BABU SO HAUSA NOVEL

AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

Ahaka ta maida kayanta ta d’auki jakarta koda ta d’auko wayarta kashe taganta baki d’aya bata tsaya kunnawaba sakata kawai tayi a jaka sannan tanufi ‘kofar fita daga gidan.

Cikin sa’a taga gidan bud’e batayi wata-wataba tafito tad’au hanya dukda ba’kin duhun dake akwai ga unguwar tsit babu wani mahalu’ki bakajin motsin kome sai haushin karnuka da kukan tsun-tsaye.

Tafiya take batare datasan inda zataba, harta fito titi, nanma wani titi rami’ka batare datasan inda ze 6ulla da itaba.

Tun tana tafiya da sauran ‘karfi-‘karfinta har tafara gajiya tafara layi kamar wacce tasha tabugu.
Da-dai bakin wani junction taji an haske mata fuska da wata irin fitila me tsananin haske hannu tasa tana karewa muryar wani namiji taji yana cewa “hey your under arrest kune yan’iska masu shaye-shaye da yawon banza ko.

Kafin tayi wata mgana sunsakata mota sai ofishinsu.
Ganinta office d’in yansanda yasa hankalinta yad’an kwanta dan koba kome tasan ta ku6uta.

Love u all my Fan’s ???????? shoki ????????
[1/2, 7:21 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon ya mace ????????

Page————————-11

washe Gari bayan sun dawo daga isalmiyyah, Hussaina taje d’akin Momy zaune ta isketa bakin gado tana nazarin wani littafin addu’oi cikin ladabi ta zauna kusa da ita.

“Momy wata Alfarma nazo nema gurinki,
“Tame ina jinki fad’i, momy tace batare data kalletaba,
Nan tashiga inda-inda tana ganin kamar ‘karyar dazatayi bazata fishshetaba amma sai wata zuciyar tace “ki kwatanta hausawa sunce a rashin tayi akan bar araha.
“Dama Im…wai asibiti zamuje ganin mamar Zuby shine nakeso dan Allah ki taimakeni kibarni wlh namiki Al’kawarin bazan wuce awa d’ayaba.
“Kinga Hussaina banison abinda zezo yad’agamin hankali ina zamana lafiya, yanzu kije kisamu guri kiyi zamanki kuma mahaifinki yadawo yatarad bakinan wace amsa zanbashi,

“InshaAllah Momy bama zesan najeba,
Haka dai tayita magiya har momy tabarta tare da saharad’in idan daddynsu yadawo bata dawoba zatace batasanma fitartaba, tace ta amince da hakan.

Cikin Zumud’i takoma d’akinsu ta d’auko wani tsadadden swiss less maroon colour tasanya sannan tasanya takalmi milk jaka milk, sai tayi too much kasancewar zaren da akayi kwalliyar less d’in milk ne sannan tabi da milk d’in mayafi, {mashaAllah koni zee dana kalleta nasan ba ‘karamin kyau tayiba}

Hassana dake zaune tana bitar littafin ibadah wanda akayimasu ‘kari yau, ta kalleta “uhm sister wannan gayu haka Kuma sai ina?
“Sorry sister sauri nakeyi idan nadawo zakiji,
“To Allah maidoki lafiya
“ameen kawai tace tafice, A falo ta tarad da momy saida gabanta yayi mummunan fad’uwa dan batayi tunanin ganinta nanba,

Kallo Momy ta’karemata daga sama har ‘kasa “keda zaki ganin marar lafiya kuma da wannan gayu haka,
‘Ka’karo murmushi tayi “Hmm Momy kuma dan za’a ganin marar lafiya ba’a sa kaya me kyau.
“To shikenan nidai nagayamaki karki dad’e.
“InshaAllah bazan dad’eba.

Tana fita tahau napep sai inda sukayi mahad’a da Hafiz, tana isa kuwa ta iskeshi a mota, bud’emata yayi tashige sannan suka d’au hanya.

Sunyi tafiya me nisa kafin su shiga rukunin wasu gidaje da Alama estate ne, bakin wani gida sukayi parking shine yafara fitowa sannan yabud’emata tafito tare suka jera har zuwa cikin gidan,

Wani ‘kawataccen falo yayimata masauki gidan tsit kamar ba mutane amma kuma yanayin kayan gidan zaka kallah kagane akwai mutane, zama sukayi suna fira sama-sama kusan minti sha biyar ba Alamar wani ze fito, nan Hussaina tad’an tsorata ta kalli Hafiz Wai ina mutanen gidanne,
Murmushi yayi haba babyna kamar ba wayayyaba hajiya tana ciki yanzu zata fito, ina zuwa yafad’a tare da mi’kewa yanufi pridge lemun 5ali6e ya d’auko tare da cup d’in glass ya ajiyemata,
“Bari ingyama hajiya may be bataji shigowarmu bane, wani d’aki yashiga da Alama bedroom ne bayan minti biyar yafito ya kalli Hussaina wacce kallo d’aya zakayimata kagane a tsorace take “hajiya tana wankane amma tana zuwa, wai bakisha lemunba “Uhm na’koshi nidai sonike intafi gida kada amun fad’a kagafa har bakwai da minti sha tara tafad’a tana duba agogon wayarta.
“Koma miye ai kinsha koda lemunne kinsan idan bakishaba bazanji dad’iba.

Zubowa tayi cikin cup tad’an kur6a kad’an ta ajiye
“Haba me kikasha nan?
Lemun yad’auka yacika cup d’in yafara bata da kanshi da ta’ki kar6a ganin ranshi ya 6aci yasa ta ‘kar6a a hannunta ta shanye sannan ta ajiye cup d’in.

Cike da farinciki ya kalleta “kokefa babyna amma da kintsaya wani no’ke-no’ke “Uhm kawai tace dan tunda tasha lemun jikinta yamutu sai wata kasala data rufeta.

Hafiz yana lura da halin datake ciki saboda haka mi’kewa yayi tare dayin hanyar d’akin dayashiga d’azu “ina zuwa nasan yanzu tagama.

Hussaina kuwa hamma tafara jerowa d’aya bayan d’aya tana lumshe idanu cikin minti bakwai bacci me nauyi yayi awon gaba da ita.

Saida ya dai-daici maganin dayazubamata a lemu ya Isa yin aikinsa sannan yafito ganinta yayi kwance kan kujera tana shara bacci wani shu’umin murmushi yayi tare da ‘karasowa inda take.

Love u all my Fan’s ???????? shoki ????????
[1/2, 7:21 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon ya mace ????????

Page————————-13

Wani d’an sandane ya kalleta Wanda da Alama shine babbansu yace “miye sunanki?
Jiki na kyarma tabashi amsa “Hussaina,
“Ke yar gidan wacece kike yawo da wannan daren?
“Uhm wlh yalla6ai ba yawo nikeyiba, hasalima ni bansan ya’akayi nafito daga gidaba.
“Shut up, yafad’a cikin d’ga murya, ke muzaki rainama wayo, irinki-irinki mungamu yafi a ‘kirga, hadama wad’anda sukafiki iskanci.
“waye zefitodake daga gidanku batare da izininkiba, kada kimanta cikin Halin da aka kamaki na maye koshima bakisan ya’akayi kikayi shaye-shayen ba?

“Wlh yalla6ai bansha komeba na rantsema da Allah,
Tassss saukar wani lafiyayyen mari taji a kumatunta wanda wannan d’an sandan ya d’auketa dashi, marinda saida ya gigitata saboda tsananin azabar tafin hannun d’an sandan ba ‘karamin kato bane.

A ‘kufule yace zaki fad’amana ke ‘yar’waye kokuwa saina sa6amaki.
Cikin tsananin gigicewa take magana “zanfad’a…. Zanfad’a wlh.
“Oya ina saurarenki d’ansandan yafad’a tare da tsareta da manyan idanunsa masu ban tsoro.

“Ni Yar gidan Alhj Mansir company ce.
“What? ‘Dan sandan yafad’a tare da mi’kewa tsaye.
“Karya kike yafad’a tare da nunata da yatsa, duk fad’in garinnan waye besan Alhj Mansir kamfaniba, mutumin kirki me halayya ta kwarai ace ke yarsace kina wannan munanan halaye.
Kuma ba wannan ba iya saninmu Alh Mansir bayada wasu ‘ya’ya sai yara biyu yan tagwaye.
“Yan la6ai wlh nice ai mune yan tagwayen Nice Hussainar dan Allah Ku taimakeni Ku maidani gidanmu.

“Sajen Habu, dan sandan yakwalama wani daga cikin yansandan kira.
Da sauri d’ansandan ya iso gabanshi ya ‘kame tare da saramashi.

“Maza a fiddo mota yanzu zamuje gidan Alh Mansir kamfani “yes sir yafad’a saida ya’kara saramashi kafin yafita zuwa ma’ajiyar motocin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button