BABU SO HAUSA NOVEL

AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

Yana kaiwa nan yayi shiru, mutane suka fara kallon kallo ana magana ‘kasa-‘kasa Kowa nafad’in albarkacin bakinsa, Hassana kuwa mamakine yagama rufeta, haka Momy da daddy, Zuby kau raba idanu kawai takeyi duk illahirin jikinta kyarma yakeyi, zufa tagama rufeta kamar wacce aka she’kama ruwa.

Bayan surutun yad’an lafa Al’kali kuma yayi ‘yan rubuce-rubucensa yad’ago ya kalli Hafiz yace “Hafiz kozaka iya gabatarma kotu da wannan recording din dakace ka d’auka lokacinda Zuby take jaddadama itace takashe Hussaina, Hafiz yace Eh ranka shi dad’e yasa Hannu aljihu yaciro wayarsa ya kunno inda recording d’in yake wani mutumi dake zaune gaban Al’kalin ya amshi Al’kali yabashi dama sannan ya kunna mutane sunyi tsit ana saurare bako shakka muryar zuby ce lokacin datake cewa of course bazan tsaya ina jayayya dakaiba nina kashe Hussaina saboda tashiga gonata mutane najin Haka suka d’au salati wasu suka fara Allah wadai da halin Zuby.

Saida Al’kali yabuga teburin dake gabansa sannan kotun ta saurara, “Abisa shedun da kotu tasamu tagamsu da cewa Zuby itace takashe ‘kawarta Hussaina dan tanaso ta auri mijinta, saboda Haka wannan kotu me Adalci ta yankema Zuby hukuncin kisa ta Hanyar rataya, muna fata wannan zezama Izna gamasu Hali irinna zuby.

Wani irin murmushin farinciki ya subuce daga bakin Hassana tafad’a Jikin momynta tana kukan farin ciki.

Zuby kuwa wata mahaukaciyar ‘kara tasaki tana kuka tana tsinema Al’kalin wai beyi hukuncin tsakani da Allah ba

Haka kotu ta watse zuby na hauka tana zage zage da fizge-fizge aka angiza ‘keyarta cikin ba’kar mota wacce ake saka masu ba’kin hali irinnata.

Love u all my Fan’s
[4/23, 6:35 PM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….55

  *Bayan Wta Daya*

Jabir ne zaune a office dinsa tunani barkatai acikin zuciyarsa, a wani 6angaren kuma na zuciyarsa soda ‘kaunar Hassana ne ke d’awainiya dashi, tunanin irin zaman dasukayi yakeyi, Lallai Hassana macece waccce kowane namiji zeyi fatan tazama mallakinsa, kuma uwar yayansa.

yarasa wace hanya zebi ya bayyana mata irin tsananin sondayake mata, jiyayi zaman office din ba dad’i saboda haka tattara takardun dake gabansa yayi ya ajiyesu tare da rufe office din, kai tsaye inda ya ajiye motarsa yanufa yabud’e yashiga sannan yasa key yatayar da motar yad’au hanyar gida, zuciyarsa cunkushe da tunane-tunane.

‘Kofar gida ya ajiye motarsa, sannan yafito, da nusaiba suka had’u cikin fara’a da sakin fuska take gaisheshi, “yaya jabeer sannu da Zuwa, “yauwa ya amsa sannan ya tambayeta ina zaki haka? Cikin ladabi tabashi amsa “nan ‘Kasan layinmu zanje gidan kitso, “owk to adawo lafiya, yafad’a tare da wucewa kai tsaye cikin gidannasu, da sallama yashiga, mama ya iske zaune tana sauraren redio, jin sallamarsa yasa tarage sautin redion tare da amsa sallamar “kaine yanzu da rana nan, tafad’a tana kai dubanta gareshi, lokacinne kuma ta fuskanci akwai damuwa tattare dashi, bissmillah zauna tafad’a tana tura mai kujerar dake kusa da ita.

Fridge yanufa yafara d’auko ruwa me sanyi sannan yadawo ya zauna tare da sauke wata ajiyar zuciya, ruwan yafasa yafara sha, ahankali yaji wani sanyi na sauka a zuciyarsa, saida yakarasa shanye ruwan sannan ya kalli mama ya gaisheta cikin girmamawa, bayan ta amsa, shiru yad’an ratsa na kimanin minti biyu, sannan mama ta numfasa tace “da alama akwai damuwa tattare dakai, shin miye damuwarka kafad’amin amatsayina na mahaifiyarka idan inada maganinta zanyima idan kuma babu inbaka shawara, idan itama bazatayiba zan taimakama da addu’a domin babu abinda ya gagari Allah.

Hakane mama, ba wata damuwa bace tafe dani, inasone Hassana ta maye gurbin ‘yar’uwarta amma kwata-kwata nakasa tunkarar mahaifinta da maganar.

Murmushi mama tayi me d’auke dajin dad’i tace “ni kaina na jima inayima kwad’ayin auren Hassana yarinya me hankali da ladabi da biyayya, ga girmama nagaba da ita, abinda yasa banyima maganaba Dan ina tsoron kada kabi za6ina kuma a maimaita yar gidan jiya, watakila bakada ra’ayin hakan, amma yanzu tunda ka furta da bakinka kabar kome a hanuna inshaAllah kome zezo da sau’ki.
“Kamar da yaushe Alhj yake gida zanje ni insameshi,
“eh to yana komawa gurin ‘karfe biyu na rana sai yakuma fita ‘karfe hudu na yamma.
“Kada kadamu inshaAllah gobe zanje gidan dakaina,

Cike dajin dad’i jabeer yayima mamanshi godiya, haka suka d’an ta6a fira, saida yaci abinci sai bayan azahar yabar gidan, zuciyarsa cike dajin dad’i dan abinda mama tafad’a mai gani yake kamar yasamu Hassana yagama.

A 6angaren Hassana kuwa tun ranarda aka yankema Zuby hukunci a kotu take jinta cikin wani farinciki, dan jitake kamar da hannunta tad’au fansar kisan da’akayima ‘yar’uwarta.
Wani 6angaren kuma na zuciyarta tsananin son jabeer da ‘kaunarsa ke d’awainiya da ita, dan d’an zaman dasukayi da jabeer ta fuskanci halayensa akwaishi da tsananin ha’kuri, ga yawan ibada, wasu hawaye taji sun zubo mata Wanda ita kanta batasan dalilin fitarsuba, tasa hannu tagoge sannan tad’aga hannuwanta sama tafara rokon Allah,
“ya Allah ka mallakamin jabeer amatsayin mijina, yazamo uban yayana, Allah ameen tafad’a tare da saukar wasu sabbin hawaye a kumatunta.

Kusan kullum haka take fama da dawainiya da soyayyar jabeer acikin zuciyarta tarasa Wanda zata fad’amawa kota d’an samu sauki dan ita dama bata cika kwashe-kwashen kawayeba, sai kuma ga abinda yafaru da ‘yar’uwarta ta sanadin ‘kawa tarasa rayuwarta, itakam ta tsani ‘kawa duk yanda take.

ina Baku ha’kuri na rashin samun typing akai-akai, kunsan jiki da jini, akace yauda gobe sai Allah

Love u all my Fan’s????
[4/23, 7:26 PM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….56

Washe Gari Hassana ce keta kai kawo tsakanin falo da kitchen, kallo d’aya zakayimata ka tabbatar tana cikin nishad’i haka kawai yau ta tsinci kanta da jin wani matsanancin farinciki, yanzuma girki tagama shine take jerawa kan dining, bayan tagama takoma tagyara kitchen ta goge sannan tawuce d’akinta kai tsaye toilet tashiga tashe’ka wanka, sannan ta d’auro Al’wala dan ganin lokacin sallar azahar yayi, tana fitowa ta zura wata doguwar riga tare da saka hijab ta shimfid’a abin sallah, saida ta kammala sallar tayi addu’o’inta tashafa sannan ta isa gaban dressing mirror tafara shafa wani cream me dadin ‘kamshi sannan ta murza powder a fuskarta tashafa kwalli tashafama lebenta man le6e.

Wadrope tanufa kai tsaye ta d’auko wasu riga da siket na material orange colour d’inkin yayi matu’kar kyau bakamar datasaka ajikinkta, sai jikin nata tare da Hasken fatar jikinta ya’kara fiddo da kyan material d’in.

Kitchen tanufa tazubo abinci tare da d’auko robar ruwa me sanyi, da madarar holandia takoma d’akinta tafaraci zuciyarta wasai kamar wacce akayima albishir da gidan Aljanna, bayan ta kammala cin abincin ta d’auki plate ta maida kitchen tana mamakin kanta yanda yau taci abinci me yawa haka kamar ba itaba, wanda rabon dataci abincin kirki tun ranar data zauna gidan jabeer amatsayin ‘yar’uwarta sai kau yau, a zuciyarta tace anya ba wani abu ke shirin faruwa daniba……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button