BABU SO HAUSA NOVEL

AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

Dai-dai lokacin kuma aka fito da gawar Hussaina domin kaita makwancinta.

Anan inso inja hankalin Al’umma akan mutuwa, yanzu abinda aka gane shine da ance wane ya mutu sai mata suje su cika gida wasuma ba dangin iya bare na baba, kuma Alhalin lokacin ana kimtsa gawa irin haka na jawo matsaloli da yawa, da zarar ka mutu ‘yan’uwanka da iyayenka sha’kikai ake bu’katar suje ga gawarka bawai mutanen unguwaba, ba’ace kada mutane suje gidan suyi gaisuwaba amma ayi ha’kurin kauda mamacin, mata inajan hankalinku da kunyi gaisuwa ga wad’anda akayima mutuwar kutafi gidajenku shine mafi Alkhairi agareku kada azauna zaman gulma da cin abincin gidan mutuwa. ALLAH SA MUDACE ALLAH KUMA YASA MUCIKA DA IMANI ameen
[2/3, 10:16 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….38

® TALENTED WRITER’S GROUP (TWG) ????

Nan fa aka Shiga wani sabon tashin hankali ganin Hassana kwance ba Alamar numfashi tattare da ita, Momy kuka take tama rasa inda zata dosa saboda tsabar rud’ewa.

Sai kusan awa ukku sannan Hassana ta farfad’o lokacin ‘Karin ruwane ke shiga jikinta, ahankali tafara bud’e idonta ido biyu sukayi da ‘kanwar babanta Haj Uwani tana mata firfita, ganin ta bud’e idonta yasa tafara jeramata sannu.

Bin robar ‘karin ruwan dake hannunta tayi da kallo, tunanin ‘yar’uwarta tafad’omata arai “yanzu shikenan Hussaina tamutu nashiga ukku, ya zanyi da ‘kullallen al’amarin data barni cikinsa, yazanyi in tunkari iyayena da mijin ‘yar’uwata da wannan ‘kazamin Al’amarin damuka aikata.

Fashewa tayi da wani irin kuka me ban tausayi, tana ‘ko’karin tashi daga kan gadon, saurin ri’keta Haj Uwani tayi tare da rarrashinta.

“Kiyi ha’kuri Hussaina dukkan me rai mamacine, addu’a kawai zakibi ‘yar’uwarki da ita, dan ita tafi bu’kata akan kome “Allah ji’kan Hassana yakai Haske kabarinta Allah toni asirin wad’anda suka aikata wannan mummunan aiki akanta, Haj Uwani tafad’a tana share hawayen fuskarta.

Hassana kuwa kwance tayi, tayi lamo akan gado tana sauraren yanda Mama Uwani ‘Kanwar daddy take kwararo addu’a akanta bayan ita tasan ba itabace ta mutu, amma babu damar tafad’i, hawaye yacigaba da kwarara daga idanunta ba ‘kakkautawa. Ahaka Momy tashigo d’akin hannunta d’auke da cup, ganin Hassana na kuka ya ‘kara d’aga hankalinta itama kad’an yarage tafashe da kukan da kyar ta rarrashi zuciyarta, ta daure tami’kama Haj Uwani cup d’in hannunta “gashi tunda tatashi ‘kara ta daure ko tea tasha kota d’an samu ‘karfin jikinta.

Nan Haj Uwani kar6i cup din ta tada Hassana zaune tana ‘ko’karin bata tea d’in tana ‘kin kar6a da kyar tasamu tasha Rabin cup takoma ta kwanta da tunani barkatai cunkushe a kwalwarta.

    *Bayan sati d'aya*

Hankali yad’an kwanta mutane ‘yan’uwa na kusa dana nesa kowa ya koma gida, gidan yarage daga Momy sai Hassana wacce tundaga ranar da’akayi rasuwar tazo bata komaba saboda har yanzu jikinnata ba ‘karfi duk tabi ta rame ta kod’e.

Washe gari ranar kwana takwas da rasuwar Hussaina Momy da Hassana na zaune, Momy na aikin rarrashinta akan taci abinci dan duk yinin yau batasa kome acikintaba, daddyne yashigo gidan da sallama, Momy ta amsa masa sallamar tare dayimashi sannu da zuwa, kallon Hassana yayi yaga yanda tarame ta kod’e cikin sati d’aya duk ta fita hayyacinta, har cikin ranshi ya tausayamata dan yasan ba karamar sha’kuwa tayi da ‘yar’uwar tataba, sai dai al’amarin ubangiji ba ruwanshi da sha’kuwar dake tsakaninka da mutum idan yatashi d’aukar rayuwarsa.

“Hussaina, daddy yakira sunanta.
Gabanta yafad’i sannan ta juyo ta kalleshi tare da amsawa, amma kanta sadde ‘kasa dan bata yadda su had’a ido dan gani take idan suka had’a ido da daddy ze iya gane cewa ba Hussaina bace.

Daddy yacigaba da magana “inaso kitashi ki shirya dan munyi waya da mijinki yanzu haka yana kan hanya zezo ya d’aukeki sai kitashi ki shirya kikoma d’akin mijinki kicigaba da biyayya, kinga dai abinda yafaru da yar’uwarki saboda haka kicigaba dayimata addu’a Allah kai haske kabarinta, yana gama fad’in haka ya wuce d’akinshi, Hassana kau fashewa tayi da wani irin kuka tafad’a jikin Momy tana maida numfashi sama-sama.

Hankalin Momy ya masifar tashi ganin yanda Hussana ke kuka ga numfashinta na fita sama-sama, amma ba yanda zatayi dan tasan tunda Daddy yariga ya furta takoma tofa ba fashi saita koma yau d’in, saboda haka jiki a sanyaye Momy tatashi ta taimaka mata tayi wanka, tana fitowa tad’an shafa mai sama-sama sannan tacanja kayan jikinta zuwa wata doguwar Riga, bata dad’e da gama shirinba suka jiyo tsayawar motar jabeer a harabar gidan, kafin jabeer yashigo ciki daddy yafito ya umarci Hassana data tashi sutafi kada ta 6atamai lokaci.

Haka ta mi’ke jiki ba laka tanufi harabar gidan tana tafiya tana waige jitake kamar takoma tasanar da daddy gaskiyar Al’amari amma data tuno da irin zuciyar daddy sai tsoro yakamata, dan tasan tsaf itama ze iya aikata inda ‘yar’uwarta tatafi.

Ahaka ta isa gurin motar jabeer na ganin tahowarta yashige mazaunin driver tare da budemata gidan gaba tashiga ya tayar da mota me gadi ya bud’emasu get suka d’au hanya.

Love u all my Fan’s ????????????
[2/4, 4:46 PM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….39

® TALENTED WRITER’S GROUP (TWG) ????

Tun a mota Hassana ke faman kuka har suka iso gida, jabeer nayin parking tafito tanufi cikin gidan dagudu tana ‘kara fashewa da kuka, tana shiga falo tawuce bed room tasa key tarufe ‘kofa

tarufene dan bata bu’katar jabeer yabiyota yace ze rarrasheta, fad’awa tayi kan gado tacigaba da rizgar kuka Kamar zata cire ranta.

Tunanin Hussaina yafad’omata arai yanda suke kome tare, ba abunda ke rabasu ko bacci basu yadda yarabasu har tayi aure amma gashi mutuwa tarabasu, zaune tatashi ta d’auko wayarta tana kallon Hotunan dasukayi itada Hussaina lokacin suna gida wasu sabbin hawaye suka kwararo a idanunta, tafara surutai kamar wacce ke magana da wani a kusa da ita tana kallon wani hoto na Hussaina “sister mesa kika tafi kika barni da ‘kulallen Al’amarin da bansan yanda zanyi in warwareshiba, Hussaina ina kikaje aka rabaki da rayuwarki, me kikayimasu suka kasheki, ya Allah ka toni asirin kosu waye suka aikata maki wannan abin.

Cillar da wayar tayi gefe takoma kan gadon ta kwanta tacigaba da kukanta,
Bata tashiba sai ‘karfe bakwai da rabi na dare lokacin wani matsanancin ciwon kai ke addabarta, a daddafe tatashi tashiga toilet ta d’auro Al’wala ta rama sallolin da’ake binta daga magrib har isha’i tadad’e tana lazimi kafin tashafa takoma kan gado ta kwanta, tunani barkatai takeyi a zuciyarta tace “ni yanzu yazanyi in fidda kaina cikin wannan sar’ka’kiyar……

 Bayan kwana goma tunda Hassana tadawo gidan jabeer bayan rasuwar Hussaina bata yadda su had'u da jabeer.

Kalacin safe saitaji fitarshi take fitowa tasamu abinda zata sama cikinta, dukda ba wani abincin kirki takeciba hakanan take tutturwa, da rana zata fito tayi abinci tajera a dining sanan ragyara ko’ina na gidan ta share hadda d’akin jabeer d’in, tana gamawa take ibar wanda tasan ze isheta daga lokacin har dare sannan takoma d’aki bakuma Zata ‘kara fitowaba sai gobe idan taji fitar jabeer d’in

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button