BABU SO HAUSA NOVEL

AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

A zahiri tayi magana “nidai bari inkira Hussaina tadawo gidanta nikuma inkoma gida in fuskanci kowane irin hukunci daddy zeyimin koda kuwa zefi na Hussainar tsanani, dan bazan iya zama cikin tunani da fargaba ba.
Wayarta ta jawo talulobo sunanta ta danna kira amma kuma cikin rashin sa’a sai akacemata wayar akashe, “ya salam tafad’a tare da d’ora hannu bisa kai nashiga ukku, tafad’a tare da mi’kewa tsaye “kodai inyi tafiyata idan tadawo tamasu bayanin inda taje, “kai bazan iyayima sister hakaba, muddin nasan daddy yaji labarin tayi wannan tafiyar kasheta kad’ai ne bazeyiba….
Wayyo ni Hassana ansakani tsaka me yuwa tafad’a tare da komawa ta zauna kan kujera jiki duk ba lakka.

Horn d’in mota taji gabantane yayi wani mummunan fad’uwa da sauri tanufi window tad’ga labulen tare le’kawa, me gadi ta hango yana ‘ko’karin bud’e get, bayan ya bud’e motar jabeer tashigo duk kan idon Hassana yayi parking sannan yafito hannunsa d’auke da jakarsa, da sauri takoma ta zauna sannan tayi ‘ko’karin dai-daita nutsuwarta dukda mummunan fad’uwar gaban datakeyi.

Da sallama yashigo falon, Hassana na Zaune jikinta sai kyarma yake tana tunanin wace irin tarba zatayima mijin ‘yar’uwar tata, da kyar tasamu ta dai-daita nutsuwarta tare da mi’kewa ta dur’kusa ta kar6i jakar hannunshi tana mashi sannu da Zuwa, jabeer kuwa tsananin mamakine ya lullu6eshi yayi tsaye inda yake yakasa motsawa yayinda itakuma Hassana ta dad’e da shigewa d’akinsa domin ajiyemar jakarsa.

Murmushi yayi a Zuciyarshi kuma yace “ikon Allah, yau kuma ni Hussaina kema wannan tarbar, bin ko’ina na falon yayi da kallo ya ganshi fes-fea ba kamar yanda yasaba ganinshiba kullum kace-kace, sannan tunda yashigo daddad’an ‘kamshin girki dana freshner sun had’u sun dakar mai hanci, lumshe idonshi yayi tare dayin wani guntun murmushi sannan yanufi d’akin dai-dai Hassana itakuma zata fito daga d’akin kad’an yarage suyi karo da juna Hassanar tayi saurin ja da baya duk tawani daburce “um ga ruwan wanka can nahad’ama “To, kawai jabeer ya iya amsawa dashi tare da binta da kallon mamaki sannan ya wuce Zuwa toilet d’in, tana ganin shigarsa tayi saurin zuwa wadrope ta fiddo mashi ‘kananan kaya marar nauyi tare da ajiyesu gefen gado sannan tafita zuwa falo.

: Yana fitowa daga wankan yayi tozali da kayan da Hassana ta ajiyemai murmushi yayi saida ya murza mai sannan ya d’auki kayan ya sanya tare da feshe jikinsa da daddad’an turarensa, sannan yafito zuwa falo, zaune take kan kujera da waya hannunta tund’azu number Husaaina kawai take try amma switch off, dan tunda jabeer yadawo hankalinta yayi matu’kar tashi jikinta keta kar-karwa tsoronta d’aya kada jabeer yagane ita ba matarshi bace.

Da sauri ta tashi tana mashi sannu da fitowa, tanufi dining ta zauna sannan ta kalleshi “bissmillah mana tafad’a tare da gyaramashi kujerar daze zauna, ba musu yazo ya zauna yana binta da kallon mamaki danshi har yanzu abubuwan dake faruwa ganinsu yake kamar a mafarki wai yau shine Hussaina ke tarairaya haka lallai da walaki amma koma miye ba yanzu yakamata in tambayetaba.

Yana cikin wannan tunanin harta zubamar abincin ta ajiye gabanshi sannan itama ta zuba nata, haka suka faraci dad’in abincin na ratsa jabeer har tsakiyar kanshi, a zuciyarshi yana cewa “yaushe rabon dayaci abinci me dad’in haka kullum yana hanyar zuwa restaurant,

Da misalin ‘karfe tara da rabi na dare suna zaune falo kowanensu yayi ahiru wani Indian film suke kallo a tashar zee cinema, da Alama film d’in yayima Hassana kyau dan ta maida hankalinta kaf kan film din, yayinda jabeer bacci yacikamar ido, sai hamma yake d’aya bayan d’aya tasowa yayi daga kujerer dayake yazo inda Hussaina take zaune Yakama hannunta “Taso muje mu kwanta, wani mummunan fad’uwar gaba taji tayi saurin kwace hannunta Daga nashi tace kaje ina zuwa saina ida kallon wannan film d’in.

Juyawa yayi ya kalli TV cike da mamaki dan yasan Hussaina bata ta6a yimar musuba idan ya umarceta dasu kwanta, kuma da kallo be dametaba, da wannan tunanin ya wuce d’aki yayi kwanciyarsa kasancewar akwai gajiya jikinsa bacci yayi gaggawar d’aukarsa.

Love u all my Fan’s ????????????????????????
[1/26, 10:09 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….30

Husaaina kuwa bayan ta isa gidan Hafiz, cike da murna da jin dad’in zuwanta ya tarbeta, tana isa takira Zuby a waya, ringing d’aya zubyn ta d’auka dama jiran kiran takeyi.

“Hellow ‘kawata Zuby tafad’a cike da ‘kagara taji abinda Husaainar zata fad’a mata.
“Kawata naji dad’in shawarar da kikabani dan yanzu haka ina tare da mutumin,
Dariya zuby tayi a ranta tace “Zaki gane kurenki zaki gane da zuby kike magana.
Amma a zahiri sai tace “ai dama nagayamaki hakan kawai zakiyi kije inda ranki keso kiyi ko kwana nawa kikeso batare da wata matsala ba.
“Ai shiyasa nake masifar sonki ‘kawata Hussaina tafad’a.
Zuby tace “ai nima banida kamarki shiyasa kullum nakeson ki kasance cikin farin ciki, da haka sukayi sallama, kowace ta ajiye wayar

Wata mahaukaciyar dariya zuby tayi tare da tafa hannu ” yarinya kinshiga tarkona kad’an yarage in cimma manufata akanki,
Wata sabuwar dariya ta’kara kafin tasha mur kamar bata ta6a dariyaba “Hussaina ina me tabbatar maki yanda kika baro gidan jabeer kin barshi kenan Har abada.

Hussaina kuwa bayan sun gama waya da zuby toilet tashiga ta she’ka wanka, bayan tafito tabi jikinta da lafiyayyen lotion dinta tashafa kayan jikinta ta maida sannan tadawo falo ta zauna tana jiran shigowar Hafiz dan bayan sallar isha’i yafita yo masu take a way.

Be dawo gidanba sai ‘karfe tara da rabi lokacin Hussaina nadai zaune kan kujera a falo sai hamma take jerawa d’aya bayan d’aya, ga yunwa na addabarta ga kuma wani irin bacci dake fizgarta

Da sauri Hafiz ya isa gareta tare da ajiye ledar dake hannunsa gabanta, “sorry babyna na dad’e ko? Ya tambaya yana kallonta yanda take lumshe idanu da Alamar jin bacci tattare da ita.

“Uhm, kawai tace tare da ‘Kara gyara zamanta kan kujerar datake, “sorry sorry babyna tafad’a tare da nufar kitchen, bayan yan mintoci ya fito hannunsa d’auke da plate da cukulla da cup’s, gabanta yazo ya ajiye sannan yazuba masu abincin, da sauri Hussaina ta fara ci saida taji tayi dam sannan ta kora da lemu, toilet tanufa ta wanke bakinta tadawo kan kujerar datake tad’an kishingid’a cikin mintina biyar bacci yayi awon gaba da ita.

Hafiz Kuwa bayan shima ya kammala cin abincin tattara plate d’in yayi da cup’s ya mayar kitchen sannan ya wuce bedroom yafad’a toilet yashe’ka wanka yana futowa ya shafa cream wasu tare da feshe jikinsa da turare, jikinsa sanye yake da vest da shortnicar falo yanufa har yanzu Hussaina na kwance inda yabarta kan kujera sai sharar baccinta takeyi,

Tsayawa yayi kanta saida yakaremata kallo, take wata matsananciyar Sha’awarta ta d’arsu a zuciyarsa ahankali yakai hannunsa jikinta yafara shafata yana mata irin salon dayasaba tayar mata da hankali.

Can cikin bacci taji ana ta6ata saurin bud’e ido tayi tare da saukesu kan Hafiz dake aikamata sakon wani shu’umin murmushi, ture hannunshi tayi daga jikinta “miye haka kake shirin aikatawa kasanfa da da yanzu ba d’aya bane, yanda nasaki jiki dakai a da nabaka duk abinda kakeso yanzu baze yuyuba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button