BABU SO HAUSA NOVEL

AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

“To shine kuma baki iya zuwa rana d’aya ki dawo?
“Baze yiwu inje rana d’ayaba saboda ba nan garin bane.
“Wane garine? Hasana ta tambaya.
“Yar Kaduna ce, kuma kinsan nisan katsina zuwa Kaduna, kuma daga can Abuja zamu kai amarya kinga dole inkwana biyu.

Tana kaiwa nan a zancenta wayarta tashiga ringing tana dubawa taga sunan Hafiz gabanta yayi mummunan fad’uwa da kamar bazata d’agaba ganin Hassana ta tsareta da ido yasa ta d’aga “Heelow dan Allah kiyi Ha’kuri bani nacemiki zanzoba to yanzu haka wayar damuke ina hanya. Bata jira me Hafiz ze fad’aba ta tsinke wayar.
“Kinganiko sister wallahi tund’azu takemin waya, Amaryar cefa.

Hassana cikin sanyin jiki tace “shikenan na amince zan Zauna amatsayinki “Amma ba nan gizo ke sa’kar ba ya zamuyi da daddy da Momy kinsan dole zasu nemeni……

Saurin katseta Hussaina tayi tare da dafa kafad’arta “indan wannan kada kidamu, ni zantafi da wayarki zan barmiki tawa koda su daddy sunkira nasan bayanin dazanyimasu.

“To shikenan Hassana tafad’a, kawai dai ta amince da bu’katar ‘yar’uwar tata badan komeba sai dan taga yanda ta masifar shiga damuwa, amma can ‘kar’kashin zuciyarta cike take da tsoro da fargabar abinda suke shirin aikatawa.

Nan Hussaina ta ‘kar6i wayar Hassana ta kwafi Number Hafiz tasaka a wayar Hassana, wacce ke wayarta kuma tasata blacklist tare dayin delete d’in number daga wayarta sannan ta baiwa Hassana wayar.

Nan ta d’auki jakarta sukayi sallama da Hassana tatafi, tana fita takira Hafiz da number Hassana tafad’amashi tana hanya kuma idan ze kirata da wannan number ze kirata dan tabar waccan a gida.

Love u all my Fan’s ???????? shoki ????????‍♀????
[1/17, 9:19 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….28

Gabanta yashiga dukan tara-tara a zuciyarta tarin’ka tunanin taya zatayi zaman aure da mijin ‘yar’uwarta, bayan ba mutuwa tayiba, kuma ba rabuwa sukayba, lallai Hussaina tasakata matsala sai yanzu takejin dama bata amince da ‘kudirintaba, amma yanzu aikin gama ya gama dole ta zauna tarufama ‘yar’uwarta asiri har lokacin dazata dawo, da wannan tunanin taji ana kiraye-kurayen sallar magrib saboda haka da sauri tanufi bedroom tashiga toilet ta d’auro Al’wala ta kabbara sallah, bayan ta idar da sallar ta dawo falo tsayawa tayi tana tunanin yanda zata fara aiwatar da ayyukan gidan dan da Alama Hussaina duk yau bata gyara gidanba,

Sharar falon tafarayi, tare da yin mopping, sannan tasaka wani ‘karamin towel me haske ta goge TV, center table, dakuma dining da sauran guraren da yakamata a goge, bayan ta kammala nan takoma bedroom, ta gayara tashare tare da canjama gadon bedsheet, lokaci guda gidan yayi fes kamar bashiba, freshner ta d’auko me dad’in ‘kamshi ta feshe ko’ina hatta da toilet saida tagayara ta fesa freshener abin gwanin sha’awa gidan sai yakoma kamar wani Sabin kaya aka zuba saboda tunda yake Hussaina bata ta6a gyarashiba, kullum saidai ta 6ata.

Bayan ta kammala wannan kitchen tanufa nanma tsayawa tayi tana tunanin me zata dafa, dan tasan duk inda me gidan yake yana gab da dawowa duk da batasan lokacin dawowar tasaba, ta dad’e haka daga ‘karshe ta yanke shawarar dafa abu mai sau’ki dan dare yafara gashi anata kiraye-kirayen sallar isha’i.

Jalouf d’in kus-kus ta dafa wanda yaji kayan lambu da kayan ‘kamshi, sannan tayi amfani da tsoka nama zallah ta yankata ‘kanana aciki yanda ze zamana duk lokacin da wanda zeci ya ebo yakai baki ze had’o da naman, dayake kus-kus ne cikin minti ashirin ta kammala dahuwar ta juye a flask, tare da had’a zo6o had’add’e shima sai ‘kamahin flavour yake ta jera kan dining.

Bedroom takoma tafad’a toilet ta she’ka wanka, bayan tafito bata wani 6ata lokaci gurin yin kwalliyaba lotion kawai ta murza tare da ‘yar hoda sai man le6e, wadrope tanufa ta d’auko wani had’adden less d’inkin Riga da siket ta sanya, wow kayan kuwa sun masifar kar6ar jikinta kamar dama dan ita aka d’inkasu, duk wata sura ta jikinta ta bayyana.

Zama tayi falo tare da jawo wayar da Husaina ta barmata tashiga danne-danne, tana dubawa tashiga inbox bataga komeba, sannan tashiga chat nanma ba kome, dan Hussaina batabar komeba saida tayi delete, dan kada Hassana taga halin datake ciki.

** ** **

Daddy ne ke safa da marwa hannunshi ri’ke da waya yanata try number Hassana amma sai acemai switch off, abin na matukar bashi mamaki gashi kuma har ‘karfe tara na ‘ko’karinyi bata dawo gidaba, Momy kuwa hankalinta yayi ‘kololuwar tashi “innalillahi Alhj yanzu ina yarinyar nan tashige, anya kuwa lafiya dan bata ta6a yimana hakaba,

Juyowa daddy yayi ya kalleta shima Hankalinsa a tashe, yace “ni kaina ina mamakin hakan dan Hassana yarinyace me matu’kar tsoro da kiyaye fushinmu amma yau ace tawuce ka’idar dana gindaya mata,

Momy wacce idanunta suka fara kawo kwallah tace bari inkira number Hussaina inji idan Hassana ta taho, wayarta ta d’auko ta lalubo sunan Hussaina tanata ringing ba’a d’agaba dan ganin sunan Momy a wayar ba ‘karamin d’aga hankalin Hassana tayiba, dan tasan duk yanda akayi yanzu itada Daddy sunacan hankalinsu yatashi na rashin dawowarta gida, bata d’aga wayarba saida kiran Momy na hud’u yashigo sannan ta d’auka ta dannan OK tare da karawa a kunnenta saida ta dai-daita nutsuwarta sannan tace “Assalamu Alaikum.
A d’ayan 6angaren Momy cikin 6acin rai tace Hussaina kina ina inata kiran wayarki har kusan sau hud’u baki d’agaba.

Ba ‘karamin fad’uwar gaba Hassana tayiba, tare da daburcewa dan gani take kamar Momy zata iya ganeta.
“Uhn ah am…. Dama bani kusa da wayar ne sai yanzu naji.
“To dama tambayarki zamuyi shin Hassana ta taho gida kuwa.?
“Eh tataho momy ai tun d’azu ta taho tace daddy yace kada ta wuce ‘karfe shidda kuma biyar da rabi tabar gidannan.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un Momy tafad’a tare da fashewa da kuka, tama manta ko tsinke kiran batayiba, Hassana kuwa tsayawa tayi ri’ke da waya a kunnenta tana sauraren yanda Momy ke kuka tana gayama daddy cewa “tun ‘karfe biyar da rabi Hassana tabaro gidan Hussaina.
“Subhannallah Daddy yafad’a tare da cewa Allah bayyana mamu ita a duk inda take.

Tsinke kiran Hassana tayi tare da sake kiran Momy, ringing d’aya ta d’auka, Nan Hassana ke tambayar “Momy wai meke faruwane, naji kinkira kintambayeni nabaki amsa kuma kinsa salati.
“Hussaina ‘yar’uwarki Hassana har yanzu bata dawo gidaba kuma munkira wayarta switch off,

“Innalillahiwa’inna’ilaijirraji’un Hassana tafad’a tare da fashewa da kuka, kafin ta tsinke kiran.
A tunanin momy Hassana tana kukane saboda 6atan ‘yar’uwarta.
Itako Hassana kukan nadama da ba’kin cikin halin dasuka jefa iyayensu takeyi, sai yanzu take datasanin yarda da kud’irin ‘yar’uwarta.

Love u all my Fan’s ???????? shoki ????????‍♀. ????
[1/22, 6:47 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….29

Zaune take kan d’aya daga cikin kujerun dake zagaye da falon ta buga uban tagumi hannu bibbiyu, ba abinda take tunani sai halin da iyayenta suke ciki,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button