BABU SO HAUSA NOVEL

AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

Murmushi momy tayi “ba kome kije mana, amma kibari yanzu daddynku ze dawo, idan yadawo yaci abinci yafita, kekuma saiki shirya gurin ‘karfe ukku saiki tafi, amma ki tabbatar da lokacin tashinku islamiyya yayi kidawo gida, “inshaAllah Momy aini kinsan banida matsala yanda nake tsoron Daddy inwuce mana ya 6allani cikin gidannan, murmushi Momy tayi “ah to nidai nagayamaki wlh.

Dai-dai lokacin kuwa daddy ya dawo Momy da Hassana sukayimashi sannu da zuwa, Momy ta kar6i jakar hannunshi suka wuce d’akinsa, bayan wani d’an lokqci suka fito tare daddy ya canja kaya da Alama wanka yayi, zama sukayi kan dining Hassana tayi serve d’insu bayan sun kammala cin abinci suka d’an ta6a fira, cikin firar tasune daddy ya kalli Hassana “watako kedai kin’ki fiddo miji kiyi aure ga ‘yar’uwarki takusa wata d’aya a gidanta,

Momy ce tace “Alhj to a ina zata samu mijin kullum tana ‘kunshe a cikin gida, bata fita ko nan da can, yaushe wani ze ganta yace yanaso, indai ba itama irin na ‘yar’uwarta zakamata ba.

“No no Hassana bazan ta6a yimata abinda nayima Hussainaba, saboda nutsuwarsuma ba d’ayaba,
“To Allah dai yaza6a mata miji nagari, Momy tafad’a daddy ya amsa da “Ameen ya rabbi.
Sannan ya kalli Hassana “ki shirya yanzu idan zan fita in saukeki kigano ‘yar’uwarki.

Wani irin tsalle tadaka cikin Farin ciki tanufi d’akinsu domin ta shirya.

A gaggauce tafad’a toilet ta she’ka wanka tana fitowa tashafa ainafin cream d’inta coa-coa butter sannan ta murza farar powder, man le6e kawai tashafa sannan tanufi wadrope ta d’au’ko wasu kaya riga da zani d’inkin simple ta Sanya, dan tasan daddynsu baya ‘kaunar 6ingilallun kaya da matsatsen siket koda ta sanya zesa taciresu.
Wani madai-daicin hijab ta saka sannan tafito nan sukayima Momy sallama suka wuce, momy har cikin ranta taji dad’in zuwan Hassana gidan Hussaina da Amincewar Alhjn, dan ita dama tun abinda Hussaina tayi take tsoron bada izinin zuwa wani guri batare da saninsaba, duk da tasan Halin Hassana yasha ban-ban dana Hussaina.

Dai-dai ‘kofar gidan jabeer daddy ya sauke Hassana sannan ya ciro dubu d’aya yabata “ga wannan kihau napep ‘karfe shidda tayimaki gida, “to daddy nagode Allah kiyaye hanya,
Nocking d’in gidan tayi me gadi yataso yana tambayar waye tare da le’kowa ganin Hassana yasa yayi saurin bud’ewa tare da dur’kusawa ya gaisheta “Hajiya sannu da dawowa, wallahi banma kula da lokacin da kika fitaba, murmushi Hassana tayi dan tagane inda maganganun me gadin suka dosa a tunaninsa Hussainace, “Ba me gidan bace ‘kanwartace tafad’a tana ‘kara fad’ad’a fara’arta.
“To ikon Allah Amma kamarku tayi yawa gashi girmanku d’aya ba wanda ze iya ban-banceku, Allah me iko…..yafad’a yana ri’ke da baki.

Nan Hassana tawuceshi tabarshi cike da mamaki, yana wasi-wasi “Anya ba me gidan bace tafita, wata kila bataso asan tafita shiyasa tace ba itabace, amma in bacin haka ai kamar tayi yawa kome iri d’aya hatta da maganarsu ba ban-banci.
Wannan ai saiku rikita me gidan yakasa gane wacece tashi acikinku.
????

Zaune Hussaina take kan d’aya daga kujerun falon hannunta ri’ke da remote tana kallon wata wa’kar turanci a tashar music plus, wasu had’ad’un Riga da wando na Pakistan ne jikinta tasa gyalen kayan tayi rolling, ga ‘kamshin wani had’adden turare dake tashi jikinta, kafarta sanye da takalmi plate me masifar kyau, gefe kuma ‘yar’karamar jakartace wacce tazuba kayanta kala biyu a ciki, jiran zuwan Hassana kawai takeyi tatafi gurin Rabin ranta Hafiz dan tun d’azu yake kiranta a waya gani yake kamar bazatazoba.

Agogon wayarta ta duba ‘karfe bud’u dai-dai gashi har yanzu Hassna batazoba wani guntun tsaki taja tare da lalubo sunanta ta danna kira sai jiyo ringing d’in wayar tayi a dai-dai kofar shigowa da sauri takai dubanta gurin ido hud’u sukayi da Hassana batasan lokacin data buga wani irin tsalleba cike da farin ciki ta makaleta “oyoyo my sister.

Tofah Readers me Hussaina ke shirin aikatawane, Me take nufi da son zuwan Hassana gidanta, wace shawarace Zuby tabata duk kubiyo Zee Elkaseem (Mmn khady) yar mutan KATAINAWA domin samun cikakkiyar amsa a cikin littafin AUREN TAGWAYE

Love u all my Fan’s ???????? shoki ???????? ????????‍♀????????
[1/15, 10:28 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….27

Cike da farinciki suduka suka fad’a kan kujera, Hussaina ta kalli Hassana wlh sister na d’auka bazakizoba harna fara cire rai,

“Injiwaye inanan tafe ai,
“amma naji dad’in zuwanki wlh, dariya Hassana tayi “lallai sister aurennan ya kar6eki kinga kuwa yanda kikayi kyau kikayi wani fresh, kamar kinje wata ‘kasar Honey moon, dariya Hussaina tayi tare da kaimata duka cikin wasa “kai sister bakida dama, nidai yanzu bari nafara kawomaki lemu kisha idan kuma kina bu’katar abinci ga kitchen nan zaki iya shiga ki girka dan kema gidankine, bata jira jin abinda zata fad’ba tanufi kitchen tabud’e fridge domin d’aukoma sister dinta lemun.

Bayan shigarta kitchen kuma idon Hassana ya sauka kan jakar dake gefen Hussaina ajiye, hannu tasa ta d’auko jakar tare da zuge zip d’in ganin kayan sawa cikin jakar dakuma yan abubuwan bukata yabata mamaki, bata kai ga rufe jakar ba Hussaina ta dawo d’akin d’auke da lemu da cup d’in glass a hannunta ta ajiye gaban Hassana.

Kallonta Hassana tayi sannan ta tambayeta “sister wannan kayanfa na waye? Matsowa Hussaina tayi ta kar6i jakar ta rufe ta ajiye gefe sannan ta zubo lemun a cup ta mi’kamata “kar6i sister kisha zanyimaki bayanin kona miye….

Ba musu Hassana ta kar6i lemun ta shanye sannan ta kalli Hussaina “uhum ina jinki.

Cikin muryar Neman Alfarma Hussaina tafara magana “dan Allah sis wani taimako nakeso kiyimin wanda duk duniya nasan ba wanda zeyiminshi sai ke.
Cike da mamaki Hassana ke kallonta “ina sauraronki sister wane taimakone wannan?

Matsowa Hussaina ta’karayi kusa da ita “ba wani abu bane me wuya inaso ki zauna a gidannan a matsayina…..

“What? Hassana tafad’a tare da mi’kewa tsaye “me kike cewa sister ban fahimci inda zancenki ya dosaba, kama hannunta Hussaina tayi tare da maidata kan kujera ta zaunar da ita “plz sister ki saurareni mana nasan zaki fahimci inda zancena ya dosa.
“Ina jinki Hassana tafad’a tare da bin yar’uwar tata da kallo.

Hussaina tacigaba da magana “kamar yanda nafad’a inaso ki zauna a gidannan a matsayin nice, ba dad’ewa zakiyiba kwana biyu kawai zakiyi, kuma ni zaki taimaka.

“Kamar ya in taimakeki wannan abinda baze ta6a yiyuwa bane yaushe za’ace wani yayima wani zaman aure, aurefa ba abin wasa bane.

“Hmm sister dan Allah ki taimakamin inshaAllah ba abinda ze faru kuma ba Wanda ze gane, sanin kankine babu Wanda ke bam-banceni dake, ko Momy da daddy suna ban-bancemune ta gurin halayyarmu amma bata kamaninmuba.

“Dakata sister duk ba wannan ba, shin idan na zauna gidannan amatsayinki kekuma ina zaki?
“Yauwa sister tambayar dayakamata kiyimin kenan.
“Wata ‘kawatace zatayi aure shine ta gayyaceni to na tambayi jabeer ya Hanani kuma yace idan nasake tunkararsa da maganar ze gayama daddy, to nikuma yanda nike da ‘kawar tawa yawuce ace ta gayyaceni bikinta banjeba,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button