BABU SO HAUSA NOVEL

AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

Bayan Hannu Hassana tasa ta share hawayen dake bin kumatunta sannan ta kalli jabeer cikin dasashshiyar murya take magana “Nifa ba wani abu bane ke damuna kawai ina tunanin 6atan “yar’uwatane yau kwana biyu ko labarinta ba’a samuba.

Tana kaiwa nan tafashe da wani sabon kuka, jabeer har cikin ranshi tabashi tausayi sosai janyota yayi jikinsa yana rarrashinta, da dabara tasamu ta kwace kanta tanufi kitchen domin had’a masu breakfast.

** ** **

Daddy zaune daga bakin gado kallo d’aya zakayimai ka tabbatar da tsananin damuwar dake tattare dashi, Momy kuma nakan abin sallah tana lazimi idanunta fall da hawaye ro’kon Allah kawai take Allah bayyanar mata da d’iyarta aduk halin datake ciki,

Wayar daddy dake jone jikin socket tana chaji tahau ruri alamar shigowar kira, ko motsawa beyiba barantana yad’aga haka ta ‘karaci ringing d’inta harta tsinke aka kuma kira karo na biyu nanma beyi niyyar d’agawaba, dan ko kallon wurin beyiba, Momy ce ta kalleshi tasa hannu ta goge hawayen dasuka gangaro kan kumatunta tace “Alhj wayarka fa tana ringing, shiru yayi kamar beji maganar datakeba, magana ta’karayimashu lokacin da kiran wayar ya’kara shigowa karo na ukku “Alhj yakamata ka d’aga wayarnan dan da alama kowaye yadamu daya gayama kowace mgana ce saboda wanda yakiraka dai-dai wannan lokacin ‘karfe shidda na safiya yakira baka d’agaba yanace yanata kira kasan maganar nada matu’kar muhimmanci, tana rufe bakinta wani kiran yakuma shigowa karo na biyar, Momy bata jira daddy ba tanufi inda wayar take ta d’auko ta danna ok sannan ta mi’kamai ba musu ya kar6a yakara akunnensa batare daya kalli sunan wanda ke kiranba.

“Assalamu Alaikum aka fad’a a d’aya 6angaren, me maganar bejira jin abinda Daddy ze fad’aba yacigaba da magana
“Sunana Ahmad turaki comusioner of police, ina fata dai muna magana da Alhj manair company?
“Eh dashi kake magana daddy yabashi amsa a ta’kaice.
Zaku iya zuwa babbar headquarter mu ta police domin tabbatar da wata gawa da muka tsinta kota d’iyarkace.

Saurin mi’kewa tsaye Daddy yayi yana yana salati “to shikenan ganinan zuwa bekobi takan Momy ba ya suri key d’in motarsa jikinsa dagashi sai jallabiya, silifas yazura a ‘kafarsa yana shirin fita, momy tabiyoshi tana tambayarshi “Alhj lafiya? Beko sauraretaba yawuce hankali tashe.

Fad’awa Momy tayi kan gado tafashe da wani irin kuka me ban tausayi “ya Allah ka bayyanamin Hassana Allah sa duk inda take tana cikin aminci da kariyarka ya ubangiji, wani sabon kuka ya kubce mata.

Daddy na isa headquarter police bayan sun gaisa da comusioner nan yahad’a daddy da wasu police guda hud’u suka nufi babban asibitin dake garin kai tsaye matuare (d’akin ajiye gawa) suka nufa nan aka jawo dorowar da gawar Hussaina take, Daddy na ganinta yafashe da kuka kamar ‘karamin yaro, nan ya tabbatarma ‘yansandan d’iyarsace lokacin duk kamanninta sun canja fuskarta ta kunbura ga jini daya gama wanke mata jiki.

Nan yansandan suka shiga rarrashin Alhj “kayi ha’kuri Alhj inshaAllah zamu tsaurara bincike sai mungano Wanda ya aikata wannan mummunan laifi, dan bincike ya nuna ankashe marigayiyar ne ta hanyar dukan da akayimata aka.

Daddy kasa magana yayi sai kuka kawai dayake, haka aka d’auki gawar Hussaina cikin motar police d’in aka nufi gida da ita.

Love u all my Fan’s ????????????????
[2/2, 9:05 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….37

® TALENTED WRITER’S GROUP (TWG) ????

Momy kuwa tun bayan fitar daddy Daga gidan gabanta keta fad’uwa takasa zaune takasa tsaye.

Jin ‘karar bud’e get tayi da sauri tatashi tanufi ‘kofar fita daga falon zuwan harabar gidan, ganin motar me gidanta tare data police yasa tayi saurin komawa ciki tare da dafe ‘kirjinta saboda jitake kamar zuciyarta zata fad’o saboda bala’in fargaba.

Jin annufo falon yasa fad’uwar gabanta ya yawaita, bata ankareba kawai sai gani tayi anshimfid’ar da gawar Hussaina tsakiyar falon, tana kai dubanta gareta taji duk illahirin wasu jijiyoyin jikinta dake aiki sunyi tsaye cak, kafin ayi wata magana sai ganin Momy akayi ‘kasa ba alamar numfashi tattare da ita.

Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un Daddy yari’ka furtawa da sauri ya d’auko ruwa ya yayyafa mata, nan akayi nasarar dawowar numfashinta bakinta d’auke da salati.

Nan Daddy yacigaba da yimata nasiha yana rarrashinta da ‘kyar yasamu ta nutsu ba abinda take maimaitawa a zuciyarta sai salatin annabi.

Ranar kafin ad’au wani lokaci labarin mutuwar Hussaina ya bad’e gari dandanan gidan Alhj mansir yacika da ‘yan’uwa da abokan arzi’ki wasu na zubar da hawaye wasu kuwa sunyi jugum-jugum. Amma duk a tunananin mutane harma da daddy da Momy Hassanace ta mutu.

** ** **

Hassana zaune tana duba wani littafi na addu’oi kad’an-kad’an tayi try number Hussaina wai ko Allah zesa tashiga dan tanaso tagayamata Halin datake ciki, amma kamar kullum dai akashe ake cewa.

Jabeer ne yashigo jikinsa a sanyaye. haka kawai yana shigowa Hassana ta tsinci kanta da wata mummunan fad’uwar gaba.

Kallonta yayi ya matu’kar tausaya mata sannan yace “ki tashi yanzu zamuje gida daddy yana nemanmu, jitayi fad’uwar gabanta ya tsananta lokaci guda hawaye ya wankemata fuska a tunaninta jabeer yakai karartane.

Tasowa tayi jiki a sanyaye ta dur’kusa gaban jabeer “dan Allah kayi ha’kuri indai wannan maganarce nayima Al’kawari wlh zan gyara.

Wani irin tausayinta ya’kara mamaye zuciyarsa “a’a ba wannan maganar bace ban dad’e da isa office ba daddy yakirani yace muzo yanzu nidake nikaina bansan ko miye dalilin kiranba, haba tanajin haka wani sabon tashin hankali ya ziyarceta jikinta yafara kyarma kad’an yarage tasaki fitsari dan bako tantama tasan asirinsune ya tonu kan abinda suka aikata itada ‘yar’uwarta nasanya jabeer yin AUREN TAGWAYE batare da saninsaba, innalillahi kawai tacigaba da furtawa acikin Zuciyarta, ahaka tanufi bedroom ta bud’e wadrope ta d’auko wata doguwar Riga ta canja kayan jikinta sannan tasaka hijab med’an girma wacce ta tsayamata iya gwiwa, plate shoe tasako sannan tafito falo ta iske jabeer na jiranta, yana ganin fitowarta yayi gaba tana biye dashi har gurin mota yabude gurin driver ya zauna sannan itama yabud’emata gidan gaba ba musu tashiga, amma duk illahirin jikinta kyarma yake dan kallo d’aya zakayimata ka tabbatar da bata cikin nutsuwarta.

Ahaka har suka ‘karaso ‘kofar gidansu tundaga nesa tahango dandazon Al’umma haka yacanjamata tunanani Zuwa wani daban “to wannan iyayen mutanenfa meke faruwane “innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un.

Hankalinta be’kara tashiba saida tashiga harabar gidan nanma cike yake da jama’a maza suna jiran afito da gawa, cigaba tayi da tafiya dai-dai ‘kofar dazata sadata da falon gidan taga wasu gun-gun mata zaune sunyi jugum-jugum sai d’aya daga cikinsu ta nuna Hassana tana cema sauran matan “wannan itace Hussainar marigayiyar, d’ayar tace “oh itace wacce akayima aure kwanakin baya, d’aya tace itacefa Allah sarki mutuwa me yankan ‘kauna lalle wannan yarinya tayi rashi Allah bata ha’kuri da dangana………

Dai-dai wannan lokacin Hassana tanemi numfashinta tarasa sai mutanen dake gurin sukayo kanta anata salati aka kinkimeta akayi ciki da ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button