BABU SO HAUSA NOVEL

AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

Kama hannunta Hassana tayi suka nufi d’akinsu, da kyar Husaina take tafiya saboda ba ‘karamin duka tasha hannun daddynsu ba,

Zaunar da ita Hassana tayi bakin gado tana sharar kwallah, tace “kinga abinda nake gujemaki koh, ba irin neman dabanyimaki gurin dinner d’innan ba amma ban gankiba, wai ina kikajene?

Cikin dasashshiyar murya Hussaina tace “uhm yanzu banida lokacin dazanbaki wannan amsar,
Toilet Hassana tanufa batare data ‘karama Hussaina wata maganaba ruwan d’umi tahad’amata tarakata har toilet sannan tajawo mata ‘kofar, haka tayi wanka ta gargasa jikinta bayan tafito Hassana tasa Robb ta shafemata jikinta sannan sukabi lafiyar gado, kowace tayi shiru kamar me bacci a zahiri amma kowace da tunanin datake cikin zuciyarta, Hussaina tunanin Hafiz ne fall cukushe a zuciyarta, “lallai Hafiz ya iya soyayya, yanzu nagane jabeer ba kome ya iyaba a fanni soyayya sai dai kullum idan yazo yakamayimani nasiha da sauransu, nikam nafison namiji d’an life Wanda yasan takan love, gaskiya akwai sakal kan maganaraurean da jabeer dan ni yanzu babu namijin danake muradi a rayuwa kamar Hafiz, dan Abinda ya faru tsakaninmu yau yasa naji bana bukatar kowane namiji sai shi.

Hassana kuwa tunani take shin ina ‘yar’uwarta tashiga har takai wannan daren bata dawo gidaba, Allah sa dai Hussaina bata biyema samarin shahoba, mayaudara “Hmm tafad’a shiyasa niko Alama bana harkar samari.
Da haka ta gyara kwanciyarta bacci yayi awon gaba da ita.

6angaren dady kuwa bacci gagaran idanunsa yayi tashi yayi ya zauna gefen gado ya zabga uban tagumi, zuwa can kuma yami’ke tsaye yafara safa da marwa cikin d’aki, “lallai dole inyi saurin yima tufkar hanci, saina tashi tsaye kan tarbiyar yaranan, saboda zamaninnan yanzu saika haifi d’a baka haifi halinsaba. Kusan raba dare daddy yayi yana tunani.

** ** ** **

Washe gari zaune suke kan dining suna breakfast bakajin motsin kome sai ‘karar plate da cokulla, kowane ka kallah cikinsu rai a dagule dakuma tunanin abinda yafaru jiya.

Bayan sun kammala daddy yayi gyaran murya “kunajina? Suduka suka jiyo suka kalleshi, “tunda abin naku yazama lalata inaso insanar daku na soke maganar makarntar dazakuje AMUSLIM COMMUNITY SCIENCE &TECHNOLOGY FUTUA daga yau kucireta a ranku kuduka aure zanyimaku, ke Hassana inaso kifito da miji nanda wata d’aya, ke Kuma Hussaina ya watsamata wani matsiyacin kallo “kigayama jabeer inason ganinshi, wani irin Fad’uwar gaba Hussaina taji dajin dady yace yana neman jabeer, sadda kai tayi ‘kasa “daddy nifa mundad’e da 6atawa da jabeer.

Shiru daddy yayi yana kallonta, toki fiddo miji nanda wata d’aya, idan kika wuce iya adadin kwanakin dana ebar miki zand’au duk matakin danaga ya dace.

Mi’kewa yayi tare da d’aukar jakarsa ta zuwa office sannan ya kalli Momy “maganar fita kuma daga yau nakasheta idan sunbar gidannan a tabbatar islamiyya zasu, yana gama fad’a yasa kai yafice.

Love u all my Fan’s ???????? Shoki ????????
[1/2, 7:21 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon ya mace ????????

Page————————-4

Hassana na daga d’akinsu taji shigowar daddy wani mummunan fad’uwar gaba taji, tanajin lokacin da Momy kemasa sannu da zuwa, yana zama ba abinda yafara tambaya sai “Ina yarannan suke? Cikin inda-inda Momy tabashi amsa “uhm am suna d’akinsu ko Alh….

Kwalamasu kira yashigayi “Hassana….Hussaina….
Hassana naji tayi saurin Amsawa “na’am…
“Kuzo nan ina nemanku “to ta amsa jiki na kyarma tasako d’an karamin hijab d’inta ta fito, durkusawa tayi gaban daddy “gani daddy tafad’a tare da sunkuyar da kanta ‘kasa gabanta sai dukan tara-tara yake.

“Ina ‘yar’uwar taki? Daddy ya tambaya, “im ahm….uhmmm tafara inda-inda tarasa wace amsa zata bayar domin kare ‘yar’uwarta shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta.

Tsawa daddy ya kwatsa mata “ke…. Ba magana nike dakeba ina ‘yar’uwarki nace? Jiki na ‘kyarma tafara magana tana d’an ja da baya dan taga yanda daddyn nasu ya zuciya a lokacin ze iya mazgeta, “daddy munje walimar bikin wata ‘kawarmune shine dazan taho nayita nemanta bangantaba shine nikuma nataho,
“Owk good hakan yayi kyau, shine ita ta zauna dan bata tsoron fushina, aiko ranta inyayi dubu a gidannan yau sai ya 6aci, kallon Momy yayi “kekuma kinsan bata dawoba amma ko ajikinki saboda baki damu da tarbiyar yarankiba ko “haba Alhj ya zakace bandamu da tarbiyarsuba, wlh tun d’azu nake faman kiran wayarta sai tacemun gatanan to ya kakeso inyi? Ko zuwa zanyi intaho da ita,
“A’a ba tahowa zakiyi da itaba, idan bakije kika taho da itaba nizan taho da ita dakaina, yafad’a yana nuni da ‘kirjinshi da hannu.

Bejira abinda zatafad’aba ya zari cable d’in jikin tv yafita zuwa harabar gidan,
Me gadi na hangoshi tafe yataso da sauri “Sannu da fitowa Alhj, “yauwa mal bala, abinda kawai ya furta kenan sannan yafita daga wajen get d’in gidan ya tsaya ya maida hannuwanshi duka baya, yafara safa da marwa yana jiran yaga ta ina Hussaina zata 6ullo, tsawon kimanin minti goma sha biyar yana zarya gurin Amma bako Alamarta, mal bala me gadine ya le’ko cikin girmamawa yafara magana “Alhj lafiya kuwa naganka haka kamar hankalinka a tashe?
“Mal bala yarinyarnan ni zata rainama hankali ni zata maida mutumin banza cikin garinnan, da darajata da ‘kimata ace wai har kamar ‘yanzu ‘karfe goma da minti ashirin da takwas yarana suna gantali a gari.
Mal bala yace “amma Alh ai naga kamar sundawo ko? “Gudace tadawo yanzu jiran dawowar d’ayar nake.
“To Alhj Allah maidota lafiya, Allah sa duk inda take tana lafiya.
Komawa mal bala yayi daga ciki ya zauna kan d’an bencinshi, yanda hankalin Alhj yatashi shima duk sai yajishi cikin damuwa, saboda Alhj mutum ne harda rabin mutum.

Da misalin ‘karfe sha d’aya saura minti goma, lokacin Alhj yagaji da zarya tsakanin wajen get d’in gidan zuwa cikin gida, yana zaune kan bencin mal bala, tsayuwar mota yaji dai-dai get d’in gidansa da sauri Alhj ya mi’ke le’kawa yayi lokacin Har Hussaina tafito daga motar me motar yayi gaba abinsa,

Momy kuwa da Hassana suna cikin gida hankalinsu a tashe, Hassana banda kuka ba abinda takeyi.

Hussaina kuwa bayan Hafiz ya ajiyeta ya wuce sai lokacin wani mugun tsoro ya dirar mata cikin zuciya, jikinta yafara ‘kyarma, hankalinta be ‘kara tashiba saida taduba agogo taga ‘karfe sha d’aya na dare, ahankali tafara buga get d’in gidan, da sauri mal bala yazo ya bud’e mata tana Shiga,tafara tafiya da sauri tana wai-waye saida tazo gab dashiga falon gidan ta tsaya tacire takalminta dan kada ajiyo ‘karar tafiyarta, ri’ke takalmin tayi a hannu sannan tatura ‘kyauren falon ahankali.

Love u all my Fan’s ???????? shoki ????????
[1/2, 7:21 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon ya mace ????????

Page————————-6

  *Bayan sati d'aya*

Hassana da Hussaina sun daina fita konan da can kullum sai dai idan zasu islamiyya, maganar fitar da miji kuwa kullum sai daddynsu ya tinasar dasu,

Yauma kamar kullum zaune suke kan had’addun kujerun dake zagaye da babban falon gidan, Hassana ta kalli Hussaina, “nikam sister inaso muyi wata magana dake,
“Ina jinki Hussaina tafad’a,
“Wai meyasa kikacema Abba kun 6ata da jebeer Alhalin ba abinda yashiga tsakaninku,
Murmushi Hussaina tayi sannan ta d’au ‘kafa d’aya ta d’ora kan d’aya tana girgizawa “ba wani dalili kawai tsuntsun ‘kaunarsane ya canja she’ka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button