idan wa’azi zakayi kaje masallaci akwai masu bu’katar haka dayawa bananba inda bazeyi wani tasiriba, nifa ba dole akayima akan saika zauna daniba idan bazaka iyaba ka sauwa’kemin, ni wallahi da saki a hannuna yake da tuni na sawwa’kema na huta, wannan wane irin nacine kamar ni kad’aice mace a duniya kasakeni ka auro wata mana.

Wani gajeren murmushi jabeer yayi mai cike da takaici, “Hussaina bazan sakekiba, kuma badan ina son kyautata makiba kuma badan bazan iya rabuwar dakeba, bako d’aya kawai bazan iya sakinkiba dan saboda darajar mahaifinki, amma kisani duk abubuwan dakikemin watarana sai kinyi nadama….

Dariya tayi “Hmm nadama badai inyi nadamar rabuwa dakaiba sai dai inyi farinciki, saboda ko yanzu karabu dani inada masoyin daze aureni yari’keni da daraja da ‘kima fiye da ri’kon da kakemin…
Saukar wani lagfyayyen mari taji a kumatunta shine yahanata cigaba da magana tare da dafe kuncinta wanda yakemata tsananin rad’ad’i.
“Ka mareni… Wlh bazan yardaba, kuma wlh sai kayi nadamar wannan marin dakayimin azzalumi kawai.
Ganin yayo kanta yasa ta ruga da gudu tashige bedroom tare dasa key ta jingena da ‘kofar tana maida numfashi.
Cike da takaici da ba’kinciki jabeer yabar gidan,

** ** **

Hassanace zaune tare da Momy da Daddy bayan sungama cin abincin rana, daddy yatashi ze fita kenan Momy tayi magana “Alhj takira sunanshi, dakatawa yayi ya zuba mata idanu yana jiran jin abinda zatace, “nace wai yaushe Hassana zataje tagano gidan ‘yar’uwarta yakamata ace kabarta taje yau kimanin sati biyu kenan dayin aurennan amma kahanani kahana yar’uwarta zuwa wannan wane irin abune, ta’karashe maganar cikin ladabi.

“Ba yanzuba, yafad’a tare da d’aure fuska, tun yaushe nake gayamaku lokacin zuwa gidan waccan yarinayar beyiba, idan lokaci yayi da kaina zan umarci da aje, daga yau kada wanda ya’kara tunkarata da wannan maganar idanba so kuke ranku ya6aceba, yana gama fad’a yasa kai yafice.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button