BABU SO HAUSA NOVEL

AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

      *washe Gari*

Da misalin ‘karfe goma na safe, Zuby na kwance kan gadonta da waya hannunta tana chat a wani tambad’add’en group data bud’e maza da matane aciki ba abinda ake a group d’in sai maganganun batsa da tura blue film da sauransu, tana chat din ta Lula duniya tanayi tana matse ‘kafafu dan tsabar jaraba, da kuma sauraron voice message d’inda wani tsagera a group d’in yaturo wanda shima Admin ne a group d’in.

ganin wayarta ta tsaya cak tasan kirane ze shigo, tun kafin kiran yashigo tafara buga uban tsaki dan ganin za’a katse mata jin dad’i, amma da mamakinta sai taga number Hafiz a firgice tami’ke tsaye, sai lokacin tatunafa tasaka mashi guba a lemu kuma yasha tasan ba tantama bekwana da raiba, to amma kuma taya aka kirata da number shi.

Tana cikin wannan tunanin har kiran ya tsinke, batare da 6ata lokaciba aka kuma kira karo ba biyu, jiki a sanyaye ta danna ok sannan takara a kunnenta.

“Hello” Zuby tafad’a cikin muryar fargaba.
A d’aya 6angaren Zee tafashe da kuka tare da cewa “Zuby koh?
Zuby ta amsa da “Eh nice amma wacece ke?
Zee ta’kara fashewa da kuka, sannan tace “ni ‘Kanwar Hafiz ce naga kece mutum ta ‘karshe da kukayi waya dashi jiya, cuma naga call log d’insa duka sunanki yafi yawa da Alama akwai sha’kuwa tsakaninku shine nakiraki in gayamaki jiya da dare Allah yayima Hafiz rasuwa.

“What Zuby tafad’a kamar tana cikin irin firgicinnan, sannan tadoka uban salati “Allah Sarki Allah ji’kan Hafiz,
“Ameen” Zee ta amsa kafin ta tsinke kiran.

Zuby kuwa tana kashe wayar rawa tafara takawa tana rera wa’kar ado gwanja inda yake cewa Me nemam jini yaje kwata, niko bani zuwa bikin daba mata, mata…..mata….. ta’karashe wa’kar tana nuna kanta “saini zuby duk wanda yaja dani yajishi kushewa, wata shegiyar dariya tayi sannan tafad’a toilet ta she’ka wanka.

Tana fitowa ta tsaya gaban mirror ta watsa wani matsiyacin make up a fuskarta na marassa mutunci, wasu watsatatsin kaya tasaka dan basuda maraba da shigar arna.

Kai tsaye gidan jabeer tayima tsinke, tana isa me gadi yayimata sannu da zuwa ta wuce dan yasanta kwanaki tana yawan zuwa gidan.

Hassana kuwa ganin tad’anji ‘karfin jikinta yasa yau tashiga kitchen tagama girki tana d’aukowa daga kitchen tana jerawa kan dining, tagama jera kome sanan ta tafi da niyyar takoma d’akinta dan tasan jabeer yana gab da dawowa kuma bataso yadawo ya isketa a falo.

Ido hud’u sukayi da zuby wacce ko alama bataji lokacin data shigoba, ba ‘karamin fad’uwar gaba Hassana tajiba dan ganin zuby tsaye fuskarta ba fara’a ko kad’an.

Love u all my Fan’s ????????. Kwana biyu kunjini shiru wlh yauma da ciwon kai natashi, atayani addu’a, amma idan naji sau’ki zan ‘kara maku ko page d’ayane zuwa anjima
[2/11, 9:05 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….45

® TALENTED WRITER’S GROUP (TWG) ????

Ido Hud’u sukayi da Zuby wacce ko alama bataji lokacin data shigoba, wani mummunan fad’uwar gaba Hassana taji dan ganinta tsaye bako far’a fuskarta kamar bata ta6a dariyaba

Dakewa Hassana tayi duk da tsanananin fad’uwar gaban datakeyi, tayima Zuby sannu da zuwa.

Ko kallonta Zuby batayiba ta ‘karaso cikin falon da takalminta da kome ta wuce kan kujera ta zauna ta d’ora ‘kafa d’aya kan d’aya tana jijjigasu.

Ba ‘karamin ‘karfin Hali Hassana tayiba gurin d’auko lemu daga cikin pridge tahad’o da cup d’in glass ta ajiye gaban Zuby tana fad’in bismillah ga lemu.

Wani matsiyacin kallo zuby tabita dashi, sannan tayi murmushi “kinga ba wannan yakawoniba zowa nayi inyimaki ta’aziyyar yar’uwarki data mutu.

“Eyyah Hassana wai, Hassana tafad’a jikinta na kyarma.
Zuby tayi dariya, “wacce Hassana kuma? Husaaina dai,
“Innalillahi kawai Hassana ke mai-maitawa cikin zuciyarta ganin da alama zuby tasan kome.

Zuby ta tsiyaya lemu ta kur6a sannan ta ajiye, kafin tacigaba da magana.

“Hassana yau nazo ingayamaki abinda kike zaton ba wanda yasani Hatta da iyayenki,
“Kina Zaune da mijin yar’uwarki amatsayinta, zaman me za’a kira wannan, zaman dadiro ko karuwanci….. Hmm…….

Hassana tunda Zuby tafara magana wani irin gumi ya karyo mata, zufa ta jiketa dukda sanyin a.c daya gauraye d’akin.

Tayi ‘karfin halin cewa “Haba Zuby wace irin magana kike fad’i haka kamar baki sanniba, nicefa Hussaina ‘kawarki ‘yar’uwatace Hassana ta mutu baniba……….

“Dakata Hassana Zuby tafad’a cikin d’aga murya, “kina tunanin bansan komeba, to bari kiji ingayamaki abinda ke kanki baki saniba.

“Nice nan naba Hussaina shawarar ki zauna a matsayinta kafin tadawo daga inda zataje, nasan tayimaki ‘karyar zataje biki, Hmm to ba wani bikin dataje nasan kinsan tsohon saurayinta Hafiz, to wurinshi taje, nikuma a duniya banida wanda nakeso sama da Hafiz, nayi matu’kar farinciki lokacin da Hassana ta gayamin anyimata aure , saboda nasan hankalin Hafiz ze karkato gareni, amma wani abin takaici dukda aurenta bata rabu da Hafiz ba.

Ban ‘kara shiga tashin hankaliba sai ranar danazo gidannan Jabeer yayimin kyautar ma’kudan kud’i, kuma sai naji zuciyata ta karkata gareshi.

Hakan yasa nabata shawara akan tanemi ki zauna gidannan amatsayinta dan tasamu damar zuwa gurin tsohon saurayinta Hafiz, kamar yanda tagayamin yanaso su had’u, yayinda nikuma nayi amfani da wannan damar na rabata da duniyar dan insamu in mallaki jabeer,

Cike da tashin hankali Hassana ke nunan Zuby “dama kece kika kashe Hussaina.?

Zuby tayi murmushi “ki dakata mana, me kikeci nabaka na zuba, yanzuma dana gaya maki aiba matsar bakina kikayiba.

Cikin tsananin tashin hankali Hassana tace “Allah ne ya matsi bakinki kuma sai kinyi danasani, zuby batabi ta kantaba tacigaba da kora mata bayani.

“Hmm nayi tunanin mutuwar Hussaina zatasa ki tona kome ki koma gida, nikuma da haka insamu damar auren jabeer.

Tami’ke tsaye tad’anyi taku biyu zuwa ukku sannan tacigaba da magana “Ranar danaje office d’in jabeer da niyyar inbayyana mashi son danakemashi sai ya nunamin aishi ba matarshi ce tamutuba.

Hmm inajin haka nasan baki fad’i gaskiyaba, kuma kincigaba da zama a matsayin matar jabeer, saboda haka ina baki shawara daki gaggauta tonama kanki asiri kuma kibar gidannan, nice yadace nazauna gidannan koda ban auri jabeer ba, tafad’a tana nuna kanta.

Tana gama fad’in haka tatafi da niyyar barin gidan har takai bakin ‘kofa ta dawo tace kuma kada ki kuskura ki gayama wani maganganun dumukayi domin yin hakan barazanace ga rayuwarki, idan kuma bahakaba kema zakibi yar’uwarki inda taje.

Zuby natafiya Hassana tafad’a d’aki tasa key tarufe tafara rizgar kuka tana had’a kayanta cikin trolley, dan wani mugun tashin hankali tashiga Wanda tunda take duniya bata ta6a Shiga irinsaba.

Love u all my Fan’s ????❤
[2/12, 8:52 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….46

Da misalin ‘karfe ukku dai-dai jabeer yashigo gidan, kai tsaye d’akinsa ya wuce ya watsa ruwa ya canja kayan jikinsa Zuwa marassa nauyi, sannan yafito zuwa falo dan yaga yau da Alama akwai abinci gidan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button