AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

** ** **
Zaune yake gurin wani sha’katawa, gurin ya ‘kawatu da itatuwa da flower’s masu kyan gani da dad’in ‘kamshi, mutane ne kala-kala a gurin wasu mata da mijine da yayansu, wasu kuma saurayi da budurwa, kowa harkar gabanshi yakeyi babu Wanda yadamu da wani, shikam yakasa zaune yakasa tsaye kad’an-kad’an yaduba agogon hannunsa, dan ‘karfe hud’u sukayi da ita zatazo nan suhad’u amma gashi har hud’u da rabi kome kama da ita be ganiba.
Wayarshi ya d’auko yayi ‘yan danne-danne sannan yakara a kunne, wani abin takaicin cemasa akayi switch off, wani mugun takaici ya lullu6eshi jiyayi kamar ya kwala wayar da ‘kasa dan haushi.
Dai-dai lokacin me napep ya sauketa, sanye take da ba’kin wando pencil da jar riga iyakar cinya, wacce ta d’ameta tafiddo duk wata sura da Allah yayimata, sai wani yala-yalan gyale kalar ba’ki datayi rolling dashi kafarta jan takalmine mai matu’kar tsini, hannunta ri’ke da waya ‘kirar iPhone 7 yayinda d’ayan hannun take ri’ke da poss kalar ja, duk illahirin gurin ya buge da ‘kamshin tsadadden turarenta, wani ‘katon ba’kin glass ne rufe da kwayar idanunta wanda ake kira no respect, cikin takunta na yanga da ‘kasaita ta iso inda yake lokacin yayi zurfi cikin tunanin rashin zuwanta besan ta iso gurinba saida taja kujera ta zauna ‘kamshin turarenta ya daki hancinta sannan ya maida dubansa gareta.
“Haba zuby saboda me zaki shanyani anan aka gayaki banida aikin yine tun d’azu nake kiran wayarki gaba d’aya a kashe, cikin tsananin 6acin rai da d’aga murya yake mata magana.
Tashi tayi tsaye tare da d’age bakin glass d’inda ya rufe kwayar idanunta ta d’aga mai hannu “dakata Hafiz karfa kace zaka d’agamin murya, kasani da da yanzu ba d’aya bane, sabodame zakari’kamin shouting a kunne banison hayaniya
Hafiz sakin baki yayi yana kallon zuby yanda take gayamashi magana son ranta, wanda a da koda kud’i aka sakata bazata iya gayamai hakaba.
A zuciyarshi yace lallai dole inyi maganinki zuby, amma a zahiri sai yayi murmushi “sorry abin bekai hakaba yanzu dai zauna muyi magana ta fahimta
Komawa tayi ta zauna ta d’ora ‘kafa d’aya kan d’aya tana taunar cingam irinnan gogaggin yan duniya.
“Kingane zuby abinda yasa nakiraki nace muhad’u anan kinga yanzu rabona dake kusan wata biyu kenan kuma kinriga kin sabamin da lallausan jikinki, kin shagwa6ani da shan daddad’ar zumarki ‘kauracewarki gareni ba ‘karamin cutar dani yakeba yakamata mukoma yanda muke da.
Murmushi zuby tayi me d’auke da rainin wayo, “Hmm Hafiz aini yanzu na wuce ajinka, dan yanzu gaf nake danayi aure, kuma wanda zan aura yafika kyau kud’i wayewa, kai yafika kome wlh.
“Amma waye wannan wanda ze aureki shin besan Halinkiba, ze kwasarma kanshi bala’i “besaniba kuma baze ta6a saniba dan iya sanin da yayimin mutunniyar kirki yasanni kuma ahaka zan bayyanamai soyayyata kuma inada tabbacin ze aureni.
“Kada kaji inata baka labari ban gayama ko wayeba, ba Kowa bane face JABEER mijin ‘kawata Hussaina wacce tarigamu gidan gaakiya.
Tana gama fad’amai tasa hannu ta d’auki wayarta da poss d’inta dake ajiye kan table d’in tare da gyara zaman glass dinta a fuska tace kaga tafiyata sai anjima ko…
Tafiya take tana karairaya Hafiz kuwa bin bayanta yayi da kallo yanda take juya mazannai, wani miyau ya had’e ‘kutt sannan ya kwalamata kira “Zuby……. A yangance tajuyo ta kalleshi tana wani shu’umin murmushi, hannu yasa Aljihu ya ciro wata agogo ya d’aga mata zaki iya sheda wannan agogon da kuma ranar da kika yaddata.
Wani mummunan fad’uwar gaba taji lokacin data tuno da ranar data kashe Hussaina bayan ta dawo gida tanemi agogon tarasa.
Love u all my Fan’s ????????
[2/7, 12:25 PM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}
Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????
Page………………….42
® TALENTED WRITER’S GROUP (TWG) ????
Dawowa tayi ahankali jikinta yayi sanyi, “Hafiz ina kasamu agogona?
“Murmushi Hafiz yayi me cike da samun nasara “Zuby kenan idan ke sammako kikayi wani a hanya ya kwana, kince zaki auri jabeer ko, saboda kinaso zaki aureshi shine kika raba matarshi da duniya, kina tunanin bansan ke kika kashe Hussainaba.
Kyarma Zuby tafara ‘kirjinta na dukan tara-tara ta kalli jabeer, sannan ta dake ta nuna ba Alamar tsoro tattare da ita tace “of course, bazan tsaya jayayya dakaiba Nina kashe Hussaina kuma bazan ta6a danasaniba saboda Hussaina tashiga gonatane ta hanyar rabani dakai, Wanda a lokacin banida wanda nakeso bayanka.
Amma yanzu na canja akalata zuwa ga jabeer kuma nasha Al’washin saina aureshi.
Murmushi Hafiz yayi tare da mi’kewa tsaye yayi taku ahankali yazagayo bayan kujerar datake zaune yadafa bayan kujerar sannan yadu’ko saitin kanta yace
“Karya kike Zuby nasan har yanzu kina sona, kuma inada tabbacin babu wani namiji daze maye gurbina a zuciyarki.
Kawai shawarar dazan baki shine :nasan ke mayyar kud’ice kuma nasan badan kome kikeson jabeer ba sai dan kud’insa.
Idan kinajin shawara me zai hana mu had’a kai inrufa maki asiri idan kin auri jabeer shima ki aikashi inda kika aika matarshi ki kwashe mana dukiyarsa muyi aure mucigaba da jin dad’inmu. Yana gama fad’in haka yadawo kan kujera ya zauna yana fuskantarta.
Wani shu’umin murmushi tayi tacigaba da taunar cingam d’inta sannan tayima Hafiz wani sakaran kallo “baka isaba Hafiz bakuma zeta6a yiyuba kura da shan bugu gardi da kwace kud’i.
Ai dukiyar jabeer tawace ni kad’ai tafad’a tana nuna kanta,
Murmushi Hafiz yayi sannan ya d’auki wayarshi yayi yan danne-danne saiga duk magan-ganun da zuby tayi ashe yayi recording Of course bazan tsaya ina jayayya dakaiba nina kashe Hussaina kuma bazan ta6a danasaniba, saboda tashiga gonata latsa wayar yayi ya kashe sannan ya maida Aljihu, zaki iya fansar kanki da shawarar danabaki idan kuma kinyi gardama zan mi’ka wannan recording d’in ga hukuma.
Take zuby takashi ta duri ruwa ta dad’e da sanin shu’mancin Hafiz tsaf ze kaita a hukuma kuma ya wanke kansa. “Kada ka damu na amince da shawararka amma dan Allah ka goge wannan rocording d’in, tafad’a tana kyarma kamar wacce akayima wanka da ruwan ‘kan-‘kara.
“Zan goge kada kidamu fatana kawai mucigaba da harka kamar yanda muka saba.
“Indan wannan ne kada kadamu muje koh.
Owk muje kawai yafad’a, mota suka nufa gidan gaba Hafiz yabud’ema zuby tashiga sannan ya zagaya mazaunin driver suka d’au hanya.
Gidan Hafiz suka sauka ranar sun she’ke ayarsu suduka sun nunama juna sunyi missing d’in junansu.
** ** **
Sai bayan sallar isha’i jabeer yadawo lokacin ya iske Hasaana tagama sallah mama ta zubo mata tuwon masara da miyar ku6ewa ga manshanu, nan Mama ta kalleshi “zakaci tuwon ne azuboma “Eh mama ai kinsan tuwo mutuminane, mama da kanta tashiga kitchen ta zuboma jabeer tuwon
Bayan sun kammala ne sukayi haramar tafiya gida, mama ta kalli jabeer “shin ka kar6o sakamakon kuwa a asibitin naji har zaku tafi bakayiman bayanin komeba
“Eh mama na kar6o wallahi ba wani abu bane ke damunta (Malaria) zazza6in cizon sauro, amma ga magun-guna na siyo likitan yace inshaAllah indai tanasha zata samu sauki.
Fara’ar mama tad’an ragu dan ita a tunanunta cikine da Hassana, amma saitaji sa6anin haka “to Allah sauwa’ke Allah maidaku gida lafiya, nan sukayi bankwana suka d’au hanyar gida.