BABU SO HAUSA NOVEL

AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

Shiru sukayi suduka anrasa wanda zefara magana dan Hussainama yau ko arzi’kin gaisuwa Jabeer be samuba, illah wani irin haushinsama datakeji dan tadad’e dagayamshi maganar soyayyarsu ya janye ya nemi wata Amma dayake shine d’an anace sarkin naci ya’ki ha’kura.

Jabeer ne ya katse shirun ta hanyar cewa “jiya naga fitarku lokacin zaku islamiyya naso inyimaku magana amma sainaga rashin dacewar hakan kasancewar gurin dazaku yanada muhimmaci bekamata ace na tsaidakuba.
“Hmm aikode, kawai tafad’a tare da yamutsa fuska ta juyar da kanta gefe tana taunar cingam ‘kas-‘kas
Har cikin ranshi yaji haushin yanda tayi Mashi magana amma sai ya danne kasancewar anason namiji yazama me shariya akan wasu ‘kananan abubuwa, magana ya’kara karo na biyu.

“Gaskiya inajin dad’in yanda kuke zuwa islamiyyah fatana akodayaushe kafin Aurenmu ace kunyi safka kunyi hadda koda hizif talatin ga sauran litattafan addini, kinga ko’ina zanyi Alfahari da matata tanada ilimin addini, sannan kuma uwa uba yaranmu zasu koya a gun mamarsu kafin suma asakasu tasu islamiyyar…..

Dakatar dashi tayi ta hanyar d’aga mashi hannu tana magana cikin masifa “dakata malam, wai akan wa kake magana? “Ni, tanuna kanta da hannunta, to indai nice kama daina wannan tunanin kacire soyayyata daga cikin zuciyarka, danni yanzu batakai nakeyi ‘karama kanemi me sonka tunda wuri kafin lokaci ya’kurema.

Haba Hussaina donmi kike nema ki gujeni? Menayimaki? Kadafa ki manta mundad’e muna soyayya kullum burinmu be wuce muzama mata da mijiba, amma yanzu Cikin ‘kan-‘kanin lokaci kina nema ki canja ra’ayi.

“Oh nema manake incanja, tobari kaji in gayama ba nema nakeyiba nama canja gaba d’aya yanzu baka cikin tsarin mazan danike burin aure…
Tuni kuma wani ya maye gurbinka acikin zucyata saboda haka kaje kawai kanemi wata,

Cike da mamaki da takaicin yanda Hussaina ke gayamar magana yabar gidan, dan kosamun damar yin bankwana da Momy beyiba,

Dai-dai harabar gidan suka had’e da Zuby tana shigowa “tana ganin jabeer ta washe baki “a’a’a Manya kenan anzo gun mutuniyar, dariyar ya’ke kawai ya ‘ka’karo Wanda hakan baze hana kagane cikin tsananin damuwar dayakeba,
“Eh wlh kuma gashi harna fitoba, to shikenan agaida gida.

Tana tsaye yashige motarsa yatayar da ita Malam bala me gadi yabud’emashi get yanatayimar fadanci dan yasaba duk ranar dayazo yakan bashi nacin goro amma yau sai yaga Alamar ranshi kamar a 6ace yake, haka yabar gidan Malam bala yamaida get yarufe sannan yakoma kan bencinsa yazauna yana cewa “ho yar nema yau ta6atama mutumin rai ‘yan aninnan danike samuma yau bansamesuba, sannan yajawo redio ya kunna yana saurare.

Zuby kuwa taso taji wani abu daga bakin jabeer amma ganin ranshi a 6ace kuma bebata fuskar hakanba yasa tayi ciki tana zumud’in ji daga bakin ‘kawarta.

Love u all my Fan’s ????????shoki ????????
[1/2, 7:21 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon ya mace ????????

Page————————-8

Rungumota yayi jikinsa tare da d’ora lips d’insa kan kumatunta yasakar mata kiss,
“Kinsan wani abu babyna? Yafada cikin had’addiyar murayarshi me kashe mata jiki.
“A’a saika fad’a my dear.
“Gaskiya naji dad’i nayi matu’kar farinciki yanda kika amince kikazo inda nake yanzu na’kara yarda da ‘kaunar da kikemun hundred percent, wani irin dad’i taji har cikin ranta sannan tafara magana cikin kasalalliyar murya,
“My dear inaso ka yarda dani kamar yanda na yarda dakai,
“Na yarda dake babyna yafad’a tare da saka hannunshi d’aya cikin hijab d’inta yafara wasa da dukiyar fulaninta, hannunsa d’aya kuma nakan cikinta yanamata wani salo wanda ke ‘kara rikitata,

Suduka sun lula duniyar soyayyar shan minti, bakajin komai sai numfashi dasuke maidawa sama-sama, haka sukayita wasanni tsakaninsu tare dajin dad’in kasancewa da juna.

Hassana kuwa tana islamiyyah suna karatu, bayan malamin dake d’aukarsu darasin Qur’an yafita sai me d’aukarsu hadith yashigo, saboda haka tana ganin haka tasan lokacin tashinsu yakusa dan dama hadith shine period d’in ‘karshe kuma baya dad’ewa lokacinsa ke ‘karewa saboda haka kafin yafara karatu ta d’auko wayarta sunan Hussaina ta lalubo sannan ta dannan kira.

Lokacin Hussaina na jikin Hafiz yariga yagama tayar mata da hankali kwata- kwata bata cikin hayyacinta har wayar takaraci ringing d’inta tagama bata d’agaba, sai a kira na ukku sannan tad’aga
“Hellow sister antashine, “eh kitaho muhad’e yanda zamu koma gida tare.
“Owk ganinan zuwa.

Bayan ta tsinke kiran ta maida dubanta ga Hafiz “yauwa my dear dama inason magana dakai,
“Ina jinki babyna.
“Bawata magana bace dama daddynmune yace yabamu wata d’aya mu fitar da miji, nikuma ba wanda nakeso sai kai shine nace yakamata ka gabatar da kanka gareshi.

Shiru yayi kamar me tunanin wani abu, itakuma ta zubamar ido tana jiran amsar daze bata, ganin beda niyyar yin magana yasata ta6oshi “dear lfy naga kayi shiru kobakaji me nake fad’a bane.

“Murmushi yayi “najiki babyna, kada kidamu aini dama irin wannan ranar nake jira, zanzo inshaAllah kada kiji kome aini me ‘kaunarkine.
“Wani irin murmushi tasakar mashi cikin farin ciki sannan taduba wayarta ‘karfe shidda saura minti goma a gaggauce sukayi bankwana yabata iyayen kud’i ta’ki amsa saboda tana tsoron gida aganta dasu.
Me napep ta tsaida tashiga zuwa gidansu.

Yana ganin tafiyarta ya kece da wata irin dariya tare dakaima sitiyarin motarshi duka “wow Allah kai damo ga harawa kobeciba yayi birgima, kowa yagayamata zan iya auren macen danagama lugui-guitawa a waje, aini sai kamilar mace wacce tasan darajar kanta ba irinkiba wacce zatabi namiji har inda yake.
A haka yatashi motarsa ya ‘kara gaba ranshi fari tass.

Hussaina kuwa napep na ajiye Hassan itama ana ajiyeta, saboda haka tare suka shiga gida babu wata matsala.

washe Gari
Da misalin ‘karfe hud’u da rabi na yamma Zaune suke falo suna kallon gidan tv startime tashar farin wata suna shirin addini da Alqibla, kasancewar yau Alhamis ba islamiyyah suduka hada Momy duk sun maida hankalinsu kan shirin amma banda Hussaina wacce hankalinta yana kan waya tana chat da Hafiz Wanda yawanci magan-ganun duk na shan mintine sukeyima junansu.

Tsayuwar mota sukaji a harabar gidan, da sauri Hassana ta le’ka ta window kafin tadawo ta zauna ta dubi Hussaina, tace “jabeer nefa yazo, cigaba da chat d’inta Hussaina tayi bata ko kalli Hassanaba barantana tabata amsar maganar datayimata.

Ganin batada niyyar motsawa yasa Momy cewa “ba magana ake makiba kobakijine jabeer ne yazo,
Turo baki tayi ni wlh momy wannan jabeer d’in yadameni nifa nagayamashi yanzu bani sonshi ko ana dole ne……
Bugemata baki momy tayi “banison sakarcin banza idan kince kin daina son jabeer wa kike dashi wanda yafishi, yaro mutumin kirki me hankali ga nutsuwa, saboda hakama mahaifinku yad’aukeshi tamkar d’an cikinsa.

Tashi tayi tana dira ‘kafa cikin shagwa6a ni Momy nafad’amaki inada Wanda nakeso kuma ai yace zezo ya gabatar da kanshi gurin daddy.
“Keni rufemin baki sakaran banza.

Momy ta kalla Hassana “jeki shigo dashi,
“To tafad’a sannan tanufi ‘kofa tana kallon Hussaina
Wacce tadage ita a dole batason jabeer hadda yan guntayen hawayenta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button