AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

Zama yayi kan dining yazuba macaroni jalouf da Hanta, yanaci abincin nakaimasa karo, saida yaji ba sauran guri a cikinsa sannan yanufi pridge ya d’auko lemu ya tsiyaya a cup yasha , yajima zaune kan dining yana danne-danne a wayarsa kafin yatashi yakoma kan kujera da remote control hannunsa yana ‘ko’karin kunna tv yajiyo sheshshekar kuka daga d’akin matarsa, saurin ajiye remote d’in yayi yanufi d’akin dukda yasan idan zeyi juyin duniyan nan da wuya ta bud’e barantana kuma tafad’a mashi matsalarta.
Nocking yafarayi ahankali kafin yakira sunanta, “Hussaina ki bud’e mana bekamata ace ki kulle kanki a d’akiba kuma kina cikin damuwa waye zaki fad’awa kiji dad’i.
Ga kuma jikin naki har yanzu be gama warwarewaba.
Jin maganarsa yasa ta’kara fashewa da kuka, da kamar bazata tanka ba barantana ta bud’e amma sai wata zuciyar tabata shawarar ta bud’e kawai.
Haka tatashi jiki ba laka ta bud’e ‘kofar, ganin yanda idanunta suka kad’a sukayi ja, ya tabbatarmashi da ta dad’e tana kukan, wani irin tausayinta ya dira a zuciyarshi, kama hannunta yayi suka koma cikin d’akin ya zaunar da ita gefen gado sannan shima ya zauna dai-dai wannan lokacin kuma idanunsa suka sauka kan trolley data had’a kayanta ciki.
Juyowa yayi ya kalleta da mamaki a fuskarsa, yace “wannan jakar kayanfa lafiya dai.
Shiru tayi dan batasan irin amsar da zata bashiba.
Saida yakuma tambayarta karo na biyu tare da ru’kota yana ‘ko’karin had’a jikinshi da nata,
Saurin kwacewa tayi tare da mi’kewa tsaye tafashe da wani sabon kukan, tana ja da baya kamar tana tsoron jabeer d’in.
Da mamaki shima ya mi’ke yana tunkararta “Haba Hussaina danmi kike guduna baki ‘kaunar inta6a jikinki ko kad’an amatsayina na mijinki………..
“Kaiba mijina bane jabeer, haka kuma niba matarka bace, matarka ta mutu tsawon wata ukku dasuka wuce,
“Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un jabeer yafad’a “Hussaina anya kina cikin hayyacinki kuwa, nine yau zakice ba mijinkiba,
ba shakka lallai ‘kila kinfara irin shaye-shayennan na zamani…….
“Ko d’aya jabeer ban ta6a shan komeba, kuma dukkan abinda nafad’ama cikin hankalina nake……
Yanzu zanbaka labarin abinda baka saniba, koda kuwa yin hakan nima ze zama ‘karshen rayuwata kamar yanda ‘yar’uwata tabar duniya.
Wani sabon kuka tafashe dashi, saida tayi me isarta tayi shiru dan kanta batare data samu me rarrashintaba, saboda jabeer yariga ya shiga wani hali, so yake kawai yaji asalin gaskiyar abinda tafad’a wanda zesa ya yarda cewa ita ba matarshi bace kamar yanda tafad’a.
Nan ta kwashe labarin abinsa suka ahirya tsaf da Hussaina lokacin tana raye, na zamanta gidan amatsayin Hussainar wanda daga tafiyarne bata dawoba sai dai aka kawo gawarta, amma bata gaya mashi wacce takashe Hussainarba, sannan kuma bata gayamashi cewa gurin tsohon saurayinta tajeba, tadai gayamashi taje bikine kamar yanda ita Hussainar tagayamata.
Saukar wani wawan mari taji a fuskarta, wanda har saida taga wasu taurari, dafe kuncinta tayi ta zube ‘kasa tana kuka,
Shima jabeer d’in hawaye yake, yarasa inda zesa kanshi, innalillahi kawai yake mai-maitawa, yana fad’in Allahumma ajirni fi masibati wa khalibli khairan minha
“Hassana kin cuceni, kinsa na aikata abinda banta6a aikatawaba, amma ai Allah yana gani batare da sanina na aikataba, komiye kece sila.
Hassana dai bata ‘kara maganaba tun marin dayayimata kuka kawai take tana dana sanin amincewa da ‘kudirin ‘yar’uwarta.
A fusace jabeer ya d’auki trolley data had’a kayan yakai mota, sannan yadawo ya figeta itama ya bud’e motar yajefata kamar wasu kayan wanki, sannan yatayar da motar yafara dokama megadi horn, da gudu yazo ya bud’e masu get jabeer ya kwashi hanya da gudun tsiya.
Love u all my Fan’s ????????
[2/12, 12:46 PM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}
Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????
Page………………….47
® TALENTED WRITE R’S GROUP (TWG) ????
Wani mummunan fad’uwar gaba Hassana tayi lokacin dataga jabeer yayi parking cikin harabar gidansu, amma a zuciyarta saitaji ta dake akan kome ze faru ‘kara ya faru da zaman datake, wanda ita kanta batasan makomarsaba.
A fusace jabeer yafito daga motar sannan ya bud’e but ya d’auko trolley yanufi cikin gidan beko kalli inda takeba.
Da sauri tabi bayanshi tana sharar hawaye har tana had’awa da d’an gudu-gudu.
Momy da daddy suna zaune falo suna kallon labarai a tashar aljazeera, suka jiyo sallamar jabeer, daddy ne ya amsa yana ‘ko’karin fita yaga jabeer d’in yashigo janye da trolley, komawa yayi ya zauna yana kallon jabeer cike da mamaki harya ‘karaso yasamu guri ya zauna dai-dai saitin ‘kafar Daddy yana matsar kwalla.
Cike da alamomin tambaya Daddy ke kallon jabeer, Momy ma da alama hakanne a fuskarta.
Suna shirin tambayarsa saiga Hassana tashigo da kuka share-share a fuskarta, kamar wacce aka jeho tafad’i gaban Momy da Daddy tana cigaba da kukanta.
Daddy ne yayi ‘karfin halin tambayarsu “lafiya meke faruwa kukazo haka birkice, wani kuka Hassana ta’kara fasawa dan tasan yau kashetane kad’ai Daddy bazeyiba, amma ta kwammace hakan da zaman datake a gidan jabeer.
Suduka ba wanda yayi magana, shima jabeer d’in hawayene ke zarya a kumatunsa, yama rasa ta inda ze gayama Daddy abinda ke faruwa.
Daga ‘karshe dai yayi ‘karfin hali ya kalli Hassana yace “ki maimaita masu abinda kika fad’amin.
Daddy ya watsa mata wani kallo wanda yasa saida Hantar cikinta ta juya, sannan tayi saurin saddar da kanta tana hawaye, dan tasan babu wasa ko kad’an tattare da Daddy saboda haka batare da 6ata lokaciba ta fayyace masu kome kamar yanda tafad’ama jabeer kafin suzo nan.
Lokaci d’aya Momy da daddy suka saka salati, kafin Daga bisani d’akin yayi shiru bakajin kome sai sheshshekar kukan Hasaana, wacce jira take kawai taji anrufeta da duka, dan tasan ta caccanci abinda ma yafi haka.
Duk zafin Daddy da d’aukar matakinsa kan abu, yau kasa koda motsi yayi, sai Momy ce tayi magana “Amma Hassana baki kyautaba, itama abinda kawai ta iya fad’i kenan tayi shiru.
Mi’kewa daddy yayi tare da d’aukar makullan motarsa ya kallesu yace “kutaso ku dukanku ku sameni a mota, yana gama fad’i yayi gaba da sauri yabud’e motarshi yashige zuciyarsa cunkushe da ba’kinciki da takaici.
Minti biyar ba’ayiba sai gasu sun fito, gidan gaba Daddy ya umarci Jabeer ya zauna Hassana kuma da momynta baya.
Sannan daddy ya tayar da motar, Malam bala me gadi yabud’e masu get da sauri yana masu Allah kiyaye.
** ** **
Zaune suke gaban wani dattijon mutum Wanda kallo d’aya zakayima fuskarsa ka tabbatar da kamala da ilimi tattare dashi, dan ya ajiye sunnah a fuskarsa (gemu) bayan sun gaisa Daddy yayi Mashi bayani dukan abinda ke tafe dasu.
Malam Kasim yayi matu’kar mamakin jin wannan abu daya faru amma dayake shi addini me saukine kuma ya kawo yanda za’a warware kowace matsala saboda haka yafara yimasu bayani bayan yayi addu’a da salatin annabi (s.a.w)
“To kamar yanda kuka Sani tunda ita wannan yarinya dama ba matarsa bace bamu bu’katar ace sai yasaketa, amma tunda har wani abu na mu’amalar auratayya yashiga tsakaninsu, to zatayi istibira’i idan tagama zata iyayin aure.
(Istibira’i yana nufin zama da wacce tayi zina takeyi a gida na tsawon wasu watanni batare data ‘kara kusantar zinaba, dan ta tsarkake kanta kafin tayi wani auren)