BABU SO HAUSA NOVEL

AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

Aiko Maman jabeer najin haka ta fahimci inda zancen yadosa, wani irin farin ciki ya lullu6eta, dama kullum fatanta be wuce jabeer d’in yayi aureba.

Kusan minti sha biyar Zuby na zaune tana jiran ko jabeer ze shigo amma be shigoba, hakan yasa tayi sallama da mama tace zata tafi.

Mama tace “tun yanzu baki bari jabeer d’in yashigo masallaci yaje, cike dajin kunya Zuby tace “ba kome mama sauri nake wallahi islamiyya zani nagama har lokacin yafara wucewa.

To ki gaida gida ki gaida mamanki kinji, “to zasuji inshaAllah tafad’a sannan ta fice daga gidan.

Bakin ‘Kofa suka had’e da jabeer yana ‘ko’karin shigowa gidan, ganin Zuby tafito daga gidan ba ‘karamin tayar mashi da Hankali yayiba,

“Zuby meya kawoki gidanmu,? Ya tambayeta yana ‘karemata kallo dan ba ‘karamin kyau shigar datayi tayimata ba, murmushi tayi tace “meko ze kawoni idan banda tsananin so da ‘kaunar danikema.

Dur’kusawa tayi gabanshi idanunta na zubar da Hawaye, “Dan Allah jabeer ka taimakeni ka taimaki rayuwata, wallahi ina sonka ina ‘kaunarka tsakani da Allah, nasan kasan zafin so, kasan rad’ad’in so, dan Allah kada kacema ummanka baka sona, dan nasamu kar6uwa a wajenta d’ari bisa d’ari dan Allah kaima ka kar6eni kamar yanda ta kar6eni.

Ganin yanda take kuka tana mashi magiya gashi hartasa hankalin mutanen gurin yafara dawowa kansu yasa wani irin tausayinta ya dirarmai a zuciya besan lokacin daya kama hannuntaba yabud’e mota ya sanyata sannan shima yashiga suka d’au hanya.

Tunda suka tafi ahanya yake aikin rarrashinta, amma ta’kiyin shiru saida ya amsamata daya amince ze aureta, wani irin dad’i ya lullu6eta, tunnan tafara zumud’i tana sanar mashi da bata son asa bikin nesa idan sonsamune ayi kome nanda wata biyu.

Love u all my Fan’s ????????????
[2/19, 9:42 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….50

® TALENTED WRITER’S GROUP (TWG) ????

    *BAYAN WATA UKKU*

Hidima ta kankama sosai dan ahalin yanzu saura kwana goma d’aurin auren jabeer da Zuby, 6angaren jabeer be wani farinciki dan jiyake kamar tilastashi ake auren zuby amma ko kad’an babu dai-dai da kwayar zarra na sonta acikin zuciyarsa,

Ita kuwa Zuby ta dad’e da sanyama ranta zama matar jabeer, tuni tafara tsara yanda za’a gudanar da program d’in bikin itada ‘kawayenta, maganar gayya kuma ta dad’e da gama gayyato duka abokaninta maza da mata, program kusan kala bakwai ta tsara za’ayi a cewarta yanzune jabeer zeyi aure na kece raini saboda haka sati guda cif za’ayi ana gabatar da shagulgulan auren.

** ** **

Hassana ce kwance d’akinta, duk abin duniya yabi ya dameta ba abinda take tunani sai tsawon lokacin data d’auka gidan jabeer, cikin wannan zaman dasukayi ta la’kanci halayensa da dama ciki kuwa hada tsananin ha’kurin dake gareshi.

Juyi tayi ta gyara kwanciyarta zuwa rigin-gine ta ‘kurama silin d’in d’akin ido tsananin so da ‘kaunar jabeer na ‘kara mamaye zuciyarta.

Wani ‘kawataccen murmushi tayi, sannan tatashi zaune ta d’auko wayarta chat ta hau tana dubawa, wanda rabon data hau and’au lokaci me tsawo.

Best group d’inta tafara shiga na Ciwon ‘ya mace tana duba d’umbun message d’inda ta taras kwatsam idanunta sukayi kaci6is da hotunan wasu amarya da ango da aka turo ana gayyatar duk wanda yasamu damar halatta, ganin yanda aketa maganar bikin da kuma yanda ake fad’in kalaluwan program d’inda za’ayi yasa taji tana sha’awar bud’e hotunan amarya da angon dan taga yayan wani hamshakinne ake gagatawa haka.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un tashiga furtawa lokacin da idanunta sukayimata kaci6us da hoton jabeer da zuby.

Take wani irin gumi ya karyo mata, a hargitse tami’ke ta sanya hijab d’inta sannan ta sanya ni’kaf da safar hannu data ‘kafa, sannan ta ‘kara d’auko wayarta ta ‘kara kallon hoton jabeer da zuby ta ‘kara kallo Sannan tafara magana kamar Zuby na jinta “‘karya kike Zuby, wallahi ‘karyarki tasha ‘karya baki isa ki kashemin ‘yar’uwaba kuma ki auri mijinta wallahi saina d’au tsatstsauran mataki akanki.
Tana gama fad’in haka tafice daga gidan batare data nemi izinin Momy ko Daddy ba.

** ** **

Zuby kuwa kud’i ta amsa masu yawa daga hannun jabeer tasiyo kaya kusan kala goma wad’anda zata sanya gurin bikin, kowane kaya da jakarsa da takalminsa, yau sukayi da telanta zataje kar6ar d’inkunan saboda haka waya tafarayimashi ta tambayeshi ko ya’karasa, yacemata yagama ita kawai yake jira.

Wata ‘katuwar hijab tasaka sannan tafita, dan tunda tasamu tashawo kan jabeer ta daina shigar banza, koma Tayi saita saka ‘katuwar hijab.

Minti ashirin ya sadata da shagon USMAN FASHION Wanda ta yarda kuma ta amince da d’inkinsa dan babu wani tela dazemata d’inki taji dai-dai idan bashiba, ya kware a d’inkin mata, danshi baya d’inkin maza, lokacin data shiga shagon saida Hussaina tafad’o mata a rai dan itace ta nuna mata shagon telan sune nan daddy ke kawo masu d’inkinsu duka harda na momy.

Wannan tallace ga babban tela USMAN FASHION shagonsa nanan cikin garin katsina sabon layi bayan tsohuwar refabulik Hotel, d’inkin mata zallah na Zamani atamfa, material, shadda, yakeyi, duk me bu’katar ‘karin bayani zata iya tuntu6armu ta wannan no ????????

07037112229

Usman Fashion yataso me maida tsohuwa yarinya ????????????

Love u all my Fan’s ????????
[4/13, 9:58 PM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….51

® TALENTED WRITER’S GROUP (TWG) ????

Bayan angama Had’a mata d’inkunan jabeer tayima waya akan yazo ya d’auketa, ‘kofar gidansu ya sauketa sannan yaja motarsa yayi gaba da tsan-tsan kiyayyarta a cikin zuciyarsa,

Washe gari ya rage saura kwana tara d’aurin auren zuby da jabeer,
Zaune yake d’akinsa yahad’a uban tagumi hannu bibbiyu ba abinda yake tunani sai yanda ze zauna da Zuby amatsayin matarshi, ko kad’an bayajin sonta acikin zuciyarsa dai-dai da kwayar zarra, dan dai mamanshi kawai data nuna tsananin son auren shiyasa ya amince, besan me zuby tarika gayamataba kokuma takemata harta yarda da ita d’ari bisa d’ari kuma ta matsamashi akan sai ya aureta.

Wani guntun tsaki yaja gami da gyara zamanshi yajawo remote ya kunna TV lokacin ana labaran ‘karfe takwas

Da farko ga kanun labaran, ayau ne shugaba muhammadu buhari ya sauka gida Nigeria daga tafiyar da yayi zuwa ‘kasar England, Gobene Al’kalin babbar kotun jihar katsina ze gabatar da shari’a tsakanin wata matashiya me suna Hassana Mansir Company inda take ‘karar ‘kawar ‘yar’uwarta Zubaida wacce akafi kira da Zuby akan tana Zarginta akan kisan ‘yar’uwa.

A firgice jabeer ya mi’ke tsaye, yana mai-maita kalmar “Zuby takashe Hussaina, innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un, komawa yayi ya zauna hankalinsa a matu’kar tashe,
“Wannan bala’i dame yayi Kama? Anya zuby zata iya aikata kisan kai, meyasa Hassana takai zuby ‘kara akan abinda batada kwakwkwarar sheda akansa, amma ita tasani Allah kaimu goben masu iya magana sunce duk wanda yace ze had’iye gatari sai asakar masa ‘kota.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button