AUREN TAGWAYE HAUSA NOVEL

Tana cikin wannan tunanin taji tsayuwar motar daddy, tananan hartaji shigowarsa falo sannan tafito tayimashi sannu da zuwa tawuce d’akinta, binta yayi da kallo da alama akwai abinda yake tunani dangane da ita.
Momy kanta ta lura da hakan, itace tadawo dashi daga tunanin dayake ta hanyar ‘kar6ar jakar hannunsa tawuce d’akinsa, shikuma yabi bayanta, ruwan wanka tafara had’a mashi saida yayi wanka ya canja kaya zuwa masu sakai-sakai sannan suka fito zuwa dining, Momy da kanta tazuba masu sannan suka fara ci.
Bayan sun kammala cin abincinne Momy ta kwalama Hassana kira, da sauri tazo tace “gani momy.
Momy ta umarceta data kwashe kayan dasukaci abinci, “to ta amsa sannan tafara kwasa tana kaiwa kitchen saida ta kammala ta gyara gurin tsaf, sannan takoma d’aki wayarta ta jawo ta kunna data best group dinta tashiga na Ciwon ya mace ta iske su Mmn Ummi da Mmn zee da Momyn ramadan da Ameena PA da dai sauransu anata raha itadai mutanen grouf din na matu’kar burgeta, sallama tayimasu suka amsa, nan fa Ameenoo tafara “oyoyo ga ‘kawata, nan Hadiza tace kaji shishshigi ‘kawarki ko tawa, murmushi Hassana tayi tace “Hmm kudakata aini banida ‘kawa duk grouf dinnan kowama ‘kawatace dan gaskiya kuna matu’kar burgeni kun iya zama da mutane.
A falo kuma momy ta kalli daddy Wanda ya maida hankalinsa kan jaridar dake hannunsa, tace “waini Alhj haka zamu zubama yarinyar nan ido tayita zama agida, kuma ita gashi tunda canma bata kula kowa barantana yanzu.
Shiru daddy yayi na kimanin mintuna biyar, itakuma Momy ta zubamai idanu tana jiran taji me zai fad’a.
Numfasawa yayi sannan yace “to me kike tunanin zanyimata kuma,?
Momy tad’an gyara zamanta “nida cewa nayi mezai hana tacigaba da karatunta kafin kuma muga abinda Allah zeyi.
Wani mugun kallo daddy ya watsama Momy wanda saida yasa hantar cikinta ta kad’a sannan yafara magana cikin d’aure fuska
“kada ki kuskura in ‘karajin wannan maganar daga bakinki, koda zatakai shekara nawa a gidannan babu maganar cigaba da karatu, munanan tare da ita har lokacin dazataga dama tagfito da miji tayi aure.
Yana gama fad’in haka ya kwashe jaridarsa yawuce d’akinsa yabar Momy zaune sake da baki.
Love u all my Fan’s ????
[4/24, 6:32 PM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}
Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????
Page………………….57
Momy kuwa tunda daddy yagama magana yashige d’akinsa yabarta zaune a falo, tunani barkatai takeyi a zuciyarta tana ganin kamar shawarar data kawoma daddy batada makusa amma sai gashi yanda ya nuna kwata-kwata bazebi shawarar tataba.
Tayi zurfi cikin tunani taji kamar ana sallama a bakin ‘kofar falon ‘kara saurarawa tayi jitayi ankara doka sallamar mi’kewa tayi tare da amsa sallamar ganin maman jabir datayi yasa tasaki murmushi “a’a yau kune a gidannamu lale maraba sannu da zuwa, “yauwa tafad’a itama fuskarta d’auke da murmushi.
Bayan sun gaisa momy tacika gabanta da kayan sanyi, mama tazuba lemun tasha sannan ta ajiye cup ta maida dubanta ga momy “Allah sa dai Alhj yana gida dan maganace me matu’kar muhimmaci take tafe dani.
Numfasawa momy tayi kafin tace “eh yananan bari namaki magana dashi, sannan tanufi d’akin daddy kwance ta iskeshi ya kalli bangon d’akin da alama yayi zurfi cikin tunani, zama tayi bakin gadon sannan tasanar dashi zuwan maman jabeer,
Tare suka fito Alhj na gaba momy na bayanshi, zama sukayi baki d’ayansu a falon bayan daddy sun gaisa da maman jabeer nan take sanar dashi maganar dake tafe da ita na nemawa jabir auren Hassana, da kuma yanda jabeer din yasanar da ita jiya.
Murmushi Daddy yayi wanda ya nuna alamun farin ciki tattare dashi sannan ya numfasa yace “in banda abin jabeer aini matsayin d’a na d’aukeshi koshi da kanshi yafad’amun ai bazan hanashi jininaba inshaAllah babu wata damuwa, yanzu abinda yakamata shine yafara zuwa su fuskanci juna shida yarinyar,
Godiya maman jabeer tashigayi, tana yaba halin kirki da dattako irinna Alhj mansir, mutumne me tarin dukiya, amma Allah be d’oramashi girman kaiba, da raina talaka.
Haka sukayi bankwana momy tayimata rakiya har harabar gidan suna ‘kara tattauna al’amarin yaran, da alama ita kanta momy taji dad’in hakan dan kowane iyaye zasuyi burin ‘yarsu tasamu nagartaccen namiji kamar jabeer, mutum me ilimi da ri’ko da addini, ga kuma ri’kon amana.
** ** **
Sanye suke cikin kayan uniform kalar dark blue, matane zallah zaune suke cikin wani ‘kazamin d’aki dan ba abinda ke tashi d’akin sai wani irin matsanancin wari, can na hango wata matashiyar yarinya zaune tahad’e kai da gwiwa da alama kuka take, itama sanye take da kalar uniform d’in jikin rigarta ansa number itace number ta sha takwas, wata ‘katuwar mata nagani taje kanta ta tsaya ta ta6ota tana fad’in “yaya dai ‘yanmata?
Ahankali wacce akayima maganar tad’ago ta kalli wannan wannan ‘katuwar matar, fuskarta sharkaf da hawaye tayi wani ba’kikkirin duk ta rame, jin wannan ‘katuwar matar takira sunanta “Zuby yadai yanaganki haka, zuby tasa hannu ta goge hawayen dake idanunta ta ‘kara gyara zama batada niyyar yin magana.
Wannan ‘katuwar matar dake tsaye ta gagga6e da wata mahaukaciyr dariya cikin muryarta wacce tafi kama data ‘kato, saida tayi dariya me isarta sannan tadafa kafad’ar zuby tace “Haba zuby ke kullum kuka kamar ke kad’aice kiduba kiga fad’in wurinana kowa harkar gabansa yake amma ke kinsama ranki tunani kin’ki ci kin’ki sha duk kin lalace.
Kallo zuby tabi mutanen gurin dashi kowace kuwa harkar gabanshi yakeyi kamar ba gidan yari sukeba, sannan tamaida dubanta ga matar tace dole inyi kuka dole ci da sha ya gagareni, rai raifa nakashe, dole tun duniya inga sakayya ko zaman gidannan ma kad’ai bala’i ne.
Wata mahaukaciyar dariya matar tasake bushewa da ita “tace lallai yarinyar nan rayuwarki na ‘Kazan ruwa, kowa tuba dan wuya ba lada, ni yanzu jiran lokacin daza’a sallameni kawai nake ind’ora daga inda natsaya.
Love u all my Fan’s ????
[4/25, 8:13 AM] Zee Elkaseem: ???? AUREN TAGWAYE ????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
Written & Story by
Zee Elkaseem
{Mmn khady}
Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace ????????
Page………………….58
Kallo kawai zuby tabita dashi dan tasan duk abinda tafad’a haka yake Har a zuciya na (Fiddausi so Dangi) amma itakam ayanzu tayi nadamar abinda ta aikata, gashi yanzu son abin duniya yakaita ya baro.
Suna cikin wannan maganar wannan katuwar matar taji an d’auketa da wani migun mari, waigawa sukayi bakin d’ayansu wata azzalimar ‘yar sanda ce suka gani, dan Duk illahirinsu masifar tsoronta sukeyi har suna suka sakamata inspector zalima, ai da gudun tsiya wannan ‘katuwar matar tabar gurin duk kuwa da uwar ‘kibar dake jikinta.
Zuby kuwa saboda rashin ‘karfin jiki kasa motsawa tayi daga wajen, hakan yaba inspector zalima damar wankamata lafiyayyun mari har guda biyu, dan gani take zuby ta rainata kowa na gudu atafi aiki amma ita ta gagara tashi, zuby kuwa yunwa da kishi, da rashin karfin jiki yahanata mi’kewa ganin haka inspector Zalima tasa bulala tacigaba da zabgama Zuby, saida tayimata rud’u-rud’u duk tafasa mata jiki sannan tabarta. Kuma sannan tatasa keyarta zuwa aikin dazasuyi na kwasar bola da wankin toilet dinsu mai d’auke da ‘kazantu kala-kala. Niko zee kallon zuby kawai nake tsananin tausayinta kwance a fuskata, nace lallai Zuby yau duniya tamata gwatson mage.