BABU SO HAUSA NOVEL

AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

Jitayi dukta tsargu da kallon dayake mata, ba ‘karamar dauriya tayiba lokacin data iso taja kujera d’aya ta zauna sannan ta fara zubamar kalacin duk illahirin jikinta kyarma yake.

Haka suka fara breakfast d’in bayan sun kammala ne jabeer ya kalli Hassana yace “waini Hussaina kwana biyu naga kin canjamin kinayimin duk wani Abu dakikasan ze faranta raina sa6anin da davaki damu da damuwataba.

Murmushi tayi “kada ka damu mijina kasan Allah ba yanda baya sauya Al’amarinsa jiya ina zaune ina kallon TV aka sanyo wani malami yana wa’azi, to wa’azin dana tsaya na saurara sainaji kamar hallayatace kaf yake zayyanawa sannan kuma tafad’i irin azabar da Allah yatanada ga mata masu irin halayyarmu shine nikuma abin yad’agamin hankali.

Cike dajin dad’i jabeer yace “kai amma Allah yayima wannan malamin Al’barka
Hassana ta amsa da “Ameen.

Shiru yad’an ratsa nayan mintittika kafin jabeer ya’kara magana karo na biyu “to amma malamin beyi magana kan matar dake “kauracewa shimfid’ar mijintaba dakuma irin azabobin da Allah ya tanadar mata.

Love u all my fan’s ???????? shoki ????????
[1/30, 9:01 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….33

® TALENTED WRITER’S GROUP (TWG) ????

Shiru Hussaina tayi dan batada cikakkiyar Amsar dazatabashi akan wannan tambayar da yayimata, ganin batada niyyar magana yasashi mi’kewa tare da d’aukar jakarsa “ni zan wuce wurin aiki “Allah kiyaye hanya kawai tacemasa batare data motsa daga inda takeba.

Yana fita ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya da sauri tanufi bedroom waya ta d’auko ta shiga laluben sunan Hussaina sannan ta danna kira cikin sa’a kuwa tasamu wayar na ringing amma harta tsinke ba’a d’agaba, batayi ‘kasa a gwiwaba ta’kara kira karo na biyu nanma tanata ringing sai gab da zata tsinke sannan aka d’aga
“Hussainace tafara magana Hellow sister ai ganinan ina shiri inshaAllah yau zandawo yanzuma bada dad’ewaba.

Wata ajiyar zuciya Hassana tayi “nidai dan Allah ki dawo kinga muna shiga hakkin mijinki saboda na kula irin mutanennane mabu’kata nikuma kinga ba yanda za’ayi inbiyamasa dan Allah ki dawo saboda gudunmatsala.

Kada ki damu sister inshaAllah yau zandawo “To shikenan tafad’a tare da ajiye wayar kan mirror datake kwalliya gabanshi,
gefe kuma ga jakar kayanta da sauri tagama kwalliya sannan ta jawo jakar taciro wani riga da zani na atamfa ta sanya sannan ta d’aura d’ankwalin kayan wata madaidaiciyar hijab tasaka sannan takoma bakin gado tazauna tana jiran dawowar Hafiz, tund’azu yafita be dawoba shi kawai take jira gashi har ‘karfe sha d’aya da mintittika, ‘kara duba agogon wayarta tayi lokaci naja wani d’an guntun tsaki tayi tare da ajiye wayar gefenta ta sadda kanta ‘kasa tunanin yanda zasuyi Hassana takoma gida batare da wata matsalaba takeyi dan tafi kowa sanin halin daddy.

Wata zuciyar tace ki kira zuby tunda itace tabaki wannan shawara itakad’ai kuma zata baki shawarar yanda za’ayi Hassana takoma gida batare da ansamu wata matsalaba.

Murmushi tayi tare da mi’kewa dan d’auko wayarta, gabantane yayi wani mummunan fad’uwa lokacin dasukayi ido hud’u da ita, sanye take cikin wani matsatstsen wando da wata figigiyar riga wacce da kad’an tawuce ‘kugunta sai wani yabud’ad’d’en gyale datayi rolling dashi fuskarta ba Alamar fara’a ko kad’an.

Cike da mamaki Huasaina ta kalleta tare da fad’uwar gaba, dakewa tayi ta tanufo inda take tsaye ta maida hannuwanta baya tanayima Hussaina wani shu’umin kallo.

“Naji dad’in zuwanki ‘kawata kamar kinsan dama yanzu nake ‘ko’karin kiranki, Hussaina tafad’a tana fad’ad’a murmushin dake fuskarta.

‘Kara d’addaurewa Zuby tayi ba Alamar wasa tattare da ita, duk da haka Hussaina daurewa tayi tacigaba da kusanto inda zuby take, batayi auneba sai jitayi zuby ta hankad’ata iya ‘karfinta tayi taga-taga zata fad’i da kyar tasamu ta daddafe ta kalli zuby wacce ke ‘kara tinkarota har yanzu dai hannunta d’aya na bayanata, ‘kara Hankad’a Hussaina tayi iya ‘karfinta wannan karon saida tayi nasarar kayar da ita.

Wata irin fad’uwa Husaainar tayi kanta ya bugu da gefen gado take gurin yafashe yafara zubar jini, Hannu Hussaina tasa ta dafe gurin tana kallon zuby dake tunkarota Hannunta ri’ke da wani ‘katon icce.

Cike da tsoro da fargba Hussaina ke ‘ko’karin mi’kewa dan samun matsera dan taga Alamar ba wasa ko kad’an a idon zuby kuma ba Alamar d’igon imani tare da ita.

Ganin Hussaina na ‘ko’karin mi’kewa yasa Zuby d’aga iccen dake hannunta ta kwantarama Hussaina akai, nan take ta zube jini yagama wankemata fuska, ta kalli Zuby cikin ‘karfin hali da kyar ta iya d’aga bakinta tayimata magana.

“Zuby me nayimaki kike neman kasheni, mena tsaremaki a rayuwa?

Wata mahaukaciyar dariya zuby ta gagga6e da ita sannan ta d’addaure kamar bata ta6a dariyaba, sannan ta du’ko dai-dai inda Hussaina take kwance male-male cikin jini tana maida numfashi da kyar tace “Kin taremin kome a duniya Hussaina na dad’e ina ba’kincikin kasancewarki d’iyar masu kud’i nikuma d’iyar talakawa wad’anda talauci yayima kanta.

Sannan na dad’e ina mutuwar son Hafiz beta6a nunamin soyayyaba dai-dai da rana d’aya sai dai yana biyan bu’katarshi dani aduk lokacin daya bu’kaci hakan.
Amma lokaci guda ya nuna ba wacce yakeso sai ke, tafad’a tana nunata da yatsa.

Sannan tami’ke tsaye tayi taku biyu zuwa ukku “ban ‘kara shiga tashin hankaliba sai ranar danaje gidanki mijinki yayimin kyautar kudad’e masu yawa tundaga lokacin naji ba wanda nakeso samada mijinki jabeer kuma naci Al’washin sai yazama mallakina.

Na zauna nayi tunani nayi nazari naga ba yanda za’ayi insamu biyan bu’kata saita hanyar kawar dake daga doron duniya.

Hussaina najin haka wani irin kuka da nadama sukazomata lokaci guda.

Zuby kuwa ba tausayi ba imani tacigaba da bugun Hussaina aka da wannan ‘katon iccen saida ta tabbatar da babu sauran numfashi tattare da ita sannan tayi saurin barin gidan.

Love u all my Fan’s ????
[1/31, 9:13 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….34

® TALENTED WRITER’S GROUP (TWG) ????

Gaisuwa gareku masoyan wannan littafi wannan shafin nakune Mummy Ramadan da Bilkisu Mu’azu (Bilma) Allah bar ‘kauna yakuma raya maku yaranku bisa tafarki na Addinin musulunci

Da musalin ‘karfe biyar na yamma Hassanace Zaune itada jabeer sai janta yake da fira amma ita kwata-kwata hankalinta baya gurinsa itadai fatanta d’aya Hussaina tadawo itakuma ta koma gida dan yau ya kasance weekend jabeer be fita ko’inaba tun safe yake gida sai wani shu’umin kallo dayakebinta dashi.

Wayarta ta jawo tacigaba da try number Hussaina wacce tun misalin sha d’aya na safe daaukayi waya ta gayamata tana hanya, tundaga lokacin kota kira sai tayi ringing tagama ba’a d’agaba, yanzu kuwa data kira cemata akayi (switch off) kashe take baki d’aya hankalinta ya’kara tashi ga jabeer yatasata gaba da Alama yanada bu’kata.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un ta furta tana ‘ko’karin ‘kara try number Hussaina lokacin jabeer ya’karaso inda take zaune shima zama yayi kusa da ita har jikinsu na gugar na juna, Hannu yasa ya kar6e wayar tare da jawota yahad’ata da jikinsa “wai tund’azu wa kike faman kira haka kinbarni ni kad’ai sai fira nakemaki amma Sam hankalinki baya gurina yafad’a tare da ajiye wayar kan centre table, itakuwa Hassana yana Had’a jikinta da nashi jikinta yahau 6ari, kyarma take kamar mazari, shikuwa jabeer shiga yayi cikin wani irin yanayi me wuyar fassarawa, wata matsananciyar sha’awa ta’kara saukarmai lokacin yakai ‘kololuwa gurin bu’katar mace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button