AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

Tun jabeer na rarrashinta akan tafito ta daina zaman d’akinnan har yaha’kura ya kyaleta ganin tunda yake magiya ko saurarensa batayi sai dai duk ranar dayayimata magana yajiyo sautin kukanta.
: Bayan sati d’aya tana zaune d’aki kamar yanda tasaba tanajin lokacin da jabeer yafita saboda haka da sauri tafito tahad’a abinda zataci, dankali da kwai tasoya sannan tahad’a tea cikin cup tadawo palo ta zauna tafaraci, bawani dad’insa takejiba dan yau tashi tayi da wata irin kasala ga tashin zuciya dake addabarta, ahaka tasamu ta tuttura dan yunwar jinta takeyi, tana gama cin abincin kuwa yafara tu’karta da gudu tanufi toilet tafara she’ka amai, saida ta amayar da duk abinda taci sannan taji sau’ki-sau’ki
Nan take kuma wani irin zazza6i yarufeta, tafara kyarma kan gado tafad’a sannan tajawo wani ‘katon bargo ta kudundune dukda uban zafin da akeyi a lokacin.
kuyi ha’kuri yau namaku typing kad’an, da bazanyiba ma ganin mutane sun matsamin yasa nayi, muhad’u a page na gaba
Love u all my Fan’s ????????
[2/6, 9:28 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}
Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????
Page………………….40
® TALENTED WRITER’S GROUP (TWG) ????
Jabeer be dawo gidan ba sai bayan sallar azahar kamar yanda yasaba dawowa, da sallama yashigo falon kai tsye d’akinshi ya wuce yafad’a toilet yayi wanka danya kwaso gajiya sosai, bayan yafito daga wankan ne ya murzama jikinshi mai sannan ya canja kaya zuwa ‘kanana marassa nauyi, falo yadawo kai tsaye dan yakwaso yunwa sosai yasan ze tarar da abinci kamar yanda yasaba.
Falo yadawo kai tsaye ya doshi dining area amma bisa mamakinsa sai yaga wayam bako cokali gurin barantana yasa ran abinci, cike da mamaki yashiga kitchen nanma ganinsa yayi tas ko ina a share a goge ba alamar andafa wani abinci cikinsa, cike da mamaki yadawo falon sannan yanufi d’akin Hussaina nocking yayi ahankali duk da yasan ba bud’ewa zatayiba, hannu yasa yad’an murd’a handle d’in ‘kofar da mamaki kawai sai gani yayi kyauren ya bud’e, ahankali yashiga d’akin yari’ka dubawa inda ze ganta can idanunsa sukayimai tozali da ita tana kwance kan gado ta kudundune a bargo tanata makyarkyata kamar wacce aka she’kama ruwan ‘kan’kara, duk zafin da akeyi a garin.
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un jabeer yafad’a tare da nufar inda take kwance, zama yayi gefen gadon tare da bud’e bargon yana kallonta sannan yakai hannunsa kan wuyanta, jin wani irin zafi yayi rau ajikin nata, “subhanallah zazza6i Kike amma baki gayaminba sai ki zauna da ciwo ajiki, kitashi mutafi asibi,
: Bejira mezata fad’aba yanufi wadrope ya d’aukomata hijab, da kanshi ya taimaka mata ta sanya hijab d’in sannan suka nufi mota da sauri jabeer yabud’emata gaban mota ba musu ta zauna sannan ya zagaya yashigaazaunin driver suka d’au hanyar asibiti.
Bakin wani private Hospital suka tsaya me suna Allah Bamu Lafiya dake cikin garin katsina jabeer da kanshi ya taimakama Hassana tafito daga motar suka nufi cikin asibiti, suna zuwa kai tsaye aka bud’emata file sannan aka turasu gurin likita, bayan yan tambayoyi da likitan yayima Hassana itakuma tayimai bayanin duk abinda takeji, nan take likitan ya danna wata ‘yar karaurawa saiga wata nurse tashigo, ta rissina gaban likitan cikin ladabi, ya nunamata Hassana “kije da ita kiyimata wannan gwaje-gwajen yafad’a yana mi’kamata wata takarda, “owk sir tafad’a tare da amsar takardar sannan takama hannun Hasaana suka nufi lab, nan aka ebi jini sannan tanunamata toilet tabata wani d’an konkoni na roba ta umarceta datayo fitsari anan, haka Hassana tayo fitsarin takawo sannan takoma kan wani benci Wanda masu jira ke zama ta kwanta ta kudundune cikin hijab d’inta dan har yanzu wani irin sanyi takeji,
Kusan minti talatin suna jiran result ganin yanda mutane ke ‘kara yawa yasa jabeer matsawa kusa da Hassana yace “ko muje inkaiki gidanmu tunda kusane ni sai indawo injira sakamakon dakuma magungunan daza’a rubuta.
‘Daga mashi kai kawai tayi, alamar hakan yayimata dan dama ita tamatsu dasubar wannan asibitin ganin yanda mutane suketa zuwa gashi gurin zama ma yana neman gagarar wasu itakuma ga wani irin sanyi datakeji.
Da taimalonshi suka isa gurin mota, bud’emata yayi tafara shiga sannan shima yashiga yatshi motar suka tafi, kasancewar ba nisa tsakanin asibitin da gidansu jabeer ba’a d’au wani lokaciba suka iso, bakin ‘kofar gidan sukayi parking sannan suka fito, suka nufi cikin gidan Ahankali Hassana take tafiya tana biye da jebeer, yanayi yana waigenta har suka isa cikin gidan suka kwad’a sallama Umman jabeer daga d’aki ta amsa, dai-dai lokacin ‘kanwarsa nusaiba tafito daga wanka ta kai dubanta garesu cike da fara’a “Lah Yaya jabeer ashe tare kuke da aunty Hussaina, jin an ambaci Hussaina yasa Umma Fitowa daga d’aki tana masu sannu da zuwa, takai dubanta ga jabeer baka cemin tare kuke.
“Eh wlh mama daga asibiti muke shine nace bari inkawota nan tad’an huta kafin agama gwaje-gwajen daza’ayi.
“Subhanallah, Umma tafad’a meyasameta? Ta tambaya tana ‘karema Hassana kallo wacce ta saddar da kanta ta’ki bari su had’a ido da Umma, amma hakan behana Umma tagano wani Abu tattare da itaba, murmushi tayi me d’auke da farin ciki, sannan takama Hannun Hassana suka nufi d’aki tanata jera mata sannu.
Love u all my Fan’s ????????
[2/7, 10:32 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}
Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????
Page………………….41
® TALENTED WRITER’S GROUP (RWG) ????
Jabeer ne zaune gaban likita, saida likitan yayi wasu ‘yan rubuce-rubuce sannan yafad’a mashi ainafin abinda ke damun Hassana, sannan yabasu shawarar hanyoyin daza’abi domin kare lafiyarta,
Nan jabeer yayi godiya sannan ya sayi magungunan da’aka rubuta ya wuce gida.
Da sallama yashigo gidan, zaune ya iske Hassana da kwano a gabanta d’an wake ne Mamanshi tayimata shine takeci dan ba ‘karamin dad’i yayimataba, dai-dai lokacin nusaiba tafito daga d’aki cikin kayan islamiyya kalar ruwan ‘kasa, cikin ladabi ta isa kusa dashi “yaya harka dawo? “Eh nadawo nusaiba ina mama take ? “Tashiga nan makwabta zata kar6oma Aunty Hussaina kunun aya, tunda kashigo ni bari na wuce islamiyya dama nafara latti baniso inbar aunty ita kad’ai shiyasa nad’an jinkirta.
“To shikenan maza kitafi ga wannan kihau napep dan kiyi saurin zuwa yafad’a yana mi’komata d’ari biyu hannu biyu tasa ta kar6a sannan tayi godiya tawuce.
Kujera jabeer yajawo ya zauna gaban Hassana suna fuskantar juna “sannu ya jikin naki,? “Da sauki, tafad’a tana cire Hannunta daga kwanon d’anwaken, buta ta d’auka tanufi bakin maguji domin wanke hannunta, jabeer yabita da kallo har cikin ranshi yake matu’kar tausayamata ganin yanda tarame sai wani uban fari datakara.
Umma ce tashigo da sallama, dai-dai lokacin Hassana tagama wanke Hannunta zata mi’ke Umma tayi saurin kamata ta mi’ke tana ri’ke da ita har kan tabarma datake ta zaunar da ita, tana jeramata sannu a zuciyarta kuma fall da farin ciki ganin takusa samun jika.
Dai-dai lokacin kuma aka kira sallar la’asar saboda haka jabeer besamu damar yin wata magana da maman tashiba yad’auki buta yayi Al’wala ya wuce masallaci.