BABU SO HAUSA NOVEL

AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

Suna isa sukayi horn megadi yabud’emasu get jabeer nayin parking Hassana tafito da sauri tanufi d’akinta tarufe da key kamar yanda tasaba tayi kwanciyarta, tunanin Hussaina yafad’o mata a rai batasan lokacin data fashe da kukaba,

Shikenan ni yanzu haka zancigaba da zama, gidan yar’uwata ba gidan mijinaba. Ya Allah ka kawomin mafita ina cikin tsaka me wuya.

Love u all my Fan’s ????????
[2/7, 7:48 PM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….43

® TALENTED WRITER’S GROUP (TWG) ????

wannan shafin nakine my lovely jikalle ta Halimatu Shu’aibu, momynki na mi’ko gaisuwa gareki sweet dougher d’inta Allah bar zumunci

Washe gari da misalin ‘karfe goma na safe jabeer ne zaune office d’insa da wasu fayiloli yanata faman wasu rubuce-rubuce, nocking d’in ‘kofar akayi ahankali, d’agowa yayi ya kalli ‘kofar sannan ya maida hankalinsa ga aikinsa, kara nocking akayi karo na biyu, aje biron hannunsa yayi sannan yabada izinin shigowa.

Da sallama tashigo office d’in sanye take da riga da siket na less, wad’anda suka kame mata jiki, sai wani madaidaicin gyale data yafa har saman kai dan kan nata bako d’an kwali, ‘kafarta sanye cikin plate shoe,

Kallonta jabeer yayi daga sama har ‘kasa yace “zuby kece tafe da wannan lokacin,
“Nice tafad’a tana murmushi.
“Bissmillah zauna mana yafad’a yana nunamata kujera.

Ba musu ta zauna tana wani sakar mashi wani shu’umin murmushi, bayan sun gaisa tace “dama zowa nayi inyima gaisuwa dan lokacin da’akayi rasuwar bani gari, gaskiya munyi babban rashi tafad’a tana matsar kwallan munafinci, Hussaina ‘kawatace banida tamkarta nayi babban rashi.

A mamakance jabeer yake kallonta, kindai manta Ai Hassanace tamutu ba Hussaina ba.
Wani mummunan fad’uwar gaba zuby tayi lokacin data tuno da shawarar databa Hussaina na cewa Hassana ta zauna maimakinta.
Inkau hakane ba shakka Hassana bata gayama jabeer ba itabace Hussaina idan kuwa hakane akwai aiki babba agabanta.

Jabeer ya kalleta “naji kinyi shiru me kike tunani, firgigi tayi kamar wacce tafarka daga bacci, ah bakome, nizan wuce Allah bada ha’kuri. “Ameen kawai jabeer yace sannan yacigaba da aikinsa.

Jiki ba lakka Tabar office d’in, daga nan gida kawai tawuce zuciyarta cike da tunani barkatai.

Zuby a d’akinta sai safa da marwa takeyi, tana sa’ke-sa’ke a zuciyarta “tabbas Hafiz shine babban matsalata idanko hakane dole in d’au mataki kanshi.

Wani mugun murmushi tayi lokacin wanda koni zee bansan ma’anar yinsaba.
Wayarta ta d’auko ta danno sunan Hafiz bugu d’aya ya d’auka “hellow zuby na yadai, akwai labari ne?

“Sosaima kuwa akwai labari me dad’in sauraro, inaso muhad’u a park dinda muka saba had’uwa.
“Owk ba damuwa kamar ‘karfe nawa?
“Yanzu-yanzu kome kakeyi ka ajiye kataho dan abari ya huce shike kawo rabon wani.
“Owk ganinan zuwa.

Saurin fad’awa wanka zuby tayi ta she’ka wanka, tana fitowa batare da 6ata lokaciba lotion kawai ta murzama jikinta sannan tasaka irin ‘kananun kayan data saba sakawa, tana fitowa bakin titi ta tsaida me napep tagayamai inda ze kaita, cikin mintinan dabasu wuce talatinba ta iso gurin ta sallami me napep, wayarta ta fiddo da niyyar takira Hafiz ta tambayeshi ya isone hangoshi tayi jingine jikin motarsa yana sakar mata murmushi, itama murmushin tayi sannan tanufi gurin wasu kujeru kai tsaye ta zauna, shima Hafiz nan yadawo ya zauna kusa da ita a ‘kagare dayaji labarin datazo mai dashi.

Kusan minti biyar da zamansu zuby batayi maganaba, a ‘kagauce Hafiz ya kalleta inajinki zuby, na bud’e kunne ina sauraron jin daddad’an labari kinyimin shiru.

Kallonshi tayi daga sama har ‘kasa “owk kada ka damu nad’an gajine inaso in huta tukun, bari naje can na kar6o mana drink’s mud’ansha konaji sanyi-sanyi,
“A’a kibari in anso mana Hafiz yafad’a yana mi’kewa tsaye,
“A’a kabarshi kawai zan amso saurin yin gaba tayi dan kada Hafiz d’in yacemata a’a.

Haka ta isa gurin siyar da drink’s kwalbar lacasera biyu ta kar6o duk idanun Hafiz kanta dan tsakanin gurin dasuke da gurin siyan drink’s d’in ba nisa.

Gurin dawowa maimakin tabiyo hanya street saita kauce ta inda be ganinta, tad’an jima sannan tayo zagaye tadawo da lemun guda biyu hannunta.

Zama tayi sannan tabud’e kwalba guda tami’kama Hafiz, itakuma tabud’e guda tanasha suna labari nan takeba Hafiz labarin cewa taje office d’in jabeer kuma ya amince da aurenta, wani dad’i yaratsa zuciyar Hafiz, dai-dai lokacin kuma yagama shan lemun lacasera dake hannunsa ya jefar da robar.

Mi’kewa zuby tayi tsaye tare da kecewa da wata irin dariya tace “anzo gurin kasani Hafiz kwananka ya’kare yau zakayi bankwana da duniya, zuge Jakarta tayi tafito da wata ‘yar’karamar kwalba tace “gaga wannan shine ake kira da silent killer, kuma ahine na zubama a lemun dakasha, saboda haka zaka iya zuwa gida karo’ki Umma yafiya kafin ka margaya barzahu, dan baya kisa farat d’aya, ni kaga tafiyata.

Tana gama fad’amashi tami’ke takama hanya tayi tafiyarta.
Hafiz kuwa duk illahirin jikinsa kyarma yake, yasan shu’umancin zuby kome tafad’a zata iya aikatawa, da sauri ya suri makullan motarsa yabar gurin.

Love u all my Fan’s ????????
[2/10, 1:06 PM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….44

® TALENTED WRITER’S GROUP (TWG) ????

Cikin tsananin rud’ani da tashin hankali Hafiz ya isa gida, falon mahaifiyarsa ya zube yanata mai-maita istigifari, a zuciyarsa yana cewa “wannan bala’i dame yayi kama, gashi yanzu son zuciya yajamin na jefa kaina ga halaka, ‘kanwarsa ce tashigo da sallama ganin yayan nata kwance da alama yayi nisa a tunani ga hawaye kwance a idanunsa dan alamu sun nuna besan da shigowar wani mahalu’ki a d’akinba.

Saida ta matso gaf dashi tadafa kafad’arshi “Yaya lafiya kuwa na ganka haka da Alama kukama kakeyi, saurin tashi yayi ya goge sauran hawayen dasuka ma’kale a idonshi ya ‘ka’karo murmushin ‘karfin hali yace *Bakome Zee kada ki damu kaina ne kemin ciwo.

“Kuma shine ka zauna a gida, yakamata kaje asibiti, “to ‘kanwata zanje jeki shirya saimu tafi tare dan kan yana matsamin sosai bazan iya driving ba, “owk to ba damuwa bari na sanarma Hajiya kafin mutafi, saurin ri’ko hannunta Hafiz yayi kada kije tana bacci kuma kinsan doctor yahana atasheta idan tana bacci, muje kawai idan mundawo mun gaya mata.
A harabar gidan suka bud’e mota suka shiga Zee ke driving Hafiz kuma na zaune gefenta lokacin yaji cikinsa na juyamasa, ahankali ciwon ke gaba, zee kuwa hankalinta ya matu’kar tashi ganin yanda yayan nata ke magowa gashi har wani kumfa yafara fitowa a bakinsa, wani irin mahaukacin tu’ki tari’kayi dan ikon Allah kawai yakaisu asibitin, suna Isa aka kar6eshi Emergency aka nufa dashi, nan lokitoci suka rufa akanshi, yayinda zee ketai kai komo a bakin ‘kofar d’akin da aka shiga dashi tanata sharar hawaye dan ganitake kamar za’a fito acemata Hafiz ya mutu dan yanda aka shiga dashi ba alamar rai tattare dashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button