BABU SO HAUSA NOVEL

AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….53

Al’kali ya gama yan runbuce-rubucensa sannan yafara magana “ko lauyan wacce ake ‘kara yanada abin cewa.

Lauyan zuby ya mike “inada magana ya mai girma mai shari’a, da farko inaso in tabbatarma wannan kotu me Adalci zuby ba ita bace ta kashe Hussaina, kodan Idan akayi la’akari da ‘kawancen dake tsakaninsu dakuma aminci da yarda da juna, bayan wannan an tabbatar da marigayiya Hussaina batada wata ‘kawa bayan zuby, kuma Kowa yasan zuby yasan kyawawan halayenta bazata iya koda kashe 6era ba, barantana mutum, kuma ‘kawarta aminiyarta, saboda yarda da ita dakuma kyawawan halayenta yasanyama mijin ita marigayiyar yayi kwad’ayin aurenta Wanda a halin da ake ana saura kwana goma a daura aurenta ita Hassana tayi ‘kararta akan tana zarginta da kisan yar’uwarta wacce batada wasu kwararan shedu,…….. Yana kaiwa nan ya russuna yace “nagode ya mai girma me shari’a, sannan yakoma ya zauna.

Bayan Al’kali yayi rubutu, sannan yad’ago yace “ko lauyan wacce ke kara yanada abin cewa, sai lokacin lauyan Hassana yami’ke ya’kara gabatar da kanshi sannan yafara magana.
“Ya mai girma mai shari’a inaso inyima wacce ke ‘kara wasu yan tambayoyi, Alkali yace “anbaka dama, “kotu na bu’katar ganin Hassana a gabanta, wani mummunan fad’uwar gaba Hassana taji sannan tami’ke tana karanto addu’oin samun nasara abakinta.

Bayan tatsaya inda aka umarceta lokacin lauya yafara jera mata tambayoyi tana bashi amsa, karshe yace Hassana to ko zaki iya bayyanama kotu dalilin dayasa kike zargin zuby akan kisan ‘yar’uwarki? Hassana tagyara tsayuwa tace “itace tasameni har gida tafad’amun lokacin ina zaune gidan jabeer amatsayin matatarsa marigayiya Hussaina, kuma sannan ta gargadeni akan in gaggauta barin gidan da ita yadace da ta zauna amatsayin matar gidan sannan kuma tayimani kashedi da idan na kuskura nafad’ama wani nima zata kasheni.

Lauya ya’kara jefarta da wata tambayar “taya akayi kika zauna gidan jabeer amatsayin matarsa alhalin kuma yana auren ‘yar’uwarki?

Wani irin kuka ya kwacemata dan tunowa datayi da abinda yafaru da ita na AUREN TAGWAYE dasukayi itada yar’uwarta, ahankali tasa hannu tashare hawayenta sannan takwashe labarin abinda yafaru kaf tsakaninta da marigayiya Hussaina tundaga had’uwarsu da Hafiz har zuwa lokacin da taro’keta akan tanaso ta zauna gidanta amatsayin ita akan cewa zataje bikin ‘kawarta Wanda zubyn ce takitsa mata haka kuma tayi sa’a Hussainar ta amince shine tayi amfani da wannan damar takasheta dan tasamu damar aure mijinta, wannan shine iyakar abinda nasani.

Lauyan ya kalli al’kali wanda yake rubutu acikin littafinsa yace “inaso kotu tabani dama inyi wasu ‘yan tambayoyi ga mijin marigayiyar, alkali yace “anbaka dama.

Haka kotu ta umarci ganin jabeer, shima bayan yan tambayoyi da’akayimasa yaba kotu labarin iya abinda yasani tundaga aurensa da Hussaina dakuma zaman da Hassana tayi agidansa amatsayin ita marigayiya Hussainar. Daga kan tambayoyin da lauyan yayima Jabeer yajuya gurin Al’kali yace nagode ya mai girma mai shari’a, sannan yakoma ya zauna.

Lauyan Zuby yami’ke yana gyara rigarsa, yace “ya mai girma mai shari’a labarin da wacce ke ‘kara ta bayar kwata-kwata beda nasaba da abinda ake ‘kara Kanshi, saboda haka ina ro’kon wannan kotu mai Adalci datayi watsi da wannan shari’ar kuma sannan abima zuby hakkinta akan ‘kazafin kisa da aka li’kamata wanda batajiba bata ganiba.

Al’kali yace “ko lauyan wacce ke ‘kara yanada wasu ‘karin bayani? Lauyan Hassana yami’ke yace “babu yamai girma mai shari’a, bayan Al’kali yayi yan rubuce-rubucensa sannan yadago ya kalli Al’ummar dake cike ma’kil cikin wannan kotu yafara jawabi

“Abisa shedu dakuma bayanai da lauyoyi suka gabatar agaban kotu, kotu ta gamsu da bayanan kowane 6angare dakuma shedun dasuka gabatar saboda haka kotu tayi watsi da wannan shari’ar saboda batada makama, sannan kotu taba zuby damar d’auka ‘kara akan ‘kazafin kisa da aka li’ka mata.

Wani irin kukan takaici Hassana tafashe dashi dan jin abinda al’kali yafad’a, Zuby kuwa wani shu’umin murmushi tayi, take kotu ta kaure da surutun jama’a Kowa na fad’in albarkacin bakinsa.

Al’kali yabuga teburin dake gabansa sannan kotu tayi tsit, yana shirin cigaba da jawabi kawai sai ganin wani matashin saurayi sukayi yashigo kotun yana cewa “nine sheda na ‘karshe wanda zan war-warema kotu kome da kome akan wannan case din.

Nanfa kallo yakoma kan wannan matashin sunayin ido hud’u da zuby gabanta yayi wani mummunan fad’uwa, Jikinta yafara kyarma wata irin zufa ta keto mata, Hassana kuwa kallonsa takeyi tanaso ta tuna inda tata6a ganin wannan fuskar amma takasa tunowa.

Love u all my Fan’s.
[4/19, 1:45 PM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}

Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????

Page………………….54

Baki d’ayan hankalin mutanen dake cikin kotun yakoma kan wannan saurayin daya shigo yana fadin zebada sheda, Hassana kuwa mamakine yakamata azuciyarta tace ” toshikuma waye wannan ? meya sani game da mutuwar ‘yar’uwata,? anya akwai wata sheda daxe bada wacce zatasa Al’kalinnan ya saurareshi tunda har abinda nafad’a besa ya yarda cewa zuby takashe Hussainaba.

Muryar Al’kalince tadawo da ita daga tunanin datake, jitayi yana fad’in “saurayi daga ina? Kotu tanaso tasan ko kai waye kafin kabada sheda agabanta.

‘Kara dai-daita nutsuwarsa yayi sannan yafara magana “sunana Hafiz kuma ni saurayin Marigayiya Hussaina ne, wannan kuma friend d’inace yafad’a yana nuna Zuby.
Amma ita sona take kuma batada burin daya wuce in aureta, nikuma a lokacin bata gabana saboda ko d’an iska yanaso ya auri mace tagari ba irin zuby ba wacce tagama watsewa a titi, kwatsam saita fahimci muna soyayya da ‘kawarta marigagyiya Hussaina, muna cikin wannan halin mahaifin Hussaina yayimata aure saboda ganin ta 6ullo da wasu Halaye marassa kyau.

Haka dai yacigaba dabada labarin iyakar abinda yasani dangane da mutuwar Husssaina kuma ya tabbatarma kotu zuby itace takashe Hussaina saboda tanason ta auri mijinta dan ganin cikin irin jin dadin datake dakuma yanda mijinta ke Sonta.

A lokacin nikuma nabukaci da muhad’a kai idan ta auri jabeer ta kasheshi ta kwashe dukiyarsa tadawo muyi aure dan inada tabbacin babu wani namiji datakeso sama dani, jabir najin haka besan sanda yakalli zuby ba yana jin wata muguwar tsanarta cikin zuviyarsa, dama tun can ba sonta yakeba.

Hafiz yacigaba da magana shine tanuna rashin amincewarta, nikuma alokacin na kunna mata recording din danayimata lokacin datake jaddadamin ita takashe Hussaina, nan take ta tsorata dajin wannan recording dan nayimata barazanar muddin bata amince da bu’katataba zan dam’ka wannan recording hannun hukuma, shine tacemin inbata kwana biyu zatayi shawara.

Ranar data nemeni dan gayamin shawarar data yanke ranar tazubamin guba a lemu dan kada natonamata asiri, Allah yasa inada sauran numfashi ‘kanwata takaini asibiti da taimakon lokitoci nasamu kaina, shine nasa ‘kanwata tabugama Zuby waya tafad’a mata cewa namutu, tunda aka sallameni daga asibiti na tattara kayana nakoma garin Kaduna gurin abokina, ina can nasamu labarin wannan shari’a shine nazo dan inbada sheda yanzu hakama saukata garin kenan nawuto nan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button