BABU SO HAUSA NOVEL

AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

Nan sukayima Malam godiya sannan suka koma gida, Hassana tayi matu’kar mamakin yanda iyayenta suka kar6eta batare da sun nuna matsanancin fushi akantaba.

Tayi mamakin yanda Daddy ya umarci data wuce d’akinta tayi wanka kuma tacigaba da istigifari domin shi Allah gafurun rahimunne.

Haka tawuce d’aki sukuku kamar kazar da kwai ya fashemawa a ciki.
Tana shiga d’akin kuwa tafad’a kan gado tafashe da wani sabon kuka dan tunowa datayi da Hussaina wacce tare sukayi rayuwa a d’akinnan amma yanzu gashi bata raye.
Zuby tafad’o mata arai, a zuciyarta ta rin’ka banka mata Allah ya isa dan duk halin datashiga itace sila, sannan kuma taraba ‘yar’uwarta da duniya.

Love u all my Fan’s ????????
[2/19, 7:07 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….48

® TALENTED WRITER’S GROUP (TWG) ????

         *Bayan Sati Biyu*

Zaune yake yahad’a uban tagumi duk abubuwa sunbi sun dagulemai, ba abinda yake tunani sai tsawon lokacin da suka d’auka suna zaman aure da Hassana wadda duk a tunaninsa Hussainace wai ashe Hussainar ce ta mutu ba Hassanaba, wasu siraran hawaye suka zubo kan kumatunsa, beyi ‘ko’karin gogewaba haka yabarshi yanata zuba wani na bin wani.

Sallamar da ake dokawa daga bakin ‘kofar falon ce tasa yayi saurin goge hawayen dake fuskarsa tare dayin ‘karfin halin amsa sallamar.

Yauma kamar kullum sanye take cikin irin matsiyatan kayan data saba sanyawa, duk illahirin surar jikinta a bayyyane take.

Da mamaki yabita da idanu yana kallonta ganin wani shu’umin murmushi datake sakarmai, kafin yayi magana ta ida ‘karasowa cikin falon ta zauna kan d’aya daga kujerun dake zagaye da falon sannan ta d’ora ‘kafa d’aya kan d’aya kafin tafara magana.

“Da farko dai jabeer ina ‘kara yima ta’aziyyar matarka Hussaina data rigamu gidan gaskiya, sannan kuma ina jajantama game da cin amana da suka ‘kullama tsakaninta da ‘yar’uwarta sukasa kayi AUREN TAGWAYE batare da saninkaba.

Ta numfasa sannan taci gaba da magana “kada ka damufa da wannan Allah be ta6a kama bawansa da laifin da besaniba (niko zee nace kaji su zuby kamar ansan Allah)

Jabeer kuwa tunda tafara surutunta ‘kala be cemataba ita kad’ai keta zuba shikuwa binta kawai yake da ido.

Tasowa tayi daga inda take zaune tana wani girgiza tana rangaji harta ‘karaso gabanshi ta dur’kusa.
“Jabeer akwai wata magana danazo da ita amma bansan ya zaka d’auketaba.
Tayi shiru tare da zubamai mayataccin idanunta alamar tanason jin tabakinsa kafin tacigaba.

“Ina jinki kawai jabeer yabata amsa atakaice sannan tacigaba damagana,

“Jabeer na dad’e ina dakon soyayyarka acikin zuciyata tun kafin ka auri Hussaina, ganin tana aminiyata yasa na ha’kura ban ta6a nunamaba, domin masu iya magana sunce ana barin halak kodan kunya, amma yanzu tunda babu ita, kaga zaka iya aurena in mayema gurbinta, kuma……….

Saurin d’aga mata hannu yayi “dakata dan Allah zuby, yafad’a cikin ‘kunar rai, dan tunda tafara magan-gamunta jiyake kamar tana watsa mashi garwashin wuta acikin zuciyarsa.
“Kada ki kuma tunkarata da wannan maganar danni yanzu ba abinda ke gabana kenan ba, zuby kisani na tsani rayuwa da wata mace a yanzu saboda haka kada kisa ran zan iya rayuwa dake…….

Murmushi tayi “Hmm nasan ciwon abinda Hussaina tayimakane yasa ka furta wannan kalamin, amma mata ai mune abokanin rayuwa, babu namijin da baya bu’katar mace kusa dashi matu’kar yanada cikakkiyar lafiya…..

“Fita dan Allah, ki fitarmin daga gida kina 6atamin lokaci, yafad’a yana nuna mata ‘Kofa,

Murmushin takaici Zuby tayi a zuciyarta tace “wannan wane irin zuciyane dashi tun bayan wata biyu dasuka wuce naketamai hannunka me sanda dan yagane ina sonshi, gashi har yau na bud’a baki na gayamashi sirrin dake raina amma gashi yana nuna halin ko inkula akaina, tabbass akwai aiki babba agabana…….

“Get out, maganar jabeer ce tadawo da ita daga dogon tunanin datake, wacce har saida tayi ‘yar’karamar razana, sannan ta kalleshi ta jefeshi da murmushin takaici kafin tasa kai tafice daga gidan.

Tana fita yabi bayanta, megadi na zaune bakin aikinsa, ganin jabeer yasashi tasowa yana mashi barka da fitowa, fuska ba annuri jabeer yace “daga yau idan ka kuma barin wannan yarinyar shigowa gidannan bakin aikinka…

Me gadi yayi saurin dafe ‘kirji tare da fiddo idanu waje, jin an ambaci aikinsa, jiki na kyarma yace “inshaAllah ranka ya dad’e hakanma bazata faruba.
Be tsaya sauraronsaba yakoma cikin gidan, yana Shiga falo yafad’a kan kujera, tinanin rayuwar da yayi da Hassana tafad’o mashi a rai.

Love u all my Fan’s ????????
[2/19, 8:15 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….49

® TALENTED WRITER’S GROUP (TWG) ????

Tundaga wannan lokacin Zuby ke zarya gidan jabeer amma koda wasa me gadi baya barinta Shiga, idan zatayi juyin duniyar nan be barinta, data gane haka saita koma zuwa office d’insa, nanma Haka ya gargad’i ma’aikatan gurin da kada akuma barinta tana shigowa, haka kuwa akayi dan akwai ranar datazo tundaga bakin get megadi yahanata shigowa, tayi magiyar tayi duk iya dabararta amma yahanata, kawai saita samu guri ta zauna tana kallon masu shiga da masu fita har bayan azahar bataga fitowar jabeer ba sai gurin ‘karfe ukku sannan motarshi tafito, hannu rafara d’aga mashi Alamar ya tsaya, shi kuwa bemasan tana gurin ba.

Ganin be gantaba yasa tayi saurin tsaida me napep tanunamashi motar jabeer tace yabi bayanta,

Shikuwa besan tana binsaba, kai tsaye hanyar gidan iyayensa yanufa, dai-dai ‘kofar gidansu yayi parking sannan yafito duk kan idanunta ya gaggaisa da mutanen dake gurin sannan yashige gidan nasu.

Bata fito daga napep d’inba wani yaro yazo wucewa takirashi, take tambayarsa ko nanne gidansu jabeer?

Yaron yabata amsa atakaice sannan ya wuce, nan ta umarci me bapep daya kaita gida tagaya mai unguwar suka d’au hanya.

    *Bayan kwana biyu*

Zuby tsaye bakin titi jikinta sanye da riga da zani na atamfa wanda rabon datasaka kaya irin wannan harta manta, sai kuma madai-daiciyar hijab d’inda tasanya wacce ta sakko mata har iya gwiwa.

Me napep ta tsaida, sannan tafad’a mashi inda ze kaita, suna isa ta hango motar jabeer a ‘kofar gidan haka ya tabbatar mata da yana cikin gidan, zaure ta tsaya tana fargabar shiga amma haka ta dake tayi ta maza tayi sallama, Maman jabeer dake duke bakin gurin tana alwala ita ta amsa sallamar.

Cikin ladabi zuby tashiga gidan, Maman jabeer tabita da idanu da Alamar tambaya tattare da ita dan bata ta6a ganin zuby ba.

Ganin yanda Zuby ke kakkare fuska da Alamar jin kunya yasa Maman jabeer d’in tayimata iso har d’aki, bayan sun gaisa take tambayarta “yarinya bangekiba,

Murmushi Zuby tayi “dama jabeer ne yace ze kawoni mu gaisa, to shine mukayi waya nake fad’amashi inanan gidan yayata nan ‘kasan layinku sai yake sanarmani ai yana nan gidan in’karaso mu gaisa, takare maganar tana saddar da kanta ‘kasa alamar kunya, dan tunda tazo bata yarda sun had’a ido da Maman jabeer d’inba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button